Ku Farka Musulmai

·

·

Domin neman ƙarin bayani danna nan

Yana Daga cikin abinda yakawo wa al’ummar musulmai karaya, kokarin faranta wa Kafurai rai, kokarin neman yardansu, bayan Allah yayi mana bayani cewa Har abada bazasu yadda damu ba, bazasu amince damuba. Komin yadda mukayi. Ya zama dole duk mai imani ya yarda da wannan, duk yadda da kayi da kafuri ko babanka ne bazai taba yarda dakai ba, koda ko abaki ya nuna maka yana tare dakai. Allah yace:
ﻳﺮﺿﻮﻧﻜﻢ ﺑﺄﻓﻮﺍﻫﻬﻢ ﻭﺗﺄﺑﻰ ﻗﻠﻮﺑﻬﻢ
ﻭﺃﻛﺜﺮﻫﻢ ﻓﺎﺳﻘﻮﻥ.
sunã yardar
da ku da bãkunansu kuma
zukãtansu sunã ƙi? Kuma mafi
yawansu fãsiƙai ne.
Haka kuma bazasu kiyaye muku wata dangantaka ba, Allah yace.
ﻟﺎ ﻳﺮﻗﺒﻮﻥ ﻓﻲ ﻣﺆﻣﻦ ﺇﻟﺎ ﻭﻟﺎ ﺫﻣﺔ ﻭﺃﻭﻟﺌﻚ ﻫﻢ
ﺍﻟﻤﻌﺘﺪﻭﻥ.
Bã su tsaron wata zumunta a
cikin mũminai, kuma haka bãsu
tsaron wata amãna. Kuma
waɗannan ne mãsu ta´adi.
Duk da wannan gargadi na Allah, baya nuna kada kayi musu adalci, ko kada kuyi mu’amalla. A’a. Ya halatta kuyi, abinda akeso a nuna maka shine ka zama kana sane Akan basira kada ka tafi akife, wannan ayah ta tabbata a aikace munganta kuma muna kan cigaba da ganinta, kaman yadda a Nigeria Aka kashe mana Shuwagabanninmu irinsu tafawa balewa. Da murtala. Haka kuma rashin fahimtar wa’innan ayoyi ta sanya haka yanzu muka kasa mulkan kasar da mu mukafi yawa kuma Allah ya dauramu wakilai akan wannan kasa. Rashin fahimtar wannan ayan tasa har wadda ba musulmi ba ya iyayin mulkin kaduna na wasu watanni. Rashin fahimtar wannan ayan shiyasa A wasu jahohinmu na arewacin Nigeria wadda musulmai keda rinjaye ake samun Mataimakin gwamna wanda ba musulmai ba. Amma mu ayah ce agaremu a bayyane kaman mu haifaffun ‘yan jahar pilato yadda akayi watsi damu acikin tsarin gwamnati har yakaiga anace mana mu ba ‘yan kasa bane. Wadda inza’abi hakikanin gaskiya Yawanmu takai mu mulki jahar baki daya. A wannan lokaci ta fitina da tashin hankali, maganin wannan bala’I shine mu koma zuwa ga Qur’ani. Mu koma zuwa ga tsarinmu ta musulunci, dama kuma annabi yayi bayanin zata dawo. Riko da Qur’ani itace mAfita a irin wannan yanayi ta tashin hankali. Allah yasa mudace.

3 responses to “Ku Farka Musulmai”
  1. UMAR ADAMU FASKARI Avatar
    UMAR ADAMU FASKARI

    Allah yasaka da alkhairi

  2. Idrismuhammad Avatar
    Idrismuhammad

    Alhamdulillahi Rabbil aalamiyn.
    Lallai abinda ALLAH S.W.T Yafada gaskiyane,amma musamman masu irin aqeedarku kuna da raunin imani! A’matsayinmu namusulmi ya kamata murinqayin imani da abinda Allah yahukunta, Wallahi duk wanda kagani akan kujerar mulki to Allahne yabashi ba waniba. Amma koda yaushe aikinku kenan magana kansiyasa,gulmace gulmace,cin zarafin malaman farko,tada fitinar addini,dahada gaba tsakanin musulmi. Allah yashiryeku da yan’malamanku idan kuma ba masu shiryuwa bane Allah yashafe manaku abayan Qasa mudainajin ambatonku.
    Fatiha daswalatil fatihi.

  3. ZAKARIYA YUSUF LIMAN Avatar
    ZAKARIYA YUSUF LIMAN

    ALLAH YA SAKA DA ALKHAIRI

Leave a Reply

Latest updates
Categories