Hakika dan Adam na cikin hasara

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Allah maɗaukakin sarki yana cewa acikin Suratul Asr.

Ina rantsuwa da zamani

ɗan Adam na cikin hasara

Sai dai wa’inda sukayi Imani, Sukayi aiki na ƙwarai, sannan sukayi wasiyya tsaƙaninsu da bin gaskiya, da kuma Haƙuri.

Wa’innan nau’ukan mutane huɗu su kaɗaine basu cikin hasara a duniya.

Ya zamto mutum yayi imani da Allah, imani na gaskiya, Sannan kuma ya haɗa wannan Imani da aiki na ƙwarai domin shi Imani ba wai kawai zancen baki bane dole sai mutum ya haɗa da aiki na gari shi yasa sau da dama a Al’Qur’ani Allah yake haɗa tsaƙanin Imani da aiki. Domin basu rabuwa.

Sai kuma Mutum yayi wasiyya da Gaskiya: Ma’ana mutum yayi da’awah kenan, ko kuma yayi Nasiha wa ƴan’uwansa Musulmai wurin bin gaskiya da tsayuwa akan tafarki madaidaici. Wannan ayah tana nuna falalar da’awah da kuma yi wa juna nasiha da wasiyya.

Sai kuma wasiyya da Haƙuri, wannan ma yana da Mahimmanci matuƙa. Mu rinƙa yi wa junanmu wasiyya da haƙuri acikin duk lamuranmu.

Toh sai ka binciki kanka kana daga cikin ɗaya daga cikin wa’innan mutane da aka ambata? Ko kuma kana aikata ɗaya daga ciki? Indai har baka aikata ko ɗaya daga ciki toh ka sani kana cikin hasara. Inkuma ka samu ka haɗa duka toh Haƙiƙa ka rabauta. Allah yasa mudace.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories