DARASIN LITTAFIN SHUBUHOHIN SHI’A A MAHANGAR SHARI'A(3)(Mal. Aminu Ibrahim Daurawa)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Bismillahir Rahmanir Rahim
Cigaba da darasinmu na littafin
“SHUBUHOHIN SHI’A A
MAHANGAR SHARI’A”.
–Wallafar (Abu Abdullahi) Hamza
Uba Abubakar Kabawa
–Gabatarwar Muhammad Aminu
Ibrahim Daurawa
–Darasi na 3
Darasin mu nay au zai yi Magana
ne akan wasu tushe da aka gina
addini akansu.
1) Ingattacen dalili
2) Dalilin ya dace da fahimtar
mutum
3) Dalilin ya dace da mahangar
magabata na kwarai.
Duk akidar da ba’a dora ta akan
wannan matakai ba, to ko shakka
taci karo da koyarwar addinin
musulunci.
Domin Karin bayani ko tambaya a
tuntubi : –
Hamza Uba-
08028751610-08059517410-08093632636
Muhammad Aminu Ibrahim
Daurawa: – 08023309111.
BAYANI A KAN WASU DAGA
SHUBUHOHIN DA‘YAN SHI’A
SUKE AMFANI DA SU.
Kafin mu fara bayani a kan wasu
daga cikin wadannan shubuhohi
da ‘yan Shi’a suke amfani da su
wajen yaudarar mutane, yana da
kyau al’umma su fahimci ka’ida
guda daya muhimmiya.Wannan
ka’idar kuwa ita ce, kungiyar Shi’a
tare da kashe-kashenta, kungiya
ce da aka vullo da ita, aka kuma
gina ta a kan tushe mara asali,
tushe na karya, da son zuciya.
Saboda haka duk wani dalili da
‘yan Shi’a zasu kawo wajen yada
akidarsu, baya wuce dayan dalilai
guda biyu.
Na daya: Ko dai dalili na karya,
kamar Hadisai marasa tushe da
asali ko kuma gurvataccen Tarihi
wanda aka kago.
Na biyu: Ko ya zamo su yi amfani
da ayar Alkur’ani da Hadisai
ingantattu, ko tabbataccen Tarihi,
amma wadanda ko alama ba su da
alaka da akidarsu. Saboda babu ta
yadda za’a yi, ayar kur’ani ko
ingantaccen Hadisi su goyi bayan
karya.
Domin shi Ubangiji gaskiya ne,
maganarsa ma gaskiya ce. Kamar
yadda Manzon Allah (S.A.W) yake
gaskiya, kuma dukkan
maganganunsa suke gaskiya.
Babu kuwa ta yadda za’a yi Allah
da Manzonsa su goyi bayan karya.
Kamar yadda gaskiya ba zata tava
goyon bayan son zuciya ba. Allah
(S.W.T) yana cewa “Da a ce
gaskiya zata bi son zuciyarsu to
lallai da sama da kasa da duk abin
dake cikinsu ya ruguje ya lala ce”
Don haka ‘yan Shi’a sun kauce
hanya ta gaskiya, sun kuma va ce
wajen kafa dalili ko abin da dalili
yake nunawa.
Daga cikin mafi shaharar
shubuhohin da ‘yan Shi a suke
tinkaho da su, suke kuma yada su
a cikin al’umma akwai shubuhohi
kamar haka:
Mu hadu a rubutu mabi da wannan.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

One response to “DARASIN LITTAFIN SHUBUHOHIN SHI’A A MAHANGAR SHARI'A(3)(Mal. Aminu Ibrahim Daurawa)”
  1. […] Source: DARASIN LITTAFIN SHUBUHOHIN SHI’A AMAHANGAR SHARI’A(3)(Mal. Aminu Ibrahim Daurawa) […]

Leave a Reply

Latest updates
Categories