BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM MU KARANTA TARIHI TARIHIN RIKICIN TATTAR (MAJLISI NA 8)(Dr Mansur Sakkwato)

·

·

Domin neman ƙarin bayani danna nan

Dalillan da Suka Karfafa Yakin
Tattar:
Tun da farko yana da kyau mu
gano dalillan da suka karfafa
bayyanar wadannan mahalukai
masu kama da aljanu:
1. Tattar sun dunfaro kasar
musulunci a daidai lokacin da
al’ummar musulmi take cikin rauni
a kowane bangare. Ga dai rarrabar
kawuna wadda Allah ya hana mu.
Ga talauci wanda ya faru a
sanadiyyar yawan ambaliyar ruwa
da aka yi shekaru ana yi wanda ya
kawo wahalar abinci da tsadar
rayuwa. Ga kuma ‘yan rigingimu da
aka yi ta yi tsakanin Ahlus-Sunnah
da tsirarun ‘yan Shi’ar da waziri ya
daure masu gindi. Ga kuma
karancin soja wadanda waziri ya
kokkore su daga aiki yana nuna
ma halifa cewa, akwai bukatar kula
da tattalin arziki, don haka bai
kamata a kashe kudaden
gwamnati a kan soji ba.
2. Halifan daular Abbasiyya na
wancan lokaci mutumin kirki ne,
mai son addini amma ba shi da
ikon kome a hannunsa in ban da a
birnin Bagadaza. Halifa kawai ya
zama wani dodo wanda ba a ko iya
ganin sa. An rufe shi cikin gida
daga shi sai barori da kuyangi. Bai
san abinda duniya take ciki ba,
kuma ita ma duniyar ba ta san
abinda yake ciki ba.
3. Kananan daulolin musulunci sun
yarda da shugabancin Bagadaza
kamar daular Ayubawa da ta
Gaznawa da ta Khuwarizmawa da
duk sauran kananan daulolin
musulunci in ban da daular ‘yan
Shi’a ta Masar da ta Sufaye a
Moroko. Su kam ba su ma amince
da halifa ba. Amma duka
wadannan daulolin tare da
amincewar su da gwamnatin
Sunnah ta Bagadaza ba su zaune
lafiya da ita. An yi ta yake-yake
wadanda suka raunana kowane
bangare. Akwai wata dirama da ta
faru a shekarar 529H a lokacin da
sarki Mahmud ya yi yunkurin juyin
mulki a kan Halifa Mustarshid, ya
kuma ci nasara har da kama Halifa
a hannu. Daga bisani kuma sarki
“Sabjar” ya shiga tsakani bayan
wani bore da talakawa suka yi, ya
sasanta har aka mayar da halifa a
kan kujerarsa. Shekara daya
bayan haka sai kuma sarki
Mas’udu ya bayyana nasa
tawayen, ya shelanta ya cire halifa
ya nada kanin babansa Al-Muktafi,
haka din kuma aka yi. Bayan
shekaru 11 aka samu wani rikici
tsakanin halifa Muktafi da
maigidansa abinda ya jawo halifan
ya sa aka rufe dukkan masallatai
har tsawon kwana 3 ba a sallah
cikin su. Bayan wasu shekaru 10
kuma aka sake wani yamutsi
tsakanin halifa da sarki
Muhammad dan sarki Mahmud
abin da ya jawo aka yi wata 2 ana
zaman dar-dar a Bagadaza. A
takaice dai koda Tattar suka zo ba
wani sarki da yake da karfi ko yake
da cikakken hadin kai da wani in
ban da Khuwarizm Shah. Don
haka da gamawa da shi sai fili ya
koma wayam; ba mai iya jayayya
da su.
4. A daidai lokacin da musulmi
suke cikin wannan rauni, sarakuna
suka shagala da wasanni da sabon
Allah, su kuma rundunar Tattar
runduna ce kammalalliya. Duk inda
suka zo basu bukatar kowa ya ba
su ko igiyar daure rakumi. Suna da
dawakai da rakuma da shanu
wadanda suke cin namansu,
dawakan da suke hawa kuma basu
bukatar a hauya masu dusa ko a
ajiye masu kasari ko wani abinci,
tonon kasa suke suna cin kwari da
ciyawa da duk abinda ya samu. Ga
su da yawan adadi wanda
mahaliccinmu kadai ya san
iyakarsa. Ba su da tsoro, ba su ja
da baya, ba su da jinkayi ko
miskala-zarratin ga mutane.
5. Akwai wasu kurakurai da
gangancin da sarakunan
musulunci suka yi musamman ma
dai Khuwarizm Shah lokacin da ya
kashe wasu ‘yan kasuwa da suka
zo daga kasar Sin ba bisa ga wani
dalili ba kuma ya kwace masu
dukiya. A lokacin da wannan labari
ya je ga Jinkizkhan sai ya aika
masa wasika yana barazanar zai
dau fansa, sai kuma
Khuwarizmshah ya kashe jakadan
ya sa aka aske gemun ‘yan
rakiyarsa ya ce musu su je su kai
labari. Daga nan kuma sarki
Khuwarizmshah ya je don yakar
Tattar ya tarar sun fita zuwa
Turkiyya don yaki da wani sarki
ana ce masa Kashlokhan.
Khuwarizm ya shiga garinsu, ya
auka ma matansu da ‘ya’yansu
amma bai bar garin ba sai da suka
cim ma sa suka gwabza yaki mai
tsanani. A cikin kwanaki uku suka
kashe masa jarumawa musulmi
20,000. Tare da haka su ma sun yi
hasarar rayuka ba iyaka. Tarihi ya
ruwaito cewa, saboda yawan jinin
da ya zuba na jama’a har zamewa
dawakai ke yi a cikinsa.
6. Kiristoci wadanda suka kasa
karya lagon musulmi a yakin Kuros
(Crusade) ‘yan shekaru kadan a
baya su ma sun taka rawa wajen
kwadaitar da Tattar a kan kama
kasashen musulmi. Suka rinka
nuna masu irin arzikin da ke cikin
kasashen da saukin cin galaba a
kan su. A lokacin da Tattar suka
kama kasashen Sham sun
bayyana goyon bayansu ga
kiristoci har sukan sa musulmi su
duka ma Kuros don wulakanta su.
7. Akwai kuma tasirin munafukan
musulmi, ina nufin ‘yan Shi’ah. Tun
a zamanin sarki Nasir dan sarki
Mustadi’u bi amrillah wanda ya fi
duk sarakunan daular abbasiyyah
dadewa (ya yi sarauta shekaru 47
daga 575H-622H) shi’anci ya fara
karfi a cikin daular musulunci
saboda kisisinar da ‘yan Shi’ah
suka yi ma sarki na aiko masa da
takarda a sirrance rubuce da duk
abinda ya yi a cikin dare, shi kuma
sai ya yi tsammanin gaskiya ne
Imaman Shi’ah sun sai gaibi kuma
su ne ke fada masu sirrinsa.
Alhalin kuwa yan leken asiri gare
su daga cikin barorinsa. Wannan
sarki – saboda shi’ancinsa – ya yi
ta nuna ma Tattar goyon baya da
ba su asirran musulmi. A
kodayaushe yana aika masu
wasiku. Sai na biyu shi ne sarkin
garin Musil wanda ake ma lakabi
da Al-Malik Ar-Rahim. Wannan
sarki shi ma ya dade yana sarauta
(tsawon shekaru 50), kuma dan
Shi’ah ne da ya raya wasu al’adu
da bukukuwa na kiristoci, ya kuma
kulla alaka mai karfi da Tattar har
da aurar da dansa Salihu ga ‘yar
sarkin Tattar na wancan lokaci
Hulako, duk da yake auren bai yi
karko ba kuma ya haifar da rashin
jituwa a tsakanin su amma dai ya
bada goyon baya da gudunmawa
ga Tattar har ma mayakansa sun
taimaka wajen yakar Bagadaza.
Na uku shi ne uwa uba ga wannan
al’amari, ina nufin Waziri
Mu’ayyiduddin Muhammad Ibnu
Ahmad Ibnul Alkami wanda ya hau
mukamin waziri a zamanin sarki
Musta’asim tsawon shekaru 14.
Kuma ya yi iya kokarinsa ya
daukaka shi’anci amma Ahlus-
Sunnah suka rinjaye shi, sai ya bi
ta hanyar hila da makirci kamar
yadda muka riga muka fada.
Zamu ci gaba in Allah ya so.

One response to “BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM MU KARANTA TARIHI TARIHIN RIKICIN TATTAR (MAJLISI NA 8)(Dr Mansur Sakkwato)”
  1. […] BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIMMU KARANTA TARIHITARIHIN RIKICIN TATTAR(MAJLISI NA 8)(Dr Mansur Sakkwato). […]

Leave a Reply

Latest updates
Categories