ME YA FARU A KARBALA 21(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

Da aka ki karbar bukatar Husaini ta
komawa Makka sai ya ba da wasu
zabi guda biyu; ko dai ya tafi wurin
masu jihadi a matsayin daya daga
cikin sojoji ko kuma ya tafi wurin
Yazidu da kansa ya yi mubaya’a.
Amma dai duk wadannan muradun
basu samu ba domin Allah ya
zartar da kaddarar da ya hukunta.
Ya zama dole bayan haka ta faru
Husaini ya shirya don kare kansa
daga wulakanci.
A nan ne Husaini (R.A) ya yi wata
huduba a daren Tasu’a wadda a
cikinta ya fada ma ‘yan rakiyarsa
cewa fa yana ganin akwai
arangama a tsakaninsa da
wadannan mutane gobe. Sannan
ya yi izni ga duk wanda ke da
bukatar juyawarsa ya tafi. A nan
wasu suka yi amfani da wannan
dama kafin a wayi gari sun tafi
abinsu, bayan kuwa jiya su ne
suka ce aje a dauko fansa.
Wayuwar garin Ashura Husaini ya
shirya tare da mutanen da basu
wuce 50 ba daga asalin 72 da ya
fito da su domin su fuskanci
rundunar gwamnatin Ubaidullahi
mai soji 4000.
Abin tambaya a nan shi ne, ya aka
yi aka samu wannan adadin sojoji
a Kufa garin da yake na Shi’ah ne
zalla amma ga su sun zo su yaki
Husaini ko su kama shi? Ina duk
magoya bayan da suka sa hannu a
kan takarda? Ina masu mubaya’a
18,000 da suka damka
hannayensu ga Muslim dan Aqilu a
madadin Husaini?
Wannan shi ya sa malaman Shi’a
suka tuhumci mabiyansu da aikata
danyen aikin da ya faru a wannan
rana. Kafin mu kawo
maganganunsu bari mu kammala
fadin wannan abin kunya, abin
takaici da ya cimma al’ummar
musulmi a Ashurar shekara ta 62H.
Ku dakace mu.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates