Hadisan Annabi (1)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Mair Rubutu: Hamza Diso


Alkur’ani mai girma, tare da hadisan Annabin tsira sune matsotsar farko da ake daukar addini acikin su, wannan yasa Annabi kansa da sahabbansa suka bawa hadisi muhimmancin gaske, Don kuwa sai da hadisin ne za a fahimci Alkur’ani kamar yadda Allah ya saukar.

Ga kadan daga cikin hanyoyin da Annabi da sahabbansa suka bi wajen kare hadisi ta yadda zai dawwama tare da Alkur’ani duk kuwa da cewar sun San Allah zai kare shi kamar yadda zai kare Kur’ani

(1. Annabi ya kwadaitar da Sahabbansa haddace hadisi kamar yadda yake da kuma isar dashi kamar yadda sukaji har ma yayi Kyakykyawar addu’a ga duk Wanda yayi hakan

Annabi yace:

نضر الله امرأ سمع منا شيئا فبلغه كما سمع

Allah ya haskaka fuskar duk Wanda yaji wani abu daga gare ni ya kuma isar dashi kamar yadda yaji

wannan hadisi sahabbai dayawa suka ruwaito shi kamar ibn mas’ud, Zaid bn Thabit, Anas, Abud darda’i, Mu’az da jubair. Haka Ahmad, Abu Dawud, tirmizi, ibn majah, Hakim, dabarani Dama wasu dayawa sun fitar da hadisin cikin littattafansu kuma hadisi ne mai inganci.
Sannan akwai wasu hadisan da suke nuni akan kwadaitar da haddace hadisi da kuma isar dasu dayawa, sai dai na Fadi wannan Kawai Don takaitawa.

(2. idan Annabi Zai Fadi hadisi (don a haddace) Yakan maimaita sau uku kuma a hankali ba tare da sauri ba.

Imamul Bukhari da tirmizi da hakim da Ahmad da wasunsu sun ruwaito hadisi da isnadansu zuwa Anas dan Malik yace:

أنه كان إذا تكلم بكلمة، أعادها ثلاثا حتى تُفهم عنه، وإذا أتى على قوم فسلَّم عليهم، سلَّم عليهم ثلاثا.

Annabi ya kasancewar idan ya Fadi magana sai ya maimaita ta sau uku har sai an gane, haka kuma idan yaje wajen mutane yanayin musu sallama har sau uku”(idan basu ji sun amsa ba).

Wannan hanya ta taimakawa sahabbai wajen haddace maganganun sa sosai kuma dama ga lafiyayyar kwakwalwah da aka sansu da ita.

(3. Annabi yana bin hanyoyin da zasu saukakewa sahabbai haddace maganar sa kamar:

  • Buga misali a cikin magangansa, Wanda misalan da ya dinga bugawa malamai sunyi rubuce rubuce akansu.
  • yi musu tambaya kafin ya basu amsa Don ya jawo hankalinsu.
  • mai-mai ta magana ɗaya a gurare daban-daban don kowa yaji dama wasu hanyoyin daban banda wadannan.

(4. Rubuta maganganun sa:

Akwai sahabbai da dama da suka dinga rubuta hadisan Annabi kamar Abdullah Dan Amr Wanda hadisan daya rubuta sun doshi dubu, da kuma sa’ad bn ubadah da Aliyu dan abi dalib da Abu hurairah Dama wasu.

Shi kansa Annabi yayi shiftar bayanai an Rubuta Su an aikawa wadanda suke nesa da Madina kamar rubutun da yasa akayiwa wa’il bn hujr Wanda ya bayyana ginshikan musulunci a ciki, da kuma littafin da ya rubutawa amr bn hazmn Wanda acikin sa akayi bayani akan abubuwa dayawa, Dama wasu litattafan daya aika gurare daban-daban, badan gudun tsawaitawa ba da na fade su da inda aka ruwaito su.

(5. Sahabbai sun lazimci Annabi ta yadda mutum idan baije majalisin Annabi ba to zai tura wakili ya jiyo masa abinda aka ce kuma ya haddace kamar yadda sayyidina Umar yake yi shi da Makocinsa.

(6. Zaman Yin muraja’ar hadisi tsakanin sahabbai da mai-mai ta shi, bari ma Su da kansu sunyi ta yiwa tabi’ai wasicci dayin haka

Wannan kadan Kenan daga cikin yadda aka kula da hadisi a zamanin Annabi صلى الله عليه وسلم

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories