SAKO GA MASU FAMA DA WASWASI(Mal.Aminu Ibrahim Daurawa)

Danna nan domin shiga karatu Online

SAKO GA MASU FAMA DA
WASWASI
waswasi ciwone mai hatsarin
gaske, da mutane da dama suke
fama da shi, wani nasa da yawa
wani kadan, waswasi yana shiga
ko’ina cikin rayuwar dan-Adam,
kuma yakan jawo kunci, da
damuwa ga wanda aka jarabta
dashi, an kasa waswasi kashi
uku,na daya: Waswasi a cikin
addini, wanda mutum zai dinka jin
wasu abubuwa masu nauyin fada
ko aikatawa, ko kudurewa, na biyu:
Waswasi acikin ibada, wani a
wajan tsarki, wani a wajan alwala,
wani a wajan sallah, ko Azumi, da
sauran ibadu, yayi tayi, yana
maimaitawa, ko yadinka jin
batayiba, na uku, waswasi a wajan
mu’amala, ya dinka yawan zargin
jamaa, da kokwanto, har matarsa
yana zargin tana cin amanarsa, ko
mijinta tana zarginsa, ko
abokansa. ko yadinka ganin kowa
makiyinsa ne, baya sonsa da
alkhairi,sai yawan zargi da
kokwanto, da shakka, wani har ta
kaishi ga kashe kansa, ko ya hadiyi
zuciya mutu !
maganin haka abu goma ne :
1- Neman tsarin Allah
2- Yawan anbaton Allah
3- Dagaro ga Allah
4- Yawan karatun Alkur’ani da
sauraronsa
5- Bin Sunnah da koyarwarta
6- karanta tarihin magabata
7- Mutum ya daina yawan zama
shi kadai, da yawan tunanin abin
duniya
8- yawan Addu’a
9- Abota da mutanan kirki
10- Rashin yarda da duk abinda
zuciya ta sakawa mutum. Allah ya
tsaremu

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

2 responses to “SAKO GA MASU FAMA DA WASWASI(Mal.Aminu Ibrahim Daurawa)”
  1. Idrismuhammad Avatar
    Idrismuhammad

    Allah yasaka da alkhairi,sukuma masu irin wannan lalura Allah yayaye masu.

  2. Ukasah adamu Avatar

    Mun gode

Leave a Reply

Categories
Latest updates