SAKO ZUWA GA SOJOJI MUSULMAI DA AKA TURA MALI!!!

Danna nan domin shiga karatu Online

SAKO ZUWA GA SOJOJI MUSULMAI DA AKA TURA MALI!!!
Hattara Musulmai Sojoji da aka tura mali domin yaki… Ga sako daga Allah yace a sanar daku…
Allah(swt) mahaliccinku mahaliccin komai yace:
ﻭﻣﺎ ﻛﺎﻥ ﻟﻤﺆﻣﻦ ﺃﻥ ﻳﻘﺘﻞ ﻣﺆﻣﻨﺎ ﺇﻟﺎ ﺧﻄﺄ ﻭﻣﻦ
ﻗﺘﻞ ﻣﺆﻣﻨﺎ ﺧﻄﺄ ﻓﺘﺤﺮﻳﺮ ﺭﻗﺒﺔ ﻣﺆﻣﻨﺔ ﻭﺩﻳﺔ
ﻣﺴﻠﻤﺔ ﺇﻟﻰ ﺃﻫﻠﻪ ﺇﻟﺎ ﺃﻥ ﻳﺼﺪﻗﻮﺍ ﻓﺈﻥ ﻛﺎﻥ ﻣﻦ
ﻗﻮﻡ ﻋﺪﻭ ﻟﻜﻢ ﻭﻫﻮ ﻣﺆﻣﻦ ﻓﺘﺤﺮﻳﺮ ﺭﻗﺒﺔ ﻣﺆﻣﻨﺔ
ﻭﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻣﻦ ﻗﻮﻡ ﺑﻴﻨﻜﻢ ﻭﺑﻴﻨﻬﻢ ﻣﻴﺜﺎﻕ ﻓﺪﻳﺔ
ﻣﺴﻠﻤﺔ ﺇﻟﻰ ﺃﻫﻠﻪ ﻭﺗﺤﺮﻳﺮ ﺭﻗﺒﺔ ﻣﺆﻣﻨﺔ ﻓﻤﻦ ﻟﻢ
ﻳﺠﺪ ﻓﺼﻴﺎﻡ ﺷﻬﺮﻳﻦ ﻣﺘﺘﺎﺑﻌﻴﻦ ﺗﻮﺑﺔ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻪ
ﻭﻛﺎﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻤﺎ ﺣﻜﻴﻤﺎ.
Kuma bã ya kasancħwa ga
mũmini ya kashe wani mũmini,
fãce bisa ga kuskure. Kuma
wanda ya kashe mũmini bisa ga
kuskure, sai ya ´yanta wuya
mũmina tare da mĩƙa diyya ga
mutãnensa, f?ce idan sun bari
sadaka. Sa´an nan idan (wanda
aka kashe) ya kasance daga
wasu mutãne maƙiya a gare ku,
kuma shi mũmini ne, sai ya
´yanta wuya mũmina. Kuma
idan ya kasance daga wasu
mutãne ne (waɗanda) a
tsakãninku da tsakãninsu akwai
alkawari, sai ya bãyar da diyya
ga mutãnensa, tare da ´yanta
wuya mũmina. To, wanda bai
sãmi (wuyan ba) sai azumin
watanni biyu jħre, dõmin tũba
daga Allah. Kuma Allah Yã
kasance Masani, Mai hikima.
Sannan ya sake cewa:
ﻭﻣﻦ ﻳﻘﺘﻞ ﻣﺆﻣﻨﺎ ﻣﺘﻌﻤﺪﺍ ﻓﺠﺰﺍﺅﻩ ﺟﻬﻨﻢ ﺧﺎﻟﺪﺍ
ﻓﻴﻬﺎ ﻭﻏﻀﺐ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﻟﻌﻨﻪ ﻭﺃﻋﺪ ﻟﻪ ﻋﺬﺍﺑﺎ
ﻋﻈﻴﻤﺎ.
Kuma wanda ya kashe wani
mũmini da ganganci,to,
sakamakonsa Jahannama,
yana madawwami a cikinta
kuma Allah Yã yi fushi a kansa,
kuma Ya la´ane shi, kuma Ya yi
masa tattalin azãba mai girma.
Ga Kuma abinda manzon mu(saw) yace a fada muku……
Manzon Allah(saw) yace:
(لزوال الدنيا أحون عند الله من قتل مؤمن بغير حق.
Gushewar duniya baki dayanta da duk abinda ke cikinta itace tafi sauki awurin Allah fiye da kashe ran mumini guda daya..
Wannan itace zancen fiyayyen halitta muhammadu rrasulillah(saw)….
Wannan sako nawa mai harcen damo ce, domin wanda ya karantata koshi musulmi ne ko ba musulmi ba zai fahimta cewa addinin musulunci ba addini ne na ta’addance ko na rikici ba, addinin musulunci addinin zaman lafiya ne ga duk wanda ya nemi zaman lafiya da ita..
Yaa ku sojoji musulmai ku dauki wannan ka’ida aduk inda zaku tafi aiki aciki da wajen kasa ita zata kaiku ga tsira… Ku kiyaye zubarda jinin musulmi a kowani hali….. ZABI YA RAGE TAKU!!!!

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates