RIKO DA SUNNAH SHINE HAKIKANIN SON ANNABI(Muhammad Kabiru Haruna Gombe)

Annabi Muhammad Tsira da
Aminci Su tabbata a gare shi yana
cewa duk wanda yayi riko da
Sunnah ta tamkar yayi riko da
garwa shin wuta ne.
In ka fahimci wannan Hadisin zaka
san da cewa duk wanda zai yi koyi
da karantarwan Annabi sai yaci
karo da matsaloli da yawa daga
makiya Sunnah masu cewa suna
son Annabi a baki.
Dole sai kayi koyi da Annabi kafin
kace mana kana son Annabi, shin
saka wandon ka irin na Annabi ne?
Ko mu’amalarka irin na Annabi ne?
Shin kana yin addini kamar yadda
Annabi yazo dashi? Ko kuma kana
ganin Annabi bai iya ba kaine ka
iya, shi yasa ka fito da sabon abu a
addini kuma da sunan neman lada,
in hakan ya tabbata sai ka binciki
kanka a ina ka samo shi? A wurin
Annabi ko a wurin sahabbai?
Addinin nan na Musulunci sauki
gare shi, dukkan Ibadan da zakayi
yana nan a rubuce, a Qur’ani ko a
Hadisi, ka koma ka bincika zaka
samu, kayi yadda Annabi yayi ko
yace ayi shi kenanan ka gama
naka.
Amma rayuwar in ka duba tarihin
Annabawa tun daga farko har
zuwa yau zakaga mafiya yawan
wadanda ake kashewa ko zagi ko
munanan kalamai gare su laifinsu
kawai sunce ayi addini yadda Allah
ya saukar,
Ya kai Malamin Sunnah dama mai
koyi da Sunnah, ka sani cewa aikin
da kakeyi ja ne, Dole sai kaji
munanan kalamai daga makiya
Sunnah, wasu ma sai sun dokeka,
wasu ma kashe ka zasuyi, dukkan
wadannan abubuwan anyiwa
Annabawa, anyiwa sahabbai,
anyiwa tabi’ai, anyiwa Mutanen
Sunnah da dama, to kai me zai
dameka ko yasa kaji tsoron wanin
Allah? Daga radda ka fara samun
wadannan matsaloli kayi ta
addu’an Allah ya amshi ranka ta
wannan hanyar, mutuwa dole sai
anyita, in kaji tsoron mutuwa da
bindiga ko takobi, kana iya shan
farfesun rago cikinka ya baci kayi
ta gudawa har ka mutu, mutuwa
bata sallama.
Kuma muna tabbatar muku da
cewa babu batun daga kafa kan
kira ga tafarkin Sunnah, dole sai
mun yaki bidi’ah koda ta wannan
Hanyar zaizama sanadiyar
komawar mu ga Allah.
Masu zagi, Masu Duka, Masu Kisa,
Masu Qage da sauransu muna
dada sanar daku bakwa gaban mu,
Kuma da ikon Allah sai kowa ya
fahimci kiran da mukeyi na abi
Sunnah a kawar da Bidi’ah.
Muyi ta kokarin yin addini domin
yardan Allah, Allah zai taimake mu,
Allah zai karemu da sharrin Masu
Sharri, Allah bamu ikon fadin
gaskiya ga kowanene.
Allah ya nuna mana gaskiya
gaskiya ce ya bamu ikon binta, ya
nuna mana karya karya ce ya
bamu ikon kauce mata.

Click Here to Support our work

23 Comments

 1. Hmm. Mu munce so da bam koyi daban yadda zaka gane wannan shine abu lahab baiyi koyi da annabi ba amma son da yayiwa annabi na rana daya allah yadauke masa azabar kabari duk ranar littani(monday).
  Wannan ingantaccen hadisi ne yana cikin bukhari.

  1. nalura kamar jahilci nadamunka dan ma bakasan me akenufi da izala ba ah larabce to izala tana nufin kaudawa ma’anan izalatul bidi’ah wa’iqa matus sunnah shine akwaida bidi’ah atsaida sunnah kuma maganan son annabi dakake karyane kaki koyi da annabi kuma kace kana sonsa domin inharkana sonsa takai koyi dashimana kuma kana maganar wai izala annabi yasan da ita tobari kaji ixala tanakan sunnah ne dan haka annabi yasan da ita kukuma kufada mana salatil fati dakukace tafi saukan qur’ani so6 sai kufada mana

 2. ya ku yan uwana musulmain nigeria, dun Allah mu bar son zuciya da kwadayin abin duniya mu kauda bidi’a mu rungume sunnah. mu kuma wayanda munce mun ansa kiran sunnah, dun Allah dun Manzon tsira muyi hattara kan mu a tare ba maganan rabuwa. Allah ya sa mu dace. (daga usman isa el-yazaki kwandare, lafia north dev. area, nasarawa state)

 3. DUN ALLAH YAN BIDI’A SUNA BIN MU A KAFA DUN SU TABBATA SUN GANI MUN RABU MUSAMMAN MA YAN BIDI’AN NASARAWA STATE. DUN ALLAH DUN MANZO TSIRA KU MANYAN MALLAMAN MU MUSAMMAN KAMAR MALLAM ASHAIKH THANI YAHAYA JINGIR, SHAIKH ABDULLAHI BALA LAU, SHAIKH ABUBAKAR GERO ARGUNGU, SHAIKH MUHAMMAD KABIRU HARUNA GOMBE, DA DAI SAURANSU KU JINKIRTA KU HADA MANA KAIN A WAJE DAYA DUN MU SAMU INDA ZA WARGAJE BIDI’A MU KUMA KUNYANTAR DA SU DA KARFIN ALLAH TA’ALA. ALLAH YA BA MU SA’A (daga usman isa el-yazaki kwandare, lafia north dev. area, nasarawa state 08172870166)

 4. Allah sarki wai idan banda rashin kunya irin Na wannan mutumin da wasu kuma shine malaminsu. Ai ita addinin taku shekaranta 35 aduniya karankanka ka girmeta ashe kafin bayyanar izala kai da iyayenka kafiraine ??
  Annabi ya isar da aikansa kuma bai barkomai ba toh idan hakane me yasa kuka kirkiri Izala?cikin biyu za ai daya ko bai isar da aika ba kukesa ku cika masa ko kuma bai iyaba sai yasa kuka bullo wa,iyazubillah’.
  Rashin sani yafi dare duhu ilimin da babu aiki dashi gwamma babu, ilimin jayayya baya amfanar da mutum.
  Idan ma banda jahilcin yan izala da malamansu ya za .ayi jariri yace yafi kakansa shan miya wannan ai rashin hankaline a fili abun nufi anan shine musulunci ya gangaro mana najeria hijira na da shekara 507 wanda yai daidai da 1086 miladiya Annabi Isa(A.S)Kuma tunda ka nan ansamu mahadda alqur,ani babu iyaka anyi malamai wadanda duniya tasan dasu kamar Shehu usman dan fodio,ABDULLAHI GWANDU, Nasir kabara,ABDULFATAHI MAIDUGuri da sauransu kafin zuwar wannan shaidaniyar kungiya a 1978 da wasu jahilai da batattu suka kafata.
  Abun tambaya anan iyayen iyayenku ba musulunci sukayi ba kune musulmai yanxu??

 5. aminullah inaso kasani indai katabbata musulmi yanada kyau kayi aikin da abinda annabi muhammad (s.a.w) yaxo dashi dan tawannan hanyanne xaka nuna mushi kanason shi karyane kace kanason mutun anma bakai masa biyayyaba wannan baso bane

 6. KAI MLM KAJI TSORON ALLAH. KUMA KA DAU JAWAHIRUL MA’ANI KA GURFANA GABAN MALAMAN MU SU KARANTA MAKA BA KAYI SHARRI BA.

 7. don ALLAH ina mai tambayan dukkan dan izala ko basalafe ko wani mai jingirtawa kanshi sunna da ya fadamina wani sunna suke aikatawa wanda mu yan darika bamayi kuma ya tabbata annabi tsira (saw) yayi. sannan bidi’a da suke lakaba mana don ALLAH su basayi. kabiru gombe mai kake nufi da biyayya cewa annabi mutun ne kamarka wa iyazubillahi ko iyayensa na wuta haka kake nufi da biyayya amma ALLAH ya wadaranka kuma ya shiryeka. kalmar biyayya ga annabin tsira bawai shine kawai kayi sallah, azumi, zakka, ko hajj ko shedarka cewa babu abun bautawa da gaskiya sai ALLAH shine kadai ne biyayya. mallam kabiru karanta suratul munafiqun kaga siffofin munafikai. kuma wadannan arkan basu kai mutun aljanna sai yayi nitso na gaske a soyayya ga ma’aiki. misali a bukhari akwai hadisin zulkuwaisara yana yin dukan arkan dinnan amma kash ba biyayya iranta soyayya annabi atare dashi saboda haka dan wuta ne. ature dukkan wannan shin gaskiya ne dan darika baiwa annabi biyayya? ta yaya?

 8. Wlh karya kuke yi makaryata makiya annabi s.a.w da ahlinsa tir da irin wannan yaudara da kuke yi wa jahilan mabiyanku wlh duk xuciyar da bata so annabi s.a.w ba dole ta shiga wuta. ta ya xa kuce kune masoya annabi s.a.w na gaskiya alhalin kuna zagayewa kuna zagin wasu daga cikin sahabban annabi kai harma da mahaifansa waiyaxibilla allah ya ganar da ku don duk wanda baya son annabi wlh yana cikin halaka da wahala. Ustaz ka so annabi da ahlinsa kawai

Leave a Reply

%d bloggers like this: