ME YA FARU A KARBALA 19(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

Halin da ake ciki a can Kufa:
Fitar Husaini daga Makka ke da
wuya sai labari ya game garuruwa.
Mutane kuwa suka yi ta ce-ce-kuce
a kan wannan magana. Da
rahotanni suka isa wurin Yazid a
kan wannan batu sai ya raina
kokarin gwamnansa sahabi
Nu’uman bin Bashir Radiyallahu
Anhu ta yadda har ya bari aka yi
mubaya’a ga wakilin Husaini a
cikin garinsa kuma ko labari bai
aika ma sarkin musulmi ba. Don
haka sai ya canja shi da gwamnan
Basrah domin ya magance masa
wannan matsala.
Da sabon gwamna Ubaidullahi bin
Ziyad ya kama aikinsa a Kufa bai
samu wata wahalar gano Muslim
bin Aqil ba, inda ya sa aka kamo
shi tare da mai masaukinsa Hani’
bin Urwa Al Muradi. Kamar dai da
gaske mutanen Kufa sun nuna
alhininsu a kan kama wadannan
mutane har suka yi jerin gwano a
kan titunan birni kuma suka wa
gidan gwamna zobe suna neman a
sake su. An kiyasta wadanda suka
shiga wannan jerin gwano da
mutane 4000 daga Asalin 18,000
da suka yi masa mubaya’a. Ba
kuma wani matakin da aka dauka
sai ga su kafin yammaci sun dawo
kimanin 500 kacal.
Bayan haka ne Ubaidullahi ya
bukaci ganawa da shugabannin
kabilu wadanda ya yi shawara da
su a kan wannan lamari kuma suka
kwantar da hankalinsa cewa su
zasu shawo masa kan wannan
matsala. A cikin duhun dare ne
suka rinka sulalewa har suka
watse baki daya. Abin takaici da
ban mamaki shi ne yadda aka
kashe shi Muslim a fili aka kuma
kashe mai masaukinsa Hani’ bin
Urwa, sannan aka rataye
gawawwakinsu a kasuwa don
barazana amma mutanen garin
nan ba su motsa ko karen gamba
ba. Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi
Raji’un.
Wannan ya faru ne a ranar Arafat
ta wannan shekara da muke
magana a kai. Kwana daya kenan
kacal daga fitowar yayansa
sayyidina Husain. Wayyo Allah, ina
wayar salula da zata kai ma
maigidana Husaini wannan labari?
Ina Fax da Telex da Telegram? Ina
facebook da Tweeter da
Whatsapp? Duk babu su a wancan
lokaci. Ba a zancen tashoshin
rediyo da talabijin da sauran
hanyoyin sadarwa na yanar gizo
da muke da su a wannan zamani.
A takaice dai Husaini bai san
wainar da ake toyawa a Kufa ba
har sai da ya iso gaf da wannan
gari inda ya gamu da dan sakon
Muslim wanda ya aike shi bayan
ganin al’amurra sun rikice don ya
sanar da shi abinda ake ciki. AL
ISABA FI MA’RIFATIS SAHABA,
na Ibnu Hajar (1/228). A nan yana
da kyau mu ji ta bakin masu cewa
sayyidina Husaini ya san zahiri da
badini. Ya aka yi haka?

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

One response to “ME YA FARU A KARBALA 19(Dr. Mansur Sokoto)”
  1. Husain salaf Avatar

    To Allah ya shirye mu

Leave a Reply

Categories
Latest updates