Mu yawaita Istigfari

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Istigfari yana daga cikin ayyuka masu falala a addinin Musulunci wanda kuma bashi da wahalar aikatawa. A kowani irin yanayi mutum zai iya yin Istigfari inba a bayan gida yake ba.

Istigfari yana jawo kankare zunubai, da kuma yalwatatar Arziƙi da yaye damuwa. Sannan yana hana sauƙar azabar Allah akan bayi kamar yadda Allah yace:

Allah bai kasance zaiyi musu azaba ba alhali kana cikinsu, haka nan Allah bai kasance zaiyi musu azaba ba alhali suna Istigfari

Suratul-Anfal: 32

haka yake nuna cewa yawan Istigfari yana tunkuɗe musiba da azaba akan bayi. Inkana neman ka samu katanga tsakanin ka da kowani irin sharri to ka lazimci Istigfari.

Allah yana hakaito Annabi Hud yana umartan Mutanensa da yin Istigfari. Allah yace:

Ya ku mutane na ku nemi gafarar Ubangijin ku, sannan ku tuba zuwa gareshi zai sauƙar muku da ruwan sama mai yawa, sannan zai ƙara muku ƙarfi akan ƙarfinku.

Suratu Hud: 52

An rawaito daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yana cewa:

ina rantsuwa da Allah ina Istigfari ina kuma tuba zuwa ga Allah a rana fiye da sau saba’in. a wata riwaya ina Istigfari da tuba zuwa ga Allah sau ɗari.

Bukhari: 6307

Kamar yadda Malamai sukayi bayani kan wannan hadisi cewa wannan adadi da Annabi ya faɗi ba wai yana nuna a iya wannan adadin yake tsayawa ba, A’a yana yi fiye da haka, yayi amfani da wannan adadin ne domin nuna yawan aikin.

Sabida haka ya dace Musulmi ya lazimci Istigfari a kowani lokacin sa. Yana kwance ne ko yana tafiya, ko yana zaune. Domin da haka zai samu rabauta duniya da lahira.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories