Kaddamar da hankali akan Nassi

Tun zamanin da ta gabata an samu ƙungiyoyi masu kira zuwa ga ɗaukaka Hankali kan Nassi. Ƙungiya da tafi shahara da wannan Tunani itace kungiyar Mu’utazila. Wanda ta fara yaɗuwa a ƙarshen daular umawiyyah wacce daga bisani ta bayyana sosai a lokacin daular Abbasiyya. Sun kasance suna fifita hankali akan nassi. Kuma sun kasance suna kore nassin hadisi da bata dace da hankalinsu ba. Su kuma yi tawilin Nassin Al-Qur’ani domin ta dace da tunaninsu.

Toh a wannan zamani ma ba’a gushe ba ana samun masu irin wannan tunani, koda ko basu kira kansu da cewa su mu’utazilawa bane. Masu wannan da’awah a wannan zamani suna fifita hankalinsu da tunaninsu kan nassin Hadisan Manzon Allah. Sukan yi amfani da hankali wurin yin hukunci kan hadisan Annabi Sallallahu alaihi Wasallama. Wacce ta dace da hankalinsu sai su inganta ta, wacce kuma taci karo da hankalinsu sai su mayar da ita. Wasu lokuta sukan nuna cewa ai su suna amfani ne da Al-Qur’ani. Sukan yi amfani da wasu ayoyi na Al-Qur’ani da gurguwar fahimta wurin mayar da hadisan Annabi ingantattu da da’awar cewa hadisan sunci karo da ayoyin.

idan suka tashi yin hukunci wa hadisi basu komawa kan dokoki da maluma suka tanada wurin yin hukunci kan hadisi, sai dai su koma zuwa ga hankalinsu.

Wasu daga cikinsu masu kore hadisai baki ɗaya Sukan riya cewa ai Hadisan Annabi basu dace da wannan zamani ba. Kuma har ila yau ba’a da yaƙinin tabbattuwarsu.

Wasu kuma Sukan kira cewa a zo abi Al-Qur’ani. Ayi watsi da Sunnah da ta saɓa da hankalinsu da tunaninsu.

Abin lura anan shine:

Shin Hadisan Manzon Allah wahayi ne ko kuma kawai zantuka ne ta Manzon Allah wacce ba dole ne ayi riƙo dasu ba?

Haƙiƙa duk wani musulmi mai ɗan ƙaramin ilmi a addini zai sani cewa Hadisan Annabi Sallallahu alaihi Wasallama suma wahayi ne kaman yadda Al-Qur’ani yake wahayi. Kuma acikin Al-Qur’anin ne Allah yayi umarni da ayi riƙo da sunnah.

Allah yace:

وما ينطق عن الهوى* إن هو إلا وحي يوحى

Surat- Annajm 3-4

Baya bisa son zuciya. Haƙiƙa wahayi ake masa.

Wannan ayoyi sun nuna cewa Duk maganar da Annabi yayi Shari’a ne. Sai abinda yazo ya nuna ba haka ba. Ko kuma ya nuna cewa ta shafi shi annabin ne shi kaɗai.

Sannan kuma babu yadda za’ayi mutum ya aiwatar da wannan addini ta hanyar data dace har sai yayi amfani da sunnar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi. Domin Shi yawanci Al-Qur’ani yana zuwa da hukunci ne a dunƙule, sai sunnah(Hadisi) yazo yayi bayaninsa dalla dalla. kamar yadda Allah ya bada umarnin ayi Sallah. inka duba cikin Al-Qur’ani babu inda zaka sami siffar Sallah da yau musulmai sukeyi a duniya. Babu inda Allah yayi bayani dalla dalla haka. Amma annabi ne ya nuna mana yadda akeyi kuma aka rawaito ƙarni zuwa ƙarni har ya iso garemu, ta yadda babu wanda ya isa yau yace wannan siffar bata inganta ba.

Hakanan inka dubi sauran ibadu zaka ga cewa da yawa daga cikinsu baza’a iya yinsu ba har sai ankoma zuwa ga sunnar Annabi Sallallahu alaihi Wasallama. Kamar siffar Hajji.

Sannan in ya zamto zamu rinƙa amfani ne da hankulanmu da tunaninmu wurin inganta wa ko rashin inganta nassi toh haƙiƙa zamuyi ta samun kura kurai masu ɗinbin yawa. Domin hankulanmu sun bambanta. Ba ta hanya ɗaya muke tunani ba. Abinda wani yake gani dai dai ne, wani yana ganinsa kuskure ne. Toh kaga an rinƙa samun tsaɓani kenan wanda babu iyaka.

Yakamata a fahimci wasu abubuwa guda uku:

  • Musulunci ya girmama hankali, kuma ya bashi ƴanci. Amma kuma hankali yana da iyakarsa. Wannan duk wani mai hankali yasan haka. Shi yasa inka duba Al-Qur’ani zaka samu wurare da dama Allah yana faɗi cewa: Bazasu yi tunani ba?… yake kuma kira da ayi nazari kan halittun Allah. Ba komai hankali yake iya hararowa ba. Kamar yadda kuma hankula suna bambanta wurin kaifin nazari da hararo abubuwa. Wani zai iya hararo abubuwa da wani bazai iya ba. Farkon saɓo da akayi wa Allah sababinsa amfani da hankali ne. Lokacin da Allah ya umarci Iblis da yayi wa Annabi Adam Alaihissalam sujjada. Sai ya kafa hujja da hankalinsa. Yace ai ni na fishi alheri, Ka halicce ni da wuta shi kuma ka halicce shi da laka. Shiyasa duk yadda ka kai da basira akwai iya inda hankalinka zai iya hararo wa. Da zarar ka wuce wurin toh zaka fara shiga ɗimuwa. Shiyasa aka haramta wa musulmi tunani kan zatin Allah subhanahu wata’ala. Domin bazai taɓa iya gano haƙiƙaninsa ba.
  • Sunnah(Hadisi) shima wahayi ne daga Allah. kamar yadda Qur’ani yake wahayi. Kuma aikinsa bai tsaya a wani zamani ba. Ya shafi ko wani zamani har tashin Qiyaama.
  • Sahabbai da tabi’ai basu kasance suna kaddamar da hankulansu kan Nassi ba, duk da sun kasance mafiya mutane hankali da tunani. Aliyu bin Abi ɗalib Radiyallahu anhu yake faɗi game da Shafa akan huffi. “Da addini da ra’ayi akeyi da shafar ƙasar huffi yafi shafar samarsa. Amma na ga Manzon Allah yana shafan saman huffin sa”. Wannan yake nuna maka cewa Sahabbai suna barin Ra’ayinsu ne suyi amfani da Nassi.

Bayan wannan abu uku ya dace ka fahimci cewa hankalinmu Halitta ne na Allah. Shin wanda ya halicci hankalin shi ya dace yayi wa wannan hankalin bayanin yanda zata gudanar da rayuwarta ko kuma ita hankalin da aka halitta wacce bata san haƙiƙanin kanta ba itace ta dace ta gano wa kanta abinda ya dace?

Sannan samuwar mu’ujizozi wanda Annabawan Allah suka zo dashi da kuma samuwar wasu abubuwa acikin duniyarmu wanda haryanzu ba’a kai ga gane haƙiƙaninsu ba yana ƙara tabbatar wa hankali cewa yana da iyaka wanda bazai iya wuce nan ba. Kodai wannan iyakar mai gushewa ne, ta yadda zai zo ya gano nan gaba, ko kuma dai ta har abada ne.

Dubi ƙissar Jefa Annabi Ibrahim Alaihissalam a wuta. Ta yadda wuta bata masa komai ba. A hankalce kaga yanzu ace maka an jefa mutum a wuta kuma ya fita Sumul babu abinda ya sameshi hankali zaiyi shakkar sa sabida abinda ya saba gani shine idan wuta ta shafi mutum tana ƙona shi. Amma Sai gashi hakan ya faru. Kaga wannan abune wanda yafi ƙarfin hankali ya hararoshi amma gashi ya auku. Ashe kenan akwai abubuwa da dama wanda hankali baya iya riskarsa sai ta hanyar wahayi. Akwai misalai da yawa acikin Al-Qur’ani wanda hankali baya iya riskarsa har sai an bashi labari ko kuma ya ganshi.

Toh mu ɗauki wa’innan ƙissoshi na mu’ujizozin Annabawa da Allah ya bada labari a Al-Ƙur’ani. Sai mutambayi masu kore Hadisan Manzon Allah da hankalinsu. Shin sunyi imani da wa’innan Labarai da Al-Qur’ani ya bayar?

Idan sunyi imani dasu toh dole suyi imani da Ƙissoshi da hukunce hukuncen da Sunnah yazo dashi. Inkuma sun ƙi gaskata sunnah toh dole su ƙi gaskata Al-Qur’ani. Domin duka Daga wuri ɗaya suka fito. Kuma wa’inda suka yi dakon Al-Qur’ani zuwa garemu su sukayi dakon Sunnar.

Wataƙila wani yace ai Allah ne ya ɗauki nauyin ƙare Al-Qur’ani da kanshi. Shi kuma Sunnah Allah baiyi Alƙawarin kareshi ba.

Sai muce Haka ne Allah ya ɗauki Alƙawarin kare Al-Qur’ani da kansa.

shima sunnah Allah ya samar masa da wa’inda zasu kareshi. ta yadda a duniyar ilimi har abokan gaba sun tabbatar da cewa babu wani ilmi da ake bin diddigi wurin tabbatar da inganci kamar ilimin hadisi. Ta yadda kafin a tabbatar da magana a dangantashi ga Annabi sai anyi bincike sosai akai. Tun farkon fari. Sannan aka sanya ƙa’idoji na ƙarɓan Hadisi ko mai dashi. Wanda kuma Maluman Musulunci sun aminta dasu.

Sannan kamar yadda nayi bayani a baya cewa inhar mukace hankali shine abinda zamu dogara akai wurin tabbatar wa ko kore hadisi. Ko kuma muce hankali shine zai zamo ginahiƙin hukunci ba Nassi ba, toh haƙiƙa zamu sami babban matsala. Domin hankula suna da banbanci wurin fahimtar abubuwa.

Shiyasa fifita hankali kan Nassi babu abinda zai kawo sai lalacewar tsari da kuma rikici. Domin kowa da yanayin tunaninsa, da kuma yanayin hankalinsa.

Inda za’a samu Zaman lafiya da daidaito shine komawa zuwa ga Nassi, wanda ya samo asali ne daga mahaliccin kowa da komai wanda yasan haƙiƙanin kowa da komai. Yasan abinda zai dace da kowa da komai.

Allah yasa mudace.

Click Here to Support our work

Leave a Reply

%d bloggers like this: