HUDUBA DAGA MASJIDU TAUHEED, ANGUWAR AIN SHAMS ANAN BIRNIN ALQAHIRA, WANDA SHEIKH ABDULLAH YA GABATAR.

·

·

HUDUBA DAGA MASJIDU TAUHEED, ANGUWAR AIN SHAMS ANAN BIRNIN ALQAHIRA, WANDA SHEIKH ABDULLAH YA GABATAR.
بسم الله الرحمان الرحيم.
Duk da dai Allah bai bani daman isa masallaci akan lokaci ba, ga dan kadan daga abinda na tsakuro mana…
Na shigo malam yana kan magana akan girmama annabi(صلى الله عليه وسلم‏)‏
Annabi shine fiyayye aduk cikin halittun Allah baki daya, dolene ga duk musulmi yayi koyi dashi acikin duka lamuransa…. Yaci gaba da bayani har ya gangaro kan yahud da nasara, yace bai dace ace musulmi yayi koyi dasu ba ta ko wata hanya, haka kuma bashi yiwuwa mutum ya sosu. Acikin zancensa sai ya kawo fadin Allah(subhanahu wa ta’ala) acikin suratu baqara ayah ta 120
وَلَنْ تَرْضَى عَنْكَ الْيَهُودُ ولَا النَّصَارَى حَتَّى تَتَّبِعَ مِلَّتَهُم قُلْ إِنَّ هُدَى اللَّهِ هُوَ الْهُدَى وَلَئِنِ اتَّبَعْتَ أَهْوَا ءهُمْ بَعْدَ الَّذِي جَاءَكَ مِنَ الْعِلْمِ مَا لَكَ مِنَ اللَّهِ مِنْ وَلِيٍّ وَلَا نَصِيرٍ
.
Kuma Yahũdu bã zã su yarda da kõme daga gare ka ba, kuma Nasãra bã zã su yarda ba, sai kã bi irin aqidarsu. Ka ce: “Lalle ne, shiriyar Allah ita ce shiriya.” Kuma lalle ne idan ka bi son zũciyõyinsu a bãyan abin da ya zo maka na ilmi, bã ka da, daga Allah, wani majibinci, kuma bãbu wani mataimaki.
Sannan ya sake kawo wata ayar acikin baqara ayah ta 217.
يَسْأَلُونَك عَنِ الشَّهْرِ الْحَرَام قِتَالٍ فِيهِ قُلْ قِتَالٌ فِيهِ كَبِيرٌ وَصَدٌّ عَنْ سَبِيلِ اللَّهِ وَكُفْرٌ بِهِ وَالْمَسْجِدِ الْحَرَامِ وَإِخْرَاجُ أَهْلِهِ مِنْهُ أَكْبَرُ عِنْدَ اللَّهِ وَالْفِتْنَةُ أَكْبَرُ مِنَ الْقَتْلِ وَلَا يَزَالُونَ يُقَاتِلُونَكُمْ حَتَّى يَرُدُّوكُمْ عَنْ دِينِكُمْ إِنِ اسْتَطَاعُوا وَمَنْ يَرْتَدِدْ مِنْكُمْ عَنْ دِينِهِ فَيَمُتْ وَهُوَ كَافِرٌ فَأُولئكَ حَبِطَتْ أَعْمَالُهُمْ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ وَأُوللئكَ أَصْحَابُ النَّارِ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ
Suna tambayar ka game da Watan Alfarma: yin yãki a cikinsa. Ka ce: “Yin yãki a cikinsa babban zunubi ne, kuma hani daga hanyar Allah, da kuma kãfirci da Shi, da kuma da Masallaci Tsararre, da Kuma fitar da mutãnensa daga gare shi, shi ne mafi girman zunubi a wurin Allah.” Kuma fitina ita ce mafi girma daga kisa. Kuma bã su gushħwa suna yãkinku har su mayar da ku daga barin addininku idan za su iya. Kuma wanda ya yi ridda daga gare ku ga barin addininsa har ya mutu alhãli kuwa yana kãfiri, to, wadannan ayyukansu sun bãci a cikin dũniya da Lãhira. Kuma wadannan abõkan Wuta ne, sũ a cikinta madawwama ne.
Sannan sheikh Abdullah ya kara jaddada mahimmancin shari’ar musulunci, yace dole ne a dawo ayi shari’a da dokar Allah, a kaurace wa tsarin kafurci ta democracy… Ya maimaita wannan kira har sau biyu,
Malam ya cigaba da bayyana aqeedojin ahlussunnah wal jama’a yanda yace su ahlussunnah wasu jama’a ne masu kawo gyara acikin al’ummah, ba masu tada hankali ba.
Akarshe malam ya kammala hudubarsa da yiwa kasar masar addu’ar alheri, da ita da matasanta, da duk sauran kasashen musulmai, sannan ya sake yiwa kasar masar addu’ar Allah kareta da sharrin ‘yan shi’a da kuma sauran kasashen musulmai suma Allah karesu daga sharrin shi’ar….. Ya karasa addu’ar ne da yiwa ‘yan’uwa musulmai a syria addu’a Allah ya tserar dasu daga sharrin mugayen azzalumai masu kashesu.
Allah ka amfanar damu da abinda muka saurara.
والصلاة والسلام على رسول الله.

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: