KHUDUBAR MU TA JUMU'AH A MASJID QUR'AN(Sheikh Isa Ali Pantami)

·

·

A Yau khudubarmu a MAJID
QURAN’ tayi magana Akan
BABBAR WASIYYAR MANZON
ALLAH (SAW) ga musulmai. In da
Abu Zarriy (RA) ya shiga gun
Annabi (SAW) yace Yaa Manzon
Allah kamin wasiyya. Sai Annabi
(SAW) yace: Ina maka wasiyya da
TAQWA domin shine adon
al’amuranku gaba daya.
Sai Abu Zarriy yace Yaa Manzon
Allah ka k’ara min wata wasiyyar.
Sai Annabi (SAW) yace: Ina
umurtanka da karatun Al-Qur’an da
Ambaton Allah domin shine
Ambatonka a SAMA kuma
HASKENKA a bayan KASA.
Sai yace Yaa Manzon Allah ka
k’ara min wata wasiyyar.
Sai Annabi (SAW) yace: Ina hana
ka yawan DARIYA domin yana
kashe ZUCIYA kuma yana lalata
HASKEN FUSKA.
Sai Abu Zarriy yace Yaa Manzon
Allah ka k’ara min wata wasiyyar.
Sai Annabi (SAW) yace: ka fad’i
GASKIYA komai dacinta.
Sai Abu Zarriy yace Yaa Manzon
Allah ka k’ara min wata wasiyyar.
Sai Annabi (SAW) yace: Yace kada
kaji TSORON ZARGIN KOWA a
cikin bin Umurnin Allah.
(Ahmad, Dabaraniy, Ibn Majah da
Hakim sun ruwaito

3 responses to “KHUDUBAR MU TA JUMU'AH A MASJID QUR'AN(Sheikh Isa Ali Pantami)”
  1. Assalamu alaikum malam Allah ya kara maka kwazo da basira Allah kuma ya sakama da alherinsa duniya da lahira.

  2. Assalamu alaikum malam Allah ya karamaka kwazzo da basira,ya kuma sadaka da alherinsa na duniya da lahira.Allah ya taimaka.

  3. […] Source: KHUDUBAR MU TA JUMU’AH AMASJID QUR’AN(Sheikh Isa Ali Pantami) […]

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: