Gwamnatin Afghanistan ta wajabta sanya Hijabi ga Mata masu gabatar da Labarai

Hukumar Afghanistan wanda Ƙungiyar Taliban ke jagoranta ta sanya dokar Rufe wani ɓangare na Fuska ga mata masu gabatar da labarai a ƙasar.

Abinda ya jawo hankalina wurin yin wannan rubutu shine yadda naga gidajen jaridun ƙasashen yamma da wasu masu iƙrarin kare haƙƙin Bil’adama suke ta suka kan wannan doka, har da wasu daga cikin Musulmai ta yadda suke ganin hakan tsattsauran Ra’ayine.

to abin tambaya anan ga masu hankali masu yin adalci shine:

Meye laifin Gwamnatin Afghanistan don tayi doka da ta dace da Addinin ƙasar ta da al’adun mutanen ta?

Shin Dole duk wani doka da za’ayi a wata ƙasa sai ta dace da ta ƙasashen yamma? Duk da tsaɓanin Addini da al’adu da yake tsaƙaninsu?

Kuma mafi yawancin gidajen jaridun duniya baki ɗaya da na ƙasashen Musulmi da na wanda ba Musulmi ba suna da dokar hana mace sanya Hijabi yayin gabatar da Labarai, kuma koda wasu gidajen labaran suna bada dama zaka ga basa basu dama su sanya Hijabi cikakke sai dai rabi wanda Banbancinsa da babu kaɗan ne. Shin wannan ba take Haƙƙin wa’inda suke son Sanya Hijabi bane?

Meyasa mutum Zai iya fita a faransa yayi yawo tsirara babu mai ce masa komai amma suka kafa dokar hana sanya niƙabi? Wannan ba take haƙƙin Bil’adama bane? Kun baiwa mai son yawo tsirara dama amma maison rufe jikinsa ku hanashi?

Sabida haka mai hankali zai gane cewa su ƙasashen yamma da masu goyon Banayansu masu iƙrarin kare haƙƙin Bil’adama ƙarya sukeyi, Su abu in ya dace da son ransu shine zasu goyi bayansa, idan kuma bai dace da son ransu ba toh sai su yaƙe shi, shine kawai.

amma misali kamar Ƙasa wacce take cin gashin kanta ta kafa doka wacce ta dace da mutanen ta ina ruwanku da shiga lamarin su?

wannan shine kamar batun auren jinsi, Sun halatta shi a ƙasashen su, sannan kuma suna bin duk sauran ƙasashe sai sun lazimta musu suma su halatta a ƙasashen su, ina ƴancin ɗan Adam anan? Inkunyi a ƙasashen ku babu laifi don ta dace da irin dabbanci irin ta mutanen ku, to amma ta yaya zaku farlanta shi akan ƙasashe wanda Basu yarda dashi ba? Kuma mutanen su basu yarda dashi ba? Akwai adalci anan?

duka irin wa’innan rubutun anayi ne don wayar da kan Musulmi, kada ya ruɗu da abinda yake gani ko yake ji daga ƙasashen yamma na cewa sune masu ƴanci masu kar ƴanci. Duk ƙarya ne, suna kare son zuciyar su ne, sannan kuma suna yaƙar Musulunci a ƙarƙashin ƙasa. Shiyasa zaka ga ana kashe Musulmi a India, Palastinu da sauran ƙasashe baza kaji suna kunfan baki ba, amma da zarar an taɓa musu mutane sai su fito suna surutai suna nuna an take haƙƙin ɗan Adam. Ya kamata mu farka mubar ruɗuwa da irin wa’innan Shiririta. Allah yasa mudace.

Click Here to Support our work

Leave a Reply

%d bloggers like this: