BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM MU KARANTA TARIHI TARIHIN RIKICIN TATTAR (MAJLISI NA 7)(Dr Mansu Sakkwato)

·

·

Bayan da Tattar suka gama rusa
Bagadaza sai suka nada wani Ali
Bahadur a matsayin sarki suka bar
ma shi Ibnul Alkami a matsayin
waziri. Sannan suka tasar ma
Siriya da Falasdinu da Misra don ci
gaba da barna. Ibnul Alkami da bai
samu mulki ba bayan duk wannan
bala’i da ya aukar kuma wannan
sabon sarki bai sakar masa mara
ba ko kadan don rashin amincewa
da shi sai ya tare cikin gidansa har
bakin ciki ya kashe shi a cikin
watanni ukku.
Labarin Tattar a kasar Sham ba shi
da kyau ko kadan. Amma kafin su
iso Masar da Sham (Syria)
malamai sun riga sun tashi tsaye,
irin su Izzuddin bin Abdissalam
suka hadu a kan tunkarar
wadannan makiyan Allah, suka
zaburar da musulmi ga jihadi suka
yi yekuwa ga mahukunta suna
masu nacewa kan cewa babu wata
mafita ban da a tarbi wadannan
‘yan bala’i da zuciya guda ana
masu dogara ga madaukakin sarki.
Haka kuwa aka yi.
Daga cikin malaman da suka
jajirce a kan jan damarar yaki da
Tattar akwai shehun musuluncin
nan mujahidi Ibnu Taimiyyah
wanda ya taka rawa wadda babu
irin ta. Har ya kan yi rantsuwa
cewa, wallahi zamu yi galaba a
kan su. Idan an ce masa ka ce in
sha Allahu, ya kan ce: in sha
Allahu tahqiqan la ta’aliqan.
Ma’ana ya ce in sha Allah don
tabbatar da maganarsa ba don
yana shakka ba. Wannan kuwa
shine sha’anin wanda ya yi imani
da taimakon Allah ga bayinsa
muminai kamar yadda Allah yake
cewa: “Kuma ya zama alhaki a kan
mu mu taimaki mumminai”.
Malaman Sunnah sun jagoranci
wannan yaki suna dauke da tutoci
suna karanta ayoyi suna zaburar
da mutane a kan jihadi, sarakuna
suna bayansu, sannan sauran
mayaka.
Da sarki Saifuddin Qataz ya shirya
rundunarsa maimakon ya jira
isowar Tattar sai ya fara kai masu
hari inda ya samu gagarumar
nasara a wani wuri da ake kira “Ain
Jalut” a shekara ta 658H. Daga
nan kuma sai nasarar Allah ta ci
gaba da samuwa a hannun
musulmi. Ko bayan cikawar Qataz
sai da dansa “Baibaras” ya samu
nasarar tunkude makiya, ya mayar
da su baya har ma sai da ya kwato
duk garuruwan da a can baya suka
ci na kasar Sham.
Wani ikon Allah shi ne, da tafiya ta
yi tafiya, nasarorin Allah suka
kankama ga musulmi, rinjayensu
ya tabbata, sai sarkin Tattar
“Qazan” jikan Jinkizkhan ya
musulunta a shekarar 694H tare da
duk al’ummar da ke tare da shi.
Aka yi kasaitaccen bukin karbar su
a fadar sarkin musulmi “Tauzun”.
Aka shirya dawo ma musulmi da
kayayyakinsu da aka kwace, aka
soma raya garuruwan da aka lalata
da dai sauran su.
Sai maganar darussan da ke cikin
wannan tarihi. Ku dakace mu in da
sauran rayuwa.

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: