Sunayen Allah da siffofinsa

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Mairubutu: Hamza Diso


Bibiyar sunaye da siffofin Allah da fahimtar su da bautawa Allah dasu kofa ce mai fadi da take kai bawa zuwa ga yardar Allah da kuma kyakyakyawan sanin Allah gwargwadon iko

Allah yana da sunaye masu yawan gaske wadanda bamu San Adadin su ba, duk da cewa ya ware wasu guda 99 yace: duk Wanda ya sansu ( sanin ma’anar su da bautawa Allah dasu) to zai shiga Aljanna. to amma fa ba su kadaine sunayen sa ba domin imamu Ahmad cikin musnad da Hakim a mustadrak da wasun su sun ruwaito hadisi da isnadan su zuwa Abdullahi dan Mas’ud daga Annabi salatin Allah da sallamar sa a gareshi lokacin da ya bada Addu’ar da Wanda yake cikin damuwa ko bakin ciki zai karanta ta, cikin Addu’ar yake cewa: ya Allah ina rokon ka da duk sunayen ka da ka sanyawa kan ka ko ka sanar da wani bawan ka ko ka saukar dashi (sunan) cikin litattafan ka ko ka kadaita da Sanin sa…..

Wannan hadisi – ingantacce- yana nuna akwai sunaye da Allah ne kadai ya sansu.

Duk suna daga cikin sunayen Allah yana kunshe da ma’anar sunan da kuma siffofi. Misali; sunan Allah Alwahhabu yana kunshe da ma’anar sunan wato mai cikakkiyar kyautar da babu mai irin ta, Wanda yake bada abin dayaso komai yawan sa babu Wanda zai iya bayar da abinda ya hana ko ya hana abinda ya bayar, taskarsa bata raguwa, da ace mutane da aljanu na da da kuma na yanzu da wadanda zasu zo nan gaba, da zasu tsaya a guri guda kowa ya tambayi Allah bukatar sa kuma a bawa kowa abinda yake so, to da hakan bazai rage komai a cikin taskar Allah ba sai gwargwadon abinda Allura zata ragewa teku idan an tsoma ta a cikin an zare.

Wannan bangare kenan na ma’anar wannan sunan ALWAHHABU to haka sunan yana ishara akan siffofin Allah kamar

  • Samuwar Allah din, don sai akwai shi sannan zai yi kyauta
  • Yawan kyautar Allah
  • Wadatuwar Allah
  • Jinƙai na Allah ta yadda yake yiwa bayinsa kyauta iri-iri Alhalin suna saɓa masa dare da rana

Ko wanne suna ka dauka zaka samu abubuwa daban daban a cikin sa.

Sannan sunaye da siffofin Allah ana amfani dasu wajen neman biyan bukata awajen Allah, ta yadda kowanne mai bukata zai duba sunan daya dace da bukatarsa sai ya kira Allah da wannan sunan.

Misali: mai Neman gafara zai iya kira Allah da sunan Algafuur (mai yawan yin gafara da yafiya, mai gafarta zunubai komai girman su kuma komai kankantarsu).

Mai Neman Arziki ko haihuwa ya kira Allah da sunan Arrazzaq ko Alwahhab mai Neman a daukar masa fansa ya kira sunan Aljabbar Almutakkabir Al’aziz da makamantan su, abin nufi dai kowa ya kira Allah da sunan da zai dace da bukatarsa

Sannan bai halatta ga bawa ya kirkiri suna ko siffa ya jinginawa Allah ba tare da dalili saukakke daga sama ba, haka bai kamata a kira Allah da sunan da bamu da tabbas akan ingancin sa ba kamar YAHWA, Wanda muka gani cikin littattafan yahudu

Ana iya rantsuwa da kowanne suna daga cikin sunayen Allah ko siffofin sa

Ya Allah mai yawan gafara ka gafarta mana zunuban mu. ya mai shiryarwa ka shiryar damu zuwa tafarkin ka ka tashemu a tawagar masoyan ka tare da Annabawa da siddikai da shahidai da sauran bayi na gari. Ya Allah Wanda babu abinda yake gagararsa a sama ko kasa ya mabuwayi ya mai son bayinsa ka karemu daga dukkannin abun ki, (mummunan abu) ka bamu izza akan makiyan ka, ka Sanya mu cikin masoyan ka.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories