FADAKARWA GA MASU SHIGA FACE BOOK(Mal.Aminu Ibrahim Daurawa)

Face book wata hanya ce ta gani,
da saurare, da karantawa, da
rubutawa, da yadawa.
ka tabbatar, da jinka da ganin ka,
da rubutunka, da karantawarka, da
abinda ka yada, Allah zai
tambayeka ranar Alkiyama,
Wasu suna ganin tunda su kadai,
suke kamar babu, mai ganin su sai
suyi abinda suka ga dama, alhalin
Alllah yana ganin su.
ga shawarwari domin amfanuwa:
Na daya, mu kiyaye idanuwanmu
daga kallon batsa,
Na biyu Umarni da kyawawan
aiyuka da hani da munana
Na uku duk abin zamu rubuta mu
tabbatar da muna da cikkakiyar
hujja ta ilmi
Na uku mu daina yawan bayar da
labarin abinda ya shafemu, na yau
da kullum, kamar yanzu na tashi,
yanzu ina cin abinci yanzu kaza da
kaza, duk wannan bai dace ba
Na hudu, kulla abota da mutumin
da bakasan ko waye ba,
Na biyar: yada jita jita, da kanzan
kurege, da kage da sharri, da wani
ko wasu,
Na shida: kiyaye isgili da baa ga
wata kabila ko wani yare, domin
bakasan yadda wannan mutunen
sukeji ba.
Na bakwai : kula da lokaci, domin
wasu suna wace gona da iri amfani
da face book
Na tara : masu kawo wani labari
mara kan gado, kuma su zagi, ko
tsinewa wanda yaki taya su, abin,
kamar duk wanda baice kaza ba
Allh ya yi masa kaza
Na goma: Yada kalaman batsa, da
hotunan batsa, da maza masu
shigowa da hotunan mata, da
kuma mata masu shigowa da
hotunan mata, da masu daukan
haton mace batare da sanin ta ba
su yada a face book
Duk wadannan abubuwa suna
faruwa da fatan zamu kiyaye,

Click Here to Support our work

21 Comments

  1. Slm,
    Malam, Allah ya saka maka da alkairi, Allah ya sa Aljanna makoma!
    Acigaba da fa,dakar da mu kada a gaji,
    mu kuma Allah ya bamu ikon ji da kiyayewa.

  2. Mallan Allah yasaka maka da mafi girman Alkhairi. Mallan bayan haka kuma munaso ka kara mana wata fadakarwa akan miyagun halaye.

  3. Allah ya taimaka malam.gaskya muna godya da jinjina ga ira-iren fadakarwa da kuke mana,bisa lura da tarin shubuhohinda ta kunsa

  4. malam Allah yasaka da alkairi wannan tunatar da akayi Allah yabamu ikon amfani da ita ……ameen

Leave a Reply

%d bloggers like this: