Fina-Finan Hausa Tsakanin Karya Da Gaskiya (2)(Sheikh Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo)

Harkar fim Sana’a ce!!
Wasu sukan ce ai harkar
fim ta samarwa matasa sana’a!. wannan magana
ce bai ban mamaki,
domin a matsayinmu na
musulmi ba wannan ne
mizani ko ma’auni ba, na
abu daidai ne ko ba daidai ba ne, inda kuwa
haka ne da sai a kyale
kamfanin giya su ci gaba
da sayarwa, saboda
dimbin mutanen da suke
cin abinci a karkashin wannan kamfani, ko a
kyale manoma wiwi da
sauran kayan maye su ci
gaba, saboda dimbin
masu cin abinci a
karkashinsu. Wani zai iya cewa ai duk
wadannan haramun ne,
Allah ya haramta su
babu wata shakka, to sai
in ce maka, haduwar
maza da mata ba haramun ba ne, baya
faruwa a fim, ba ya
faruwa a wajen daukar
fim, kwana nawa ake yi
da mata da maza a wasu
garuruwan don daukar fim, ashe duk abin da
yake faruwa a can,
daidai ne. Wani zai ce ai
wurin kwanan maza
daban, wurin kwanan
mata daban. Sai in ce wannan ai shi ne ba
cinya ba kafar baya, a
ina ne shari’a ta halatta
mace ta yi tafiyar
kwananki ba tare da
muharaminta ba. Manzon tsira (S.A.W)
cewa ya yi, “Ka da mace
ta yi tafiyar wuni biyu,
(a wata riwaya : wuni
uku) ba tare da
muharraminta ba”. (Bukhari da Muslim ne
suka rawaito) Sannan ga
tsiraici da ake nunawa a
cikin fina – finan shi ma
ba haramun ba ne, a ina
aka ce ya hallatta matar da ba taka ba, ta yi rawa
gabanka, a ina aka ce
matar da ba ta ka ba, ku
zauna kugu da kugu, ina
a ka ce matar da ba taka
ba ka kwanta da ita a gado daya, ko ta fito
maka da rigar barci, duk
babu wannan a fina –
finan mu na hausa!?
Kuma a she Allah bai
haramta su ba. don haka maganar cewa ai hanyar
cin abinci ce, sana’a ce,
ba ta taso ba. domin
Allah bai sanya aikata
haramun ya zama
hanyar cin abinci ba. Manzon Allah (S.A.W)
yana cewa : “Hakika
Mala’ika mai tsarki ya yi
min busa a cikin rai
cewa, babu wata rai da
za ta mutu, face sai ta cika arzikinta, ku ji
tsoron Allah, ku kyautata
wajen neman (arziki).
(Baihaki ne ya rawaito a
cikin littafinsa “Shu’abul
Iman”) Sannan in har neman
abincin za su yi da fina –
finan hausa, me zai hana
su kawar da wadancan
abubuwan na haramun,
su tsaftace shi, ashe a baya can ba a yin wasan
kwaikwayo ba?, Nasan
kowa ya san wasansu
dan haki da irin salon
yadda yake, mata ne
manya, masu sanin ya kamata, da gogewa a
rayuwa, tare da
magidanta masu
dattijantaka, da sanin
rayuwa da addini daidai
gwargwado suke yin sa, babu rawa, babu waka,
babu wuce gona da iri,
ga nishadantarwa, ga
fadakarwa, duk a cikin
lokaci kankane. Alal a
kalla an rage abubuwan haramun masu yawa a
tare da wannan wasan,
sabanin na yanzu da
kaso casa’in da tara duk
aikin haramun ne.
Duk Duniya ana yin Fim Wasu na cewa, to ai duk
duniya ana yin fim,
kuma abin da ake yi a
cikinsa ya fi abin da ake
yi a cikin fina finan
hausa, amma ba wanda ya yi magana a kansu sai
a kan fina finan hausa.
To masu wannan
magana dai su manta da
cewa duk abin da yake
ba daidai ba, to don wani yana yin sa ba zai
zama daidai ba, kuma
duk abin da Allah ya
haramta, to haramun ne
a yi shi a ko’ina, babu
ruwan Allah da cewa ai duk duniya a na yi, Allah
Madaukakin sarki yana
cewa akan harshen
Annabi Musa “Musa ya
ce, inda ku da dukkan
wadanda suke bayan kasa gaba daya zaku
kafirce to fa Allah
Mawadaci ne kuma abin
godiya” (Ibrahim : 8).
Sannan cewa ba a
magana a kansu wannan ma ba haka ba ne, kusan
yadda ake ta cece ku ce
tsakanin masu goyon
bayan fina finai da
wadanda ba sa goyon
bayansu a nan Nigeria, haka ake yi Misra da
Saudiya da sauran
kasashen musulmi, wani
sa’in ma abin ya wuce
yadda muke gani, domin
na san akwai lokacin da malaman wata kasa ta
larabawa suka kafirta
wasu ‘yan wasan
kwaikwayo na kasar,
saboda abin da suke yi a
cikin wasansu. A takaice dai wadannan abubuwa
marasa kyau da ake yi a
fina finan hausa, kamar
rawa maza da mata,
kwanciya gado daya
namiji da mace, maganganun batsa,
tafiya da mata wani gari
ko wata kasa, a yi
kwanaki don daukar fim,
da sauransu, suna nan a
haramun ne, ko da duk duniyar nan za a hadu a
ce babu komai ‘yan fim
na iya aikata su, hakan
ba zai canza hukuncinsu
a wurin Allah ba.
Sannan wani abu guda da yake ban mamaki, me
yasa ‘yan wasanmu na
nan suke kokarin
kwaikwayon na wasu
kasashe a cikin irin
wadannan abubuwa, me yasa su ba za su yi abin
da za a kwaikwaye su
ba, sai dai su kwaikwayi
na wasu!?.
Kira Da Jan Hankali
A karshe duk mai adalci wanda ya tsaya ya lura
da fina finanmu na
hausa ya san abin da ake
fada daban, abin da
kuma yake a aikace
daban, fatana su wadanda suke yin
wannan harkar su tsaya
tsayin daka su ga sun
tsarkaketa daga duk
wani abin da yake
haramun ne a musulunci, su tuna su
musulmi ne, kuma Allah
zai tambaye su a kan
duk abin da suka aikata,
kamar yadda zai
tambayi kowa da kowa, kuma abin ka shuka a
nan duniya shi zaka
girba a lahira. Idan kuwa
ba za su iya canza
abubuwan da suke
gudana a cikin fina finan ba, to wallahi gwara
mutum ya nemi wani
abun daban, wanda zai
tseratar da shi a wurin
Allah, duniya dai ba
matabbata ba ce, mun ji, mun gani, ‘yan wasa da
yawa a yau babu su,
amma fa abin da suka yi
na wasan yana nan yana
kewayawa cikin
mutane, in mai kyau ne, sun riga sun iske shi a
can lahira, in kuma
akasin sa ne, to babu
damar gyarawa. Allah ya
sa mu dace. Sannan ina
fata wannan makala tawa ta zama wata
zaburarwa ga duk
wanda zai yi rubutu ko
magana a kan fina finan
hausa da ya duba abin
da zai fada da abin da ake yi a cikin fina finan,
ya zama abin da zai fada
daidai da abin da ake
aikatawa. Allah ya nuna
mana gaskiya, ya bamu
ikon bin ta, ya nuna mana karya ya bamu
ikon guje mata.
Wassalam.

8 responses to “Fina-Finan Hausa Tsakanin Karya Da Gaskiya (2)(Sheikh Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo)”
 1. Dahiru deba Avatar

  Allah yajikan malam ja,afar mohmud adam

 2. Ibrahim hudu Avatar

  I am very happy to on this site.

 3. Malamismz Avatar

  Allah ya bsu ikon gyarawa…amin

 4. Wannan gaskiya kafada Allah ya bamu ikon aikata dede ya kuma hanemu dayin wanda ba dedenba.

 5. allah yasa suji su gyara

 6. Ibrahimaliyusumaila@gmail.com Avatar

  Allah ya shiryemu ya nuna mana gaskiya gaskiya ce ya bamu ikon bin ta ya nuna mana karya karya yace ya bamu ikon kauce mata

 7. muhammad rabiu Avatar
  muhammad rabiu

  Ameen summa Ameen Allah ya bada lada

 8. Hassan Adamu Avatar
  Hassan Adamu

  Allah Saka Da Akhairi

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: