BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM MU KARANTA TARIHI TARIHIN RIKICIN TATTAR (MAJLISI NA 6) (Dr Mansur Sakkwato)

·

·

Domin neman ƙarin bayani danna nan

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
MU KARANTA TARIHI
TARIHIN RIKICIN TATTAR
(MAJLISI NA 6)
Labarin ya fi dadi daga wadanda
suka gani da idonsu, duk da irin
rashin dadin sa. Ga yadda Ibnu
Kathir ya wasafta abinda ya faru:
“Sun far ma Bagadaza, suka kashe
duk wanda suka samu iko, maza
da mata, tsofaffi da kananan yara.
Mutane da yawa suka shiga cikin
rijiyoyi da wuraren kazamta. Aka yi
kwana da kwanaki a haka ba mai
iya fitowa. Wasu kuma sukan shiga
cikin shaguna su rufe kansu har sai
in Tattar sun ahamo sai su karya
kofofin ko su kone su da wuta.
Wasu sun samu sun haye tudanni
da saman gidaje inda can ma
Tattar suka rinka bin su suna
kashewa, jinainai na kwarara ta
cikin indararo. Wasu kuma sun yi
tsammanin su tsira a cikin
masallatai da wuraren karatu
amma ina! Ba wanda ya tsira daga
cikin wadanda suka buya a
wadannan wurare in ba Yahudawa
da Kiristoci ba, sai ko ‘yan Shi’a da
suka shige gidan waziri Ibnul
Alkami jagoransu da kuma kadan
daga cikin attajiran da suka yi
dabarar mika makuddan
dukiyoyinsu suka yi saranda suka
nuna zasu bada hadin kai.
Bagadaza ta koma kango, babu
kowa cikin ta sai ‘yan kalilan
wadanda suka sami kan su a cikin
tsoro da yunwa da kaskanci”.
Wannan duka wasaftawa ta Ibnu
Kathir ce malamin nan na tafsiri
wanda ya gane ma idonsa.
Wannan bala’in kuwa sai da ya
kwana 40. Kuma sun kashe abin
da ya tasar ma mutane miliyan 2 a
cikin wadannan ‘yan kwanaki.
Bayan haka ne Tattar suka
shelanta cewa an amintar da
mutane, sannan mutane suka rinka
fitowa daga cikin rijiyoyi da shadda
da magudanan ruwa, kai har da
makabartu. Mutane na bayyana
kowa bai gane wani saboda
canzawar halitta don tsananin
wuya da yunwa da tashin hankali.
Gawawwaki ko sun cika birnin
Bagadaza tuli-tuli kamar shara.
Ana haka sai kuma aka wayi gari
da ruwan sama abinda ya kara
yamutsa hazo ya hargitsa yanayi.
Warin gawawwaki ya haifar da
wata annoba wadda ta koma zama
sanadiyyar tagayyara da salwantar
wasu rayuka da dama. Daga
wannan gari har zuwa birnin Sham
ko ina ka bi marasa lafiya ne.
Sai da safenku. Hawaye.

Leave a Reply

Latest updates
Categories