Yawaita yiwa Annabi Sallallahu alaihi Wasallama salati a dare da ranar Juma’a

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Yana daga cikin ibada mai falala yiwa Annabi Salati, musamman a daren juma’a da kuma ranar juma’a, Annabi ya bada Labarin cewa ana bujuro mishi da duk salati da akeyi masa. Shin kana so a bujuro da salatinka kaɗan?

Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace:

إنَّ مِن أفضَلِ أيَّامِكم يومَ الجُمُعةِ؛ فأكثِروا عليَّ مِن الصَّلاةِ فيه؛ فإنَّ صَلاتَكم معروضةٌ عليَّ

سنن أبي داود: ١٥٣١

Annabi yace:

Haƙiƙa ranar juma’a na daga cikin mafi alherin ranakunku, ku yawaita yimin salati acikin wannan rana, domin ana bujuro min da Salatin da kukeyi min.

yawaita yiwa Annabi Salati ranar juma’a sunnah ce mai ƙarfi da ya dace Musulmi yayi riƙo dashi. Daga zarar daren juma’a ta shiga sai mutum ya fara har zuwa faɗuwan rana ta ranar Juma’a.

Allah zai gafarta wa mutum zunubansa, ya kuma yaye masa damuwowinsa da salati wa Annabi, sannan ya ishe mutum alfahari ace an bujuro da salatinsa mai yawa ga Annabi. Allah ya ƙara mana son Annabi da kuma koyi dashi. Ameen.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories