ME YA FARU A KARBALA 23(Dr. Mansur Sokoto)

·

·

Wa ya kashe sayyidina HUSAINI?
Bayan duk bayanin da ya gabata
na abinda ya faru, muna son amsa
wannan tambaya. WA YA KASHE
SAYYIDINA HUSAINI? Amma a
wannan karon littafan Shi’ah kadai
muke son su bada amsa.
1. Ga abinda Allamah As Sayyid
Muhsin Al Amin ya fada a cikin
A’yanus Shi’ah (1/34):
ﺑﺎﻳﻊ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ ﻋﺸﺮﻭﻥ ﺃﻟﻔﺎ ﻣﻦ ﺍﻫﻞ ﺍﻟﻌﺮﺍﻕ، ﻏﺪﺭﻭﺍ
ﺑﻪ ﻭﺧﺮﺟﻮﺍ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺑﻴﻌﺘﻪ ﻓﻲ ﺃﻋﻨﺎﻗﻬﻢ ﻭﻗﺘﻠﻮﻩ

‘Mutane 20,000 daga ‘yan Iraqi sun
yi ma Husaini mubaya’a, sun
YAUDARE shi kuma suka fito a
kansa, alhali mubaya’arsa na ga
wuyansu, kuma suka kashe shi”.
2. Ga kuma abinda Hurru bin Yazid
– daya daga cikin ‘yan rakiyar
Husain -ya ce ma rundunar da take
kokarin kashe HUSAINI a Karbala:
” ﺃﺩﻋﻮﺗﻢ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﻌﺒﺪ ﺍﻟﺼﺎﻟﺢ، ﺣﺘﻰ ﺍﺫﺍ ﺟﺎﺀﻛﻢ
ﺍﺳﻠﻤﺘﻤﻮﻩ، ﺛﻢ ﻋﺪﻭﺗﻢ ﻋﻠﻴﻪ ﻟﺘﻘﺘﻠﻮﻩ، ﻓﺼﺎﺭ ﻛﺎﻻﺳﻴﺮ
ﻓﻲ ﺃﻳﺪﻳﻜﻢ؟ ﻻ ﺳﻘﺎﻛﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻈﻤﺈ “.
“Yanzu zaku kira wannan bawan
Allah na kirki, sai da ya zo maku
sannan ku mika shi, sannan ku yi
tsalle a kansa don ku kashe shi,
har ya zama kamar wani fursuna a
hannunku?! Kada Allah ya shayar
da ku ruwa a ranar kishirwa”. Duba
AL IRSHAD na Al Mufid, shafi na
234 da I’LAMUL WARA BI A’LAMIL
HUDA na Tabrasi, shafi na 242.
3. Sai kuma abinda Tabrasi ya
hikaito cewa shi kansa sayyidina
Husaini (R.A) yana cewa:
” ﺃﻟﻢ ﺗﻜﺘﺒﻮﺍ ﺇﻟﻲ ﺃﻥ ﻗﺪ ﺃﻳﻨﻌﺖ ﺍﻟﺜﻤﺎﺭ ، ﻭﺇﻧﻤﺎ ﺗﻘﺪﻡ
ﻋﻠﻰ ﺟﻨﺪ ﻣﺠﻨﺪﺓ؟ ﺗﺒﺎ ﻟﻜﻢ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﺠﻤﺎﻋﺔ ﺣﻴﻦ
ﺍﺳﺘﺼﺮﺧﺘﻤﻮﻧﺎ ﻭﺍﻟﻬﻴﻦ ، ﻓﺸﺤﺬﺗﻢ ﻋﻠﻴﻨﺎ ﺳﻴﻔﺎ ﻛﺎﻥ
ﺑﺄﻳﺪﻳﻨﺎ، ﻭﺣﺸﺸﺘﻢ ﻧﺎﺭﺍ ﺃﺿﺮﻣﻨﺎﻫﺎ ﻋﻠﻰ ﻋﺪﻭﻛﻢ
ﻭﻋﺪﻭﻧﺎ، ﻓﺄﺻﺒﺤﺘﻢ ﺃﻟﺒﺎ ﻋﻠﻰ ﺃﻭﻟﻴﺎﺋﻜﻢ ﻭﺳﺤﻘﺎ، ﻭﻳﺪﺍ
ﻋﻠﻰ ﺃﻋﺪﺍﺋﻜﻢ. ﺍﺳﺘﺴﺮﻋﺘﻢ ﺇﻟﻰ ﺑﻴﻌﺘﻨﺎ ﻛﻄﻴﺮﺓ
ﺍﻟﺬﺑﺎﺏ، ﻭﺗﻬﺎﻓﺘﻢ ﺇﻟﻴﻨﺎ ﻛﺘﻬﺎﻓﺖ ﺍﻟﻔﺮﺍﺵ ﺛﻢ
ﻧﻘﻀﺘﻤﻮﻫﺎ ﺳﻔﻬﺎ ، ﺑﻌﺪﺍ ﻟﻄﻮﺍﻏﻴﺖ ﻫﺬﻩ ﺍﻷﻣﺔ ”
“Wai kam ba ku ne kuka rubuto
mana cewa, ‘ya’yan itace sun nuna
ba, kawai zamu zo mu sami
hadaddiyar runduna? Allah ya
abkar da halaka a gare ku ya ku
wannan taron wofi! Tunda kun
kwala mana kira a haukace,
sannan kuka daga mana takobin
da muke ganin a hannunmu yake
(Zaku kashe mu da shi), Sannan
kuka hura wutar da mun hasa ta ne
don makiyanmu kuma makiyanku.
A yanzu kun zama masu fada da
masoyanku, masu hada kai da
makiyanku. Kaico! A Lokacin da
kuke bamu mubaya’a kun yo sulu
kamar fari amma a yanzu kun
kakkabe hannayenku kamar ba ku
ne ba. Kai, Allah dai ya nisantar da
ku ya ku dawagitan wannan
al’umma” Duba I’LAMUL WARA na
Tabarsi, shafi na 949.
4. A nan ne kuma – in ji Mufid –
sayyidina Husaini ya yi masu bakar
addu’a yana cewa:
” ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻥ ﻣﺘﻌﺘﻬﻢ ﺇﻟﻰ ﺣﻴﻦ ﻓﻔﺮﻗﻬﻢ ﻓﺮﻗﺎ ﻭﺍﺟﻌﻠﻬﻢ
ﻃﺮﺍﺋﻖ ﻗﺪﺩﺍ، ﻭﻻ ﺗﺮﺽ ﺍﻟﻮﻻﺓ ﻋﻨﻬﻢ ﺃﺑﺪﺍ، ﻓﺈﻧﻬﻢ
ﺩﻋﻮﻧﺎ ﻟﻴﻨﺼﺮﻭﻧﺎ، ﺛﻢ ﻋﺪﻭﺍ ﻋﻠﻴﻨﺎ ﻓﻘﺘﻠﻮﻧﺎ ”
“Ya Allah! In har ka tsawaita
rayuwarsu to, ka tarwatsa su, ka
hahhargitsa su, kada ka bari su ji
dadin mai mulki ko wane ne sam.
Hakika sun kira mu da sunan
taimakon mu amma sai suka
zabura a kan mu zasu kashe mu”.
Duba AL’IRSHAD na Al Mufid,
shafi na 241 da Kashful Gummah
na Arbili (2/18 da kuma 2/38).
5. Al Ya’qubi a cikin Tarihinsa
(1/235) shi kuma cewa ya yi, Zainul
Abidin dan sayyidina HUSAINI
wanda Allah ya kaddari ya kubuta
ba a kashe shi ba a Karbala shi ma
ya jingina kisan Husaini da
iyalansa ga ‘yan Shi’ah, mutanen
Kufa duk kuwa da kukan munafurci
da ya tarar suna yi. Ga maganarsa
nan da nassinta:
ﻟﻤﺎ ﺩﺧﻞ ﻋﻠﻲ ﺑﻦ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ ﺍﻟﻜﻮﻓﺔ ﺭﺃﻯ ﻧﺴﺎﺀﻫﺎ
ﻳﺒﻜﻴﻦ ﻭﻳﺼﺮﺧﻦ ﻓﻘﺎﻝ” :ﻫﺆﻻﺀ ﻳﺒﻜﻴﻦ ﻋﻠﻴﻨﺎ ﻓﻤﻦ
ﻗﺘﻠﻨﺎ؟ “.
“A lokacin da Ali bin Al Husain ya
shiga Kufa – yana nufin bayan
rikicin Karbala – sai ya tarar da
matan garin na ta kuka da
hargowa, sai ya ce, “Af! Dubi
wadannan wai mu suke wa kuka.
To, wa ya kashe mu ne?”
Zamu takaita a haka, sannan mu
garzaya birnin Sham wurin Yazidu
mu ji abinda yake faruwa a can.
Ku dakace mu.

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: