BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM MU KARANTA TARIHI TARIHIN RIKICIN TATTAR (MAJLISI NA 5) (Dr Mansur Sakkwato)

Danna nan domin shiga karatu Online

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
MU KARANTA TARIHI
TARIHIN RIKICIN TATTAR
(MAJLISI NA 5)
Babbar Musiba: Faduwar
Bagadaza
Duk abinda Tattar suka yi a baya
bai taka kara ya karya ba in aka
ambaci labarin abinda suka yi ma
hedikwatar musulunci ta
Bagadaza. Ita dai Bagadaza Allah
ya sa mata kwarjini a idon Tattar
kasancewar ta hedikwatar daular
musulunci ta duniya gaba daya.
Amma hukuncin Allah ya kaddari
cewa, sarki mai ci a wancan lokaci
Halifa Musta’asim billah ya yi
sakarcin da ya mika wani babban
mukami ga wani dan Shi’ah shi ne
Ibnul Alkami wanda shi ne ya hada
kai tare da Khawwaja Nasiruddin
Al-Dusi – suka jawo Tattar suka
kwadaitar da su ga kama wannan
birni.
Siyasar da Waziri Ibnul Alkami ya
bi ita ce, ya yi duk kisisinar da ya
sa aka mayar da sojoji a karkashin
ofis dinsa, sai ya yi ta korar su aiki,
tun suna 100,000 har suka dawo
kimanin 10,000. Ya bar sauran
babu albashi na tsawon lokaci, ya
kwace masu makamai, ya lalata
aikinsu. Har ta kai ma sojoji sun
koma ‘yan maula don neman
abinci, ba su da kwarjini ko kadan
har zanbo mawaka ke yi musu.
Sannan sai ya rubuta ma sarkin
Tattar yana kwadaitar da shi ga
daular Ahlus-Sunnah yana yi masa
alkawarin ba shi cikakken hadin
kai. Haka kuwa aka yi.
Da farko Tattar basu amince ba,
amma da suka aiko wakilai suka
gane ma idonsu gaskiyar lamarin
yadda daular musulmi tayi rauni
sai suka amince. A bangaren halifa
kuma sai waziri ya yi ta nuna masa
cewa, ya kamata ayi sulhu da
Tattar don ba a iyawa da su. A
lokacin da suka iso kuma sai ya
nemi iznin Halifa don ya tattauna
da su a sansaninsu na bayan gari.
Da yaje tare da mukarrabansa
suka gama kitsa makircinsu sai ya
dawo ya ce ma sarki an samu
daidaitawa, kuma za a aurar da
diyar sarkin Tattar ga dan sarki
Musta’asim billah. Suka kuwa
gaskata shi, aka fita bayan gari da
duk manyan gari masu mukaman
sarauta da limamai da alkalai da
malamai da dukkan masu alfarma
su kimanin mutane 700. Haka suka
tafi babu makami ko daya a tare da
su. Sai da suka isa wurin tukuna
suka gane wainar da waziri ke
toyawa. Da farko aka hana su isa
sai 17 kawai daga cikin su. Daga
bisani aka rinka dibar su a hankali
zuwa daurin auren da ba su gani
ba. Aka rinka tozarta su irin
tozartawar da ba ta sifaituwa
sannan daga bisani a kashe su a
zo da wasu.
A gaban sarki aka kamo babban
dansa Abul Abbas aka kashe shi,
sannan mai bi masa Abul Fadl,
sannan aka kama karaminsu
Mubarak. Sai kuma kannen sarki
mata Fatima da Maryam da
Khadija. Sannan aka kwashe duk
budaren da ke gidan sarki. Sauran
labarin kuma ba shi faduwa. Daga
bisani suka shiga cikin gari. Suka
kama fadar sarki. Suka rinka sa a
kira dattijo ya zo da iyalansa gaba
daya, sannan a gargada su zuwa
makabarta a yanka shi a gaban
iyalansa, sannan su zabi wadanda
suke so daga cikin matansa ko
‘ya’yansa mata suyi lalata da su.
Wadanda suka fi gamuwa da
wannan wulakancin kuwa su ne
Hashimawa dangin Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam saboda tsananin
haushinsu da dan Shi’ar yake ji. A
duk tsawon lokacin da suka yi a
wannan birni babu masallacin da
aka daga kiran sallah balai ayi
ikama. Waziri Ibnul Alkami kuwa ya
sheke ayarsa, ya fashe haushinsa
a kan malaman sunnah iyakar
zarafi. Daga cikin wadanda ya sa
aka kamo aka azabta sannan aka
kashe su har da shehun malamin
nan Muhyiddin dan babban shehin
malami kuma mawallafi Abul Faraj
Ibnul Jauzi bayan an yanka
‘ya’yansa Abdullahi da
Abdurrahman da Abdulkarim.
Daga karshe aka kashe halifan
kansa a cikin wani buhu na fata da
aka rinka dukan sa a ciki wai don
kada jininsa ya zuba a kasa don
matsafa sun ce in jininsa ya zuba
akwai matsala. Sannan bala’in ya
ida game gari.
Zamu ci gaba. Allah ya sawwaka.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates