Shari'ah Itace Mafita Ga Bil'adama

·

·

Babu wani abu da zai gyara duniyannan ya kawo mata zaman lafiya sai shari’ar musulunci!!! Domin meye? Sabida wanda ya zana wannan doka shi ya haliccemu, ya halicce duniyan kuma yafimu sanin yanayin da ya dace ta zauna lafiya shiyasa ya shimfida dokoki. Hakanan babu abinda ya jefa duniya cikin tashin hankali sai amfani da dokokin da mutane suka kafa da yin watsi da ta Allah!!!
Ya dace musulmai da wanda ba musulmai ba su san Haka, domin ni nayi imanin cewa in wa’inda ba musulmai ba suka rayu karkashin shari’ar Musulunci zasufi samun Kwanciyar Hankali da ‘yanci fiye da rayuwa karkashin dokokin da dan adam ya kafa. Domin addinin musulunci ya tanadar musu rayuwa cikin salama akarkashin shari’ar musulunci.
Sannan Babban matsalar Musulmai Kansu sun kasa fahimtar mahimmancin amfani da shari’ah ballantana wa’inda ba musulmai ba su fahimta
ﺃﻓﺤﻜﻢ ﺍﻟﺠﺎﻫﻠﻴﺔ ﻳﺒﻐﻮﻥ ﻭﻣﻦ ﺃﺣﺴﻦ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻪ
ﺣﻜﻤﺎ ﻟﻘﻮﻡ ﻳﻮﻗﻨﻮﻥ.
Shin, hukuncin Jãhiliyya(2)
suke nema? Kuma wane ne
mafi kyau ga hukunci daga
Allah sabõda mutãne waɗanda
suke yin yaƙĩni (tabbataccen
ĩmãni)?
. Allah muke roko ya dawo damu kan addininmu Dawowa mai kyau. Ya gyara mana zuciyarmu mubar tsoron kowa sai shi. Allah ya tabbatar mana da shari’ar musulunci ako’ina a fadin duniya baki daya.

One response to “Shari'ah Itace Mafita Ga Bil'adama”
  1. Mohammed Auwal Garba Avatar
    Mohammed Auwal Garba

    WANNAN HAKANE AMMA MATSALAR ITACE YAYA AZA’AYI A HADA KAI DON MALAMAI SUN RARRABA AL UMMAR MUSULMAI

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: