FADAKARWA A TAKAICE

·

·

A kullum sai kaji ‘yan’uwa musulmai muna cewa Allah kawo mana zaman lafiya….. Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un. Ta yaya Allah zai sauraremu bayan munki bin dokokinsa? Shari’ar da annabi(saw) ya barmu akai mun kauce mata, Allah(swt) yace: ‘MASU TSABAWA WA UMARNIN MANZON ALLAH SUJI TSORON KADA WATA MUSIBA TA SAMESU KO AZABA MAI RADADI’
Allah yayi gaskiya gashi muna kan ganin musiba kala kala. Bala’I iri iri. Ana kashemu kaman kiyashi amma babu wadda zai tashi ya tsaya a madadinmu. Ana kama mana malami ana tsaresu amma mun kasa daukar mataki, ana kisan muminai ba laifi amma mun kasa cewa komai…. Wannan wata irin rayuwa ce? Shin ‘yan’uwa kuyi tunani. wata gudumawa kuka baiwa addinin musulunci a rayuwarku? Ku tuna fa ba’a haliccemu domin muzo muyi wasa a duniya ba. An haliccemu ne domin muzo muyi bauta wa Allah… Allah yace :’BAN HALICCE MUTUM DA ALJAN BA FACE DON SU BAUTAMIN…’. Toh mu dubi rayuwarmu a yau shin bautan Allah mukeyi da gaske ko shirme? Mun kasa tsinana komai wa kanmu sai zage zagen juna, tsine wa juna da hassadar juna.. Wallahi ta kowata hanya mun tsabawa Allah da manzonsa. Abin mamaki ka dubi yadda aka maida addinin Allah wasa. An kirkiro bid’oi da sunan addini. Ga wasu dajjalu sun shigo suna kafirta waliyyan Allah sahabban annabi. Kullum tsakaninmu babu zaman lafiya. Haba ‘yan’uwa shin kuna tunanin annabi zaiyi alfahari damu a irin wannan hali namu? Wallahi ‘yan’uwa mu tuba mu koma wa Allah. Ku dubi yadda muka mai da riba ta zamto halal. Wanda Allah(swt) yace : ‘INHAR BAKU BAR CIN RIBA BA TOH KU SHIRYA YAKI DA ALLAH’
Shin meyasa bazamu hada kai mu kafa bankin musulunci ba? Bamu da masu kudi ne da zasu taimaka? Ko bamu da masu ilmi ne da zasu gudanar da harkokin bankin? Duka muna dasu. Kuje ku dubi jami’oi kuga yadda ake lalata acikinsu. Hazbunallah
Yaa ku mazinata wallahi ku tuba.
Yaa ku ‘yan luwadi wallahi ku tuba.
Yaa ku maciya riba wallahi ku tuba.
Yaa ku maciya amana wallahi ku tuba.
Yaa ku ‘yan ta’adda wallahi ku tuba.
Yaa ku masu bid’ah wallahi ku tuba.
Yaa ku ‘yan tsubbu wallahi ku tuba.
Yaa ku masu aiki da shari’ar da bata Allah ba, wallahi ku tuba.
Yaa ku azzaluman shuwagabanni wallahi ku tuba.
Yaa ku masu zagin waliyyai wallahi ku tuba.
Yaa ku mashaya giya da sauran kayan maye wallahi ku tuba.
Yaa ku munafukai wallahi ku tuba.
Yaa ku maciya rashawa wallahi ku tuba…
Wallahi babu wata lokaci da ta rage mana. Tashin Alqiyaama ta kusa, indama kun mike kafa ne, ku nade ta ku tashi kuyi wa addinin Allah aiki. Domin mu tsira tare….. Allah ya taimaki musulunci. Allah ya nuna mana gaskiya ya bamu daman binta. Ya nuna mana karya ya bamu daman kauce mata….

6 responses to “FADAKARWA A TAKAICE”
 1. usman isa el-yazaki, kwandare Avatar
  usman isa el-yazaki, kwandare

  mallam suwaye walliyen Allah da aka zaga? Kuma suwaye suke zagin walliye? Walliyen Allah na kwarai duk wanda ya zage su, to ya shirya fushin Allah a tattare da shi. Amman wayanna walliyen nada nadan karyan su sai an yi magana a kan su insha Allah

  1. Sani Sufi Avatar
   Sani Sufi

   waliyan akwai na da ?lallai kacika jahili.

  2. Sani Sufi Avatar
   Sani Sufi

   yan izala sune suke zagin waliyai

 2. Anas m Adams Avatar

  Muna godiya agareku masoya

 3. Sani Sufi Avatar
  Sani Sufi

  waliyan Allah sune wadanda kuke aibantawa kuke zagi.to ku kiyaye in kuma kunki zamu yake ku.domin duk wani mai zagin waliyan Allah, ba ruwan Annabi dashi.Allah S.W.T yace;duk wanda yayi fito na fito da waliyi hakika yayi fito na fito da Allah ne,

 4. Sani Sufi Avatar
  Sani Sufi

  kuma duk wanda yayi fito na fito da Allah hakika ya shiga fushin Allah, kuma duk wanda ya shiga fushin Allah to dan wuta ne.kuma duk wanda ya zagi waliyi ko ya tuba sai yayi fursuna(prison) a gidan wuta.

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: