WAYE YAKE DA MATSALAR DA TA ADDABESHI? GA MAFITA!

Danna nan domin shiga karatu Online

WAYE YAKE DA MATSALAR DA TA ADDABESHI? GA MAFITA!
Wani Mutum Yazo wurin hasan albasri yace masa: Ba’a ruwan sama ma’ana fari ya damesu, sai hassan yace masa kuyawaita istigfari,
Sai wani ya sake zuwa yace masa talauci ta dameni, sai hassan yace masa Kayawaita istigfari,
Sai wani ya sake zuwa yace masa matata bata haihuwa, sai hassan yace masa Ka yawaita istigfari,
Sai mazauna awurin sukace ma hassan albasri, kai kenan duk wani wanda ya kawo maka koke sai kace masa yayita istigfari? Sai hassan Albasri yace Shin baku karanta fadin Allah bane da yake cewa:
ﻓﻘﻠﺖ ﺍﺳﺘﻐﻔﺮﻭﺍ ﺭﺑﻜﻢ ﺇﻧﻪ ﻛﺎﻥ ﻏﻔﺎﺭﺍ.
“Sai na ce, ´Ku nħmi gãfara
daga Ubangijinku, lalle ne shi
Ya kasance Mai gãfara ne.
ﻳﺮﺳﻞ ﺍﻟﺴﻤﺎﺀ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﻣﺪﺭﺍﺭﺍ.
“Ya sako (girgijen) sama a
kanku da ruwa mai ɓuɓɓuga.
ﻭﻳﻤﺪﺩﻛﻢ ﺑﺄﻣﻮﺍﻝ ﻭﺑﻨﻴﻦ ﻭﻳﺠﻌﻞ ﻟﻜﻢ ﺟﻨﺎﺕ
ﻭﻳﺠﻌﻞ ﻟﻜﻢ ﺃﻧﻬﺎﺭﺍ.
Kuma ya yalwata muku game
da dũkiya da ɗiya,Ya sanya
muku (albarka) ga gõnaki, kuma
Ya sanya muku koguna.
Nasan da yawa daga cikinmu akwai masu dinbin matsaloli wanda basu iya kirguwa, wani talauci, wani cuta, wani rashin kwanciyar hankali, wani neman haihuwa, wani neman aure, wata neman miji…… Da sauransu.. Toh Ga hanya mai sauki da zakubi wurin fita daga matsalolinku. Ku rike istigfari.. Kalmomin basu da wuya… ‘ASTAGFIRULLAH’. Allah yaye mana matsalolinmu baki daya.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

5 responses to “WAYE YAKE DA MATSALAR DA TA ADDABESHI? GA MAFITA!”
 1. Nura senior Avatar
  Nura senior

  Slm dan uwa nagari Allah ya barmu da Annabi ya sakamaka dama akwai wasu bayin Allah acikin al umma wadanda Allah ya zaba kullum sai sunyi istigfari 230 Allah ya bamu albarkacin su ameen

 2. Yasir sulaiman yusuf Avatar
  Yasir sulaiman yusuf

  Salm malam nibras dafatan kasheruwa lafiya yayakaratunka Allah yatai makemugabakidaya mukam munshiga yajin aiki sai daikutayamu da adduah kawai@

  1. masha,allahu shi illimi haskene toh yan uwa musulmai mu dage ko allah zai tai make mu a rayuwa.

 3. muda ge allah kuma ya tai make mu ameen

 4. Abdulrahman muhammad Avatar
  Abdulrahman muhammad

  Alhamdulillah

Leave a Reply

Categories
Latest updates