Dogaro Ga Allah

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Kada ka nemi abu awurin wadda bashi dashi, yana daga cikin abinda ya ruguza al’ummar musulmai yanzu tasirantuwa da kasashen yammacin duniya. A kullum wani abu ya taso a kasashensu zakaji suna jira suji me kasashen yamma zasuce, har yakaiga yanzu addini an kasashi kashi gida biyu. Akwai Musulmai Masu sassaucin ra’ayi akwai musulmai masu tsattsauran ra’ayi. Su masu tsattsauran ra’ayi sune masu bin addini sau da kafa. Abinda Allah yace suyi shi sukeyi abinda Allah ya hana basuyi, Kada ka dauka masu saka bom suna kashe mutane sune masu tsattsauran ra’ayi A’a sam, mu munsan wa’innan ‘yan ta’addane. Amma ainahin wanda ake nufi da masu tsattsauran ra’ayi sune masu bin addini sau da kafa masu son a kafa shari’ah. Wanda indaa baka fahimta ba, toh abinda ke faruwa a masar zai bayyana maka komai. Sai kuma kashi na biyu sune masu sassaucin ra’ayi. Wanda wa’innan samfurin jahilai kenan wanda sharrinsu tafi ta tsagoron arna, mujrimai munafukai. Wanda sune ainahin matsalar musulunci yanzu. Dominsu suna Ikrarin su musulmai ne amma kuma suna yaki da addini. Sune kasashen yamma suke amfani dasu wurin ruguza al’ummah. Mu dogara ga Allah mu dogara ga kanmu, sai Allah yajikanmu. Wa’innan abubuwa da suke faruwa Haka Allah yaso kuma annabi yayi bayaaninsa Alhamdulillah. Lokaci ne na hakuri da juriya. Shin kana nufin zakace Allah dayane kuma munafukai da Arna su barka? Sam Har abada fada tsakanin karya da gaskiya ba zata gushe ba. Allah ya kara mana imani ya kashemu muna musulmai.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates