WATA MAGANA TAKAITACCIYA MAI MAHIMMANCI GAME DA MUMMUNAN BALA'IN KALLON KWALLON KAFA

·

·

WATA MAGANA TAKAITACCIYA MAI MAHIMMANCI GAME DA MUMMUNAN BALA’IN KALLON KWALLON KAFA…
Bismillahirrahmanirraheem…..
Da yawa daga cikin ‘yan’uwa musulmai sun fada wata mummunan tarko, wanda a ganinsu karamar abuce, amma wallahi ba karama bace babbace kuma mai hadari sosai. A kullum inace muku Allah shi ya haliccemu sannan shi ya sanmu sanin da babu wadda ya mana irinta, sanin kwakwaf da yayi mana shiyasa ya gindaya mana sharrudan da zamu rayu akai, da zaran muka kauce mata toh wallahi mun halaka.
‘Yan’uwa Musulmai wai meyasa ne wasu daga cikinmu suke tsabawa umarnin Allah ne? Kuma sudinga ganin hakan ba a matsayin laifi ba? Allah(swt) yace
ﻳﺎ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺁﻣﻨﻮﺍ ﻟﺎ ﺗﺘﺨﺬﻭﺍ ﺍﻟﻴﻬﻮﺩ ﻭﺍﻟﻨﺼﺎﺭﻯ
ﺃﻭﻟﻴﺎﺀ ﺑﻌﻀﻬﻢ ﺃﻭﻟﻴﺎﺀ ﺑﻌﺾ ﻭﻣﻦ ﻳﺘﻮﻟﻬﻢ
ﻣﻨﻜﻢ ﻓﺈﻧﻪ ﻣﻨﻬﻢ ﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﺎ ﻳﻬﺪﻱ ﺍﻟﻘﻮﻡ
ﺍﻟﻈﺎﻟﻤﻴﻦ
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni!
Kada ku riƙi Yahudu da Nasãra
majiɓinta. Sãshensu majiɓinci
ne ga sãshe. Kuma wanda ya
jiɓince su daga gare ku, to, lalle
ne shĩ, yanã daga gare su. Lalle
Allah bã Ya shiryar da mutãne
azzãlumai.
Toh indai har hakane meyasa wasu daga cikin musulmai suke tasirantuwa da kallace kallacen kwallon kafa na team na arna? Wato wannan ba karamar bala’I bace, zakaga manya,yara, har da mata, kowa zakaji yana bayyana cewa shi dan team kazane. Gaskiya wannan a hakika yaci karo da karantarwar addini, domin Duk wani mai kallon kwallon kafa zaka samu akwai wadda yakeso acikin masu buga kwallon kafan, kuma zaka samu galibinsu kafirai ne, toh a addinin musulunci son kafiri haramun ne, kaman yadda ayar da na kawo a sama nan ta nuna. Sannan su wa’innan wa’inda kakeso kafurai, su makiyanka ne, makiya addininka, makiya annabinka, makiya ‘yan’uwanka musulmai. toh anan ta yaya zakayi kanason annabi kuma kanason makiyinsa?
Sannan a yanzu har kana da lokacin da zaka tsaya kana batawa wurin kallace kallacen kwallon kafa? Shin an halicceka don wasa ne?
Kuma yana daga cikin wannan masifa ta kwallon kafa, haddasa gaaba tsakanin al’ummah, domin a kullum zaka samesu ciki musu, wadda hakan karshe take kawo musu gaba.
Toh ya zama wajibi ga duk maison tsira, mai son annabi da gaske ya kauracewa kallace kallacen kwallon kafa wanda basu da amfani a gareshi sai dai ma su janyo masa fushin ubangiji….
Sannan duk mai kallon kafa yana taimakawa kafirci da kafirai, domin kudin da yake bayarwa wurin shiga dakin kallo, ko biyan kudin wata da yakeyi a satelite nashi itama taimakawa yakeyi wurin su wa’innan makiya addinin musulunci su samu kudin shiga, wadda akarshe za’aje ayi amfani da wannan kudi wajen kashe ‘yan’uwanmu a wurare da dama kaman yadda muke gani ke faruwa yanzu.
Sannan kada ku manta idanun da kuke amfani dashi wajen kallon kafan, da bakin da kuke ihu dashi in ansha kwallo, da kafafuwan da kuke takawa kuje wurin kallon duka akwai hakkin Allah aciki, kuma sai ya tambayeku yaya kuka sarrafasu. Wannan abin dubawa ne ga mai hankali maison ya tashi cikin tawagar manzon Allah(saw) da ya tuba ya kauracewa kallon kwallon kafa na arna..
Abin akwai wuya sosai, amma sai kayi tunani da manzon Allah(saw) da wa’innan team din da masu buga kwallon wanne kafi so? Umarnin Allah da manzonsa zakabi ko umarnin shaidan??? Zabi ya rage naka. Allah yasa mudace.

One response to “WATA MAGANA TAKAITACCIYA MAI MAHIMMANCI GAME DA MUMMUNAN BALA'IN KALLON KWALLON KAFA”
  1. Abubakar Muhammad Gamawa Avatar
    Abubakar Muhammad Gamawa

    Amiin

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: