Aljannah na samuwa ne ga wa’inda basu nufin ɗaukaka ko ɓarna

·

·

Domin neman ƙarin bayani danna nan

Allah maɗaukakin sarki yace:

تلك الدار الآخرة نجعلها للذين لا يريدون علوا في الأرض ولا فسادا والعاقبة للمتقين

Wancan gidan lahira muna bada ita ne ga wa’inda basu neman ɗaukaka acikin rayuwar duniya ko kuma ɓarna. Kuma ƙarshe mai kyau na ga masu taƙawa.

Wannan ayah tana nuna mahimmancin Tawali’u da kuma Mummunan halin girman kai da neman mulki da ɗaukaka kan mutane.

Shekhul islam ibn taimiyya yace:

Mutane kashi huɗu ne:

  • Kashi na farko: wa’inda suna nufin ɗaukaka kan mutane da kuma ɓarna. Sune shuwabanni maɓarnata kaman su Fir’auna da wanda suka bi hanyarsa. Wa’innan sune mafiya sharrin mutane.
  • Kashi na biyu: wa’inda suna nufin ɓarna amma basu nufin ɗaukaka kan mutane, sune Ɓarayi, da masu aikata ɓarna cikin mutane.
  • Kashi na uku: Wa’inda suke neman ɗaukaka amma basu nufin ɓarna, sune masu ilimin addini wanda suke amfani dashi domin neman ɗaukaka wurin mutane.
  • Kashi na huɗu: Sune ƴan Al-Jannah, sune wa’inda Allah ya yabesu cikin wannan ayah. Wa’inda basu neman ɗaukaka ko kuma ɓarna. Duk da zaka samu sunfi wa’inda basu ba ɗaukaka ɗin.

Wa’innan kashi na huɗu shi ya dace musulmi yayi ƙoƙari ya kasance daga cikinsu. A kullum mutum ya zamto mai ƙanƙan da kai, kada mutum ya zamto mai girman kai, ko kuma mai son girma, domin hakan zai kai mutum ne zuwa ga halaka.

Leave a Reply

Latest updates
Categories