ME YA FARU A KARBALA 14(Dr. Mansur Sokoto)

·

·

Husaini Ya Kaura Daga Madina
Yin wannan hijira da Husaini ya yi
ta bai wa mutanen Iraqi irin damar
da suke nema. Take sai suka fara
aike masa wasiku suna nuna masa
dacewar ya dawo garinsu inda nan
ne matattarar yan shi’ar
mahaifinsa. Daman can akwai
rade-radin sun nemi ya yi tawaye
kan gwamnatin Mu’awiya bayan
wafatin dan uwansa Al-Hasan,
amma sai ya amsa masu da cewa,
mun yi alkawari da Muawiyah
kuma ba zan kwance alkawarin ba
sai in shine ya fara kwancewa.
Duba littafin “Kalimaatul Husain”na
malamin Shi’a As-sayyid Sharifi,
shafi na 238.
Wannan shi ke nuna maka cewa,
sayyidina Husain bai zargin
Muawiya da hannu wajen gubar da
aka sa ma sayyadi Al-Hasan
wacce ta zama ajalinsa. Domin
kuwa da yana zarginsa, da bai
furta wannan magana ba. Wane
kwance alkawali ne ya kai ga kisa?
Kuma ma dai saboda me Muawiya
zai kashe Al-Hasan, mutumin da
kuka yi tarayya da shi; aka nada ku
lokaci daya amma don neman
zaman lafiya ya janye ya bar
maka. Kuma a tsawon shekaru 10
bai taba saba maka ba, ya zama
daya daga cikin sojojinka. To, ka
kashe wannan don ka samu me?!
Yan shi’ar Iraqi dai sun nace a kan
Husaini sai ya taho Kufa kuma
suka ba shi tabbacin za su
tumbuke Yazidu su dora shi a kan
karagarsa.
Masu lura da al’amura sun ga
abinda ke kai da komo a cikin
wannan lokaci kuma sun ba
Husaini shawara ta tsakani da
Allah. Ibn Abbas cewa ya yi, a
ra’ayina ya kamata mutanen Iraqi
su fara cire gwamnansu su damka
maka kujerarsa idan har da gaske
suke yi sai ka soma daga can.

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: