BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM MU KARANTA TARIHI TARIHIN RIKICIN TATTAR (MAJLISI NA 4)(Dr Mansur Sakkwato)

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
MU KARANTA TARIHI
TARIHIN RIKICIN TATTAR
(MAJLISI NA 4)
Birane biyu da muka fada a baya,
Bukhara da Samarqanda mun fade
su ne kawai a matsayin misali.
Amma bala’in ‘yan Tattar bai tsaya
a kan su ba domin sai da suka
tsallaka tekun da ake tsammanin
ba wata runduna da zata iya
tsallaka shi. Ba su da jirgin ruwa ko
guda, amma dawakansu sun iya
ruwa, don haka sai suka shirya
wasu manyan akwatuna suka zuba
makamansu a ciki sannan suka sa
masu fatun shanu don kada ruwa
ya lalata makaman, sannan
kowanensu ya rike wutsiyar
dokinsa, ya daura akwati a
kugunsa. Da haka suka tsallaka
ruwa. Kwatsam! Sai aka ji su a
garin sarki Khuwarizm Shah. Suka
tarwatsa Naisabur da Mazandaran
da Rayy (Tehran) da Hamazan da
Azrabejan da Irbil da duk sauran
garuruwan musulmi da ke
tsallaken tekun Jehon. Duk kuma
inda suka je sukan yi amfani da
fursunoni musulmi da suka kamo a
gari na baya suyi garkuwa da su,
sannan in sun gama su kashe su.
Wani lokaci kuma idan musulmi
suka buya bayan yaki ya yi zafi sai
Tattar su sa fursunonin da ke tare
da su suyi kira cewa jama’a ku
dawo! makiya Allah sun tafi. Sai
sun fito sai su gamu da gamon su.
Su kuma in sun kiya a kashe su.
Wani abin ban tsoro a game da
sha’aninsu shi ne cewa, bayan
karfi da suke da shi mutane ne
masu nacin gaske. Misali sa’adda
sojojinsu suka zo birnin
Khuwarizm wata 5 suka yi a
kewaye da shi kafin su samu buda
shi. A birnin Taliqan sun gamu da
mayakan da suka buwaye su,
amma sai suka kewaye shi har
tsawon wata 6, duk basu ci nasarar
karya shi ba. Sai da Jinkizkhan ya
zo da kansa sannan ya sake yi wa
garin zobe na tsawon wata hudu
sannan ya iya karya shi, ya kashe
duk al’ummar da ke cikin sa.
A takaice dai babu shakka musulmi
sun wulakanta matuka a wancan
lokaci, kuma tsoro ya shige su da
tashin hankali wanda babu irin sa.
Har ta kai mayaki daya daga cikin
Tattar zai iske mutane dari suna
fira ya hau su da sara da kisa har
ya kai karshen su gaba daya ba a
samu wanda ya kashe shi ba.
Wani ma sai ya kwantar da
musulmi sannan ya ce, na manta
takobina ka tsaya nan har in dawo,
kuma musulmin ba zai daga ba
saboda tsananin razana da mika
wuya. Wata mata daga cikin su ta
shiga wani gida ta karkashe
mazaje da dama ta kama wasu sai
daga baya suka gane macce ce
sannan wani daga cikin su ya
samu sa’ar kashe ta. Labaran
kamar yadda muka fadi a baya in
mutum na jin su kamar ba zai
gaskata ba.
Zamu ci gaba in Allah ya so.

Leave a Reply

%d bloggers like this: