ME YA FARU A KARBALA 9(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

HUSAINI Radiyallahu Anhu ya
Lizimci kawaici game da abinda
wansa ya yi na mika ragamar mulki
ga sayyidina Mu’awiyah, amma a
zuciyarsa bai ji dadi ba kamar
yadda akasarin mutanen Iraqi ba
haka suka so ba amma dai ya
daure ya yi mubaya’a tare da
sauran jama’a. Ba wani rahoto da
ya nuna ko sau daya ya taba nuna
ma Mu’awiyah rashin goyon
bayansa ga gwamnatinsa kamar
yadda shi ma Al Hassan din haka
ya yi. Sukan karbi kyautarsa, suna
mutunta shi tare da bin umurninsa.
Kusan ma duk yakokan jihadi da
aka yi a zamaninsa tare da su aka
yi. HUSAINI ma yana cikin
rundunar Yazidu wadda ta ci
Qustantiniyah. (Rundunar da
manzon Allah (S) ya ce sun
wajabta shiga aljanna). Shekaru
goma ne Al Hasan ya yi a
karkashin mulkin sayyidina
Mu’awiyah sannan ya gamu da
ajalinsa. Husaini kuma ya kara
wasu goma bayan haka kafin shi
kuma Mu’awiyan ya gamu da nasa
ajalin.
A cikin wasiyyar da Al Hasan ya
bar ma kanensa HUSAINI ya
gargade shi da kada ya rudu da
mutanen Iraqi. Ya ce masa ka san
wahalar da mahaifinmu ya sha a
hannunsu, kuma ni ka ga irin
tozartawar da na gani hannunsu
wadda ta sa na yada mangoro na
huta da kuda. Don haka, kada ka
yarda su sake janka cikin wannan
lamari. Ga dukkan alamu Allah ba
zai hada Annabta da halifanci a
gidanmu ba. Al Imam At Tabari ya
kawo wannan wasiyyar a tarihinsa.
To, ko sayyidina Husaini ya rike
wasicin yayansa? Amsa ita ce eh,
ya rike wasicinsa amma sai dai
akwai wasu abubuwa da suka biyo
baya. Sai a ci gaba da biyo mu
domin jin abinda ya faru.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates