KIRISTANCI (I)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

By: Hamza Diso


Hakikanin magana kiristanci bashi da tushe mai karfi wanda zai rike addinin ya bashi kariya daga sukan masu bincike da neman gaskiya.

Ta kowanne bangare ka dubi kiristanci kai tsaye zakaga gurin suka, fara daga kan aqida wadda ta sabawa dukkannin abinda annabawan baya suka zo dashi, kawo kan kamanceceniya mai karfi tsakanin addinin da sauran addinan gargajiya wadanda ‘yan Adam suka kirkira, da ma abubuwa dayawan gaske da suke nuni kai tsaye akan cewar lallai wasu masu son rai tare da wasu masu kishin addinin amma basu da wadataccen ilimi sun jirkita addinin daga yadda yake.

Amma ni zanyi rubutu insha Allah akan tabbatar da cewar babu wata hanya mikakkiya da kirista yake da ita a yau wadda za ta hadashi da Allah kai tsaye, don a gaskiyar magana babu wani littafi da yake hannun mu a yanzu wanda yake kai tsaye daga Allah ko daga Yesu, zan tabbatar da wannan maganar insha Allah ta hanyar gamsassun dalilai.


Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories