ME YA FARU A KARBALA 20(Dr. Mansur Sokoto)

·

·

Husaini Ya Isa Karbala
Da sayyadi Husaini ya kusa isa
Kufa sai ya gamu da Umar bin
Sa’ad dauke da sakon kanensa
Muslim wanda sai yanzu ne ya san
cewa an kashe shi. Muslim ya
nemi Husaini da ya koma abinsa
tunda mutanen Kufa ba da gaske
suke ba. Shi dai Umar bin Sa’ad
daman yana cikin ‘yan Shi’ar Ali
kamar yadda shi ma wannan
sabon gwamna Ubaidullahi bin
Ziyad yake. Duba KITABUR RIJAL
na TUSI Shafi na 54. Don haka Bin
Sa’ad sai ya bada labarin kashe
Muslim yana kuka mai tsanani ta
yadda ya zaburar da ‘yan uwansa
da ‘ya’yan cikinsa, ya kuma ja
hankalinsu ga daukar fansa.
Husaini ya so ya komawarsa
amma sauran dangi na ganin dole
ne a isa Kufa zuwa daukar fansar
jinin dan uwansu.
Duk mai hankali zai iya lura da
hannun kaddara a cikin wannan
lamari. Domin kuwa ya za a iya
daukar fansar wanda hukuma ta
kashe shi? Kuma a kan wa za a
dauki fansa? Sannan su wa ye
zasu dau fansar? Husaini ba wani
shirin yaki da ya zo da shi. Bil hasili
ma kaffatanin na tare da shi mata
ne da kananan yara.
Ayari na farko da sayyidina Husaini
ya hadu da su sune dakaru 1000
da suka zo karkashin jagorancin
Hurru bin Yazid. Da suka hadu da
shi Husaini ya tambaye su, kun zo
tarbon mu ne ko yakar mu? Suka
ce, a’a. Mun zo ne mu kama ka.
Husaini ya ce, aah! Ba ku ne
mutanen Kufa da kuka gayyato ni
ba? Bayan ja-in-ja da muhawara
da suka tafka, Husaini ya jagoranci
sallar azahar inda wadannan
dakaru duk suka bi shi, sannan aka
ci gaba da tattaunawa. Daga
karshe Hurru ya yi masa alfarma ta
ya kyale shi ya juya da sharadin
kada ya kama hanyar Kufa ko ta
Madina.
Abinda ya fi kome ban mamaki shi
ne dawowar Umar bin Sa’ad –
wanda ya zo da labarin kisan
Muslim bn Akil a jiya – bayan ya
koma Kufa. A yanzu wai ya zo ne
yana jagorancin wani ayari na
dakaru 4000 dauke da umurnin
Ubaidullahi bin Ziyad na a kama
Husaini! To, ya aka yi suka gamu
da Husainin bayan ya canja
hanya? Babu shakka wasu ne
suka sulale suka je suka kai ma
wannan runduna labari. Sun dai
tarar da Husaini yana kan
hanyarsa har ya sauka a Karbala.
Bayan wasu muhawarori a
tsakanin su sayyidina Husaini ya
jaddada amincewarsa ga komawa
inda ya fito. Umar bin Sa’ad ya ce,
sai mun nemi amincewar gwamna
Ubaidullahi.
Da farko da aka sanar da shi,
Ubaidullahi ya ce ba damuwa a bar
shi ya komawarsa. Amma wani
fitaccen dan Shi’ah, makiyin Allah,
maras imani, shine Shamru bin
Dhil Jaushan wanda ya kasance
cikin sojojin sayyidina Ali kamar
yadda Shahrudi ya fada a cikin
littafinsa MUSTADRAK ILMI
RIJALIS HADITH (4/224), wannan
munafukin dan Shi’an sai ya yi
fadanci zuwa ga Ubaidullahi da
cewa, ai har yanzu Husaini na da
hatsari ga mulkin Yazid, domin
akwai yiwuwar in ma ya tafi ya
dawo. Don haka babu mafita in
ban da a kama shi.

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: