ILLAR KAYAN MAYE GA MATASA(Malam Aminu Ibrahim Daurawa)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Hakika Allah taala ya girmama dan Adam ya martashi, ya bashi hankali da basira, da hikma, da azanci, da sanin ya kamata,
Hankali babbar niima ne, da wadata da ya kamata a kiyaye shi, a aiwatar dashi, inda ya dace,
shan kayan maye, da kayan marisa, da buguwa, wanda yake yaduwa tsakanin matasa maza da mata, wanda hakan yake barazana, ga tabarbarewar tarbiyya, da rugujewar al’umma ta gari, abune na takaici da Allah wadai,
Acikin shan kwaya akwai matsaloli da suka shafi yawan rigima, tashin hankali, daru, rigima, tarzoma, fitintunu, kashe-kashe, akwai barazana da kayan maye sukeyi ta bangarori kamar haka :
1-Addini wanda ya haramta haka kuma yaja kunne
2-Hankali, wanda yake gushewa, sakamakon shan kayan maye
3- Yan uwa da Dangi, wanda mashayi, yake cutarwa
4- Tattalin Arziki, wanda yake fuskantar matsala sakamakon shan kayan maye
5- lafiyar jiki,
6- al’ummar da kayan maye ya mamaye matasan ta, suna cikin matsala babba
7- tsaro, da zaman lafiya da kwanciyar hankali
A ganinku manene ya jawo yaduwar kwayoyi da kayan marisa, suka mamaye rayuwar matasa kuma ina mafita ?

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

3 responses to “ILLAR KAYAN MAYE GA MATASA(Malam Aminu Ibrahim Daurawa)”
 1. Yahaya Abubakar Abdullahi Avatar
  Yahaya Abubakar Abdullahi

  Malam, Allah ya saka da alheri ,ameen

 2. NASIRU ALI Avatar
  NASIRU ALI

  MATAKI NA FARKO shine abinda MAIgirma gwamnan KANO DR RABI’U MUSA KWANKWASO yayi 1(na hana sayar da kayan mayen da tilastawa masu wannan shaye shaye su kama sana oi su daina zaman banza

 3. kabiru Avatar
  kabiru

  Allah yasaka da alkhairi

Leave a Reply

Categories
Latest updates