ME YA FARU A KARBALA 5(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

A cikin babban kundin tarihin da
Ibnu Asakir ya wallafa ya kawo
hadisai masu dinbin yawa a kan
zagin Yazid kamar yadda ya
al’adanta a duk wadanda yake
kawo tarihinsu. Sai ka ga ya kawo
ruwayoyi masu yawa a kan yabon
mutum, sai kuma ya kawo wasu
irin su na sukar sa. Muradin
mawallafa a wancan lokaci shi ne
tabbatar da riwayoyin kowane
bangare na masoya da masoka.
Don haka ya zama dole kowace
ruwaya a jingina ta ga inda aka ji
ta don mai karatu ya zama cikin
basira. Basu san za a kai ga irin
wannan lokaci da nassin kawai ake
kallo ba, ba a ma san su wane ne
maruwaitansa ba.
Wannan shi ya sa sai ka ga mai
yabo ya damfare ma wadannan
riwayoyi, mai suka kuma yana ta
cika baki da wadancan.
Wani ya tada jijiyoyin wuyansa a
kan wata matsala, sai na ce masa
kawo nassi. Ya ce, a dauko Ibn
Kathir, ko da aka dauko ruwayar
daga Muhammad bn Al-Mubadir
ne. Na ce masa ka san wannan?
Bai sani ba. Ko da aka dauko
littafan Rijal sai ga shi babu abin
yabo ko dan kadan a tare da shi.
Malaman Sunnah kadai ne ke iya
tantancewa, su cire aya su raba ta
da tsakuwa, kowane mutum kuma
suyi masa adalci, su ajiye shi inda
ya cancanta. Wannan ya sa suka
kasance mafi adalcin al’umma.
Dubi yadda Ibnu Taimiyyah ya yi
wa ‘yan Shi’ah adalcin cewa, gara
ma akidarku da ta Khawarij. Sun fi
ku hatsari da sharri nesa. Amma
banbancinku da su shine su ba sa
yin karya (don sun dauki yin karya
kafirci ne) ku kuma kuna shara ta
(don a wurinku halas ce in an yi ta
da sunan Taqiyyah, kamar yadda
Zina take halas a wurinku idan an
yi ta da sunan Mut’ah).
Kada mu je da nisa. Hadisan Ibnu
Asakir na zagin Yazid kaffataninsu
idan ka duba isnadansu “Made in
Iraq” ne. Ka ga kuwa ga adalci bai
kamata shugaban da ya ke Sham
a karbi shedun mutanen Iraqi kadai
a kan sa ba. Ko ba kome akwai
dadaddiyar adawa a tsakani. Kai
wasu ma in ka sa hankali kana
gane cewa zuki ta mallau ne.
Kamar Hadisin da ya ce wai
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa
Alihi Wasallam ya ga Mu’awiyah ya
dauki Yazid, sai ya ce “Ga dan
aljanna can ya dauko dan wuta”.
To, ina Mu’awiyah ya ga Yazid a
zamanin Manzon Allah? Mutumin
da a lokacin ko uwarsa ma ba a
aura ba!
Haka dai makaryata ke yin lamarin
nasu. A hadisan yabo ma zaka yi
ta ganin irin wannan. Dubi wani
Hadisin da aka yi ta yawo da shi
kwanakin baya a Facebook wai
Annabi Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam ya daga Hasan da
Husaini ya ce ma sahabbai “Da
wadannan ku ke shiriya, kuma da
su ake maku kaza da kaza…”. To,
ka ga yaran da aka haifa bayan an
saukar da fiye da rabin Alkur’ani,
an sha gwagwarmaya da arna, an
ci azabarsu, har an yi hijira kuma
an buga da su ba wuri guda ba har
an ci zarafinsu, karatu ya yi nisa
sasai koda aka haife su, a ce
wadannan yaran su ne zasu
shiryar da wadancan da ke tare da
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa
Alihi Wasallam, wadanda suka
kwashe shekaru kusan 20 suna
dibar shiriya daga wurinsa, ka ga
wannan ba maganar da mai
hankali ke saurarawa ce ba.
Falalar da Hasan da Husaini suka
samu ta yin shahada, da shedar da
kakansu ya bayar cewa su ne Allah
ya basu mukamin shugabancin
matasa a aljanna, wannan ya
wadatar da su daga irin wannan
shirme.
Haka zaka ga aya ta sauka a
Makka amma ‘yan Shi’ah su jajirce
Ali take nufi tare da Hasan da
Husaini. In ka ce a’a, a dai duba
domin lokacin ba a ma aurar da
mahaifiyarsu ba ballantana a haife
su sai su ce, ji shi, makiyin
Ahlulbaiti!
To, Yazidu dai wasu riwayoyi na
Ibnu Asakir da wasu marubuta da
dama sun zarge shi da shan giya,
wasu kuma sun wanke shi tsabal
daga wannan tuhuma. Daga cikin
wadanda suka wanke shi din kuwa
har da kanen sayyidina Husain,
Muhammad bin Ali bin Abi Talib
wanda aka fi sani da Ibnul
Hanafiyyah. Nan gaba zamu kawo
cikakkiyar maganarsa a kan Yazid
in Allah ya so.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates