KUYI RIKO DA AQEEDAR SALAF KU KAUCE WA GURBATATTUN AQEEDU

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Bismillahirrahmanirrahim, wassalatu wassalamu Ala Rasulillah…
Kuskurene kaji musulmi yana cewa wai meyasa kiristoci ba’ajin suna bayyana tsabaanin dake tsakaninsu, bayan kowa ya sani cewa bambamcin Ra’ayi da rabe rabe dake tsakaninsu tafi namu yawa?
toh a hakikanin gaskiya duk masu irin wannan fahimtar suna kuskure.
Da farko abinda zamu lura dashi shine: shin kiristoci addinin gaskiya sukeyi? Amsa itace addininsu gurbatacciyar addinice wadda ba daga Allah take ba. Domin ba koyarwar annabi isha(as) suke bi ba… Saboda haka a kullum zasuyi ta rarrabuwa har tashin qiyaama Kansu bazai taba haduwa abisa ka’ida wadda Allah ya bayyana cikin suratul baqara. Allah yace: ‘INSUKA JUYA BAYA TOH SUNA CIKIN TSABANI’.
Toh shiyasa dama akan karya suke, da zaran kuka kirkiri karya kuka ginu akai sai wani daga cikinku aka mishi abinda baiyi mishi dadi ba in yaje ya bude tasa kungiyar, toh kaga a lokacin ku bazaku damu da ku tsangomeshi ba saboda kunsan kuma akan karya kuke baku da hujjah. Toh haka abin yake, duka kiristoci yanzu addininsu ta karyace, saboda haka zaiyi wuya kaga makaryaci yana tuhumar dan’uwarsa makaryaci da laifin karya…
Sannan su kiristoci basu da kishin addininsu, toh yaya zakayi kishin abinda kasan ba daidai bane? Sannan kuma shaidan bazai damu da ya dinga haddasa musu fitina tsakaninsu ba. Sabida su batattu ne.
Toh wa’innan abubuwa suna daga cikin abubuwan da ke sanya kiristoci basu sukan junansu. Da hakane wasu musulmai sai su rudu suga kaman kiristocin kansu a hadene. A’a sam. Kansu ba a hade take ba, bala’in dake tsakaninsu tafi tamu mu musulmai. Amma saboda munafunci ne yasa kake ganinsu tare.
Toh amma mu musulmai wannan tsabani wata abace wadda Allah ya kaddara dole adinga samunta tsakaninmu tun zamanin annabi. Annabi yakan bada umarni wa sahabbai wasu su fahimce ta dabam, wasu ma haka. Dubi lokacin da annabi(saw) ya bada umarnin aje ya yaki yahudawan banu kuraiza. Cewa yayi ‘DUK WANDA YAKASANCE CIKINKU MAI SAURARO MAI BIN UMARNI, TOH KADA YAYI SALLAN LA’ASAR SAI A BANU KURAIZA’. Sai sahabbai suka kama tafiya, basu isa banu kuraiza ba sai lokacin sallah ta samesu. Sai wasu sukace su tsaya suyi sallah, sai wasu sukace A’a bazasu tsaya ba, domin annabi yace kada suyi sallah sai a banu kuraiza. Sai daya bangaren sukace ai ba haka annabi yake nufi ba, ya bamu umarnin muyi sauri ne kada sallar ta samemu a hanya amma tunda munyi iya kokarinmiu amma sai ta samemu to ya zamuyi sai muyita, domin Allah yace: ‘ITA SALLAH WATA FARILLA CE MAI LOKUTA’ kaga dole mutsaya mu gabatar da sallah kafin mu wuce. Daya bangaren sukace A’a. Haka dai akayi daya bangaren suka tsaya sukayi sallansu, bayan sun kammala suka tafi kafin daya bangaren sukayi sallah anan banu quraiza… Sukaje sukayi yakin kuma suka sami nasara. Bayan sun dawo kuma annabi bai zargi kowa ba acikinsu… Toh ku duba sunyi tsabani amma basu rabu ba. Kunsan akwai banbanci tsakanin tsabani da rabuwa.. Muna iya samun tsabani Amma rabuwa Allah ya hanamu mu rarrabu… Shi yasa Allah yace ‘INKUKA SAMI TSABANI TSAKANINKU TO KU MAIDASHI ZUWA A ALLAH DA MANZONSA INKUNKASANCE MASU IMANI DA ALLAH DA MANZONSA’.
Kaga wannan ka’ida kenan na muminai, in aka samu tsabani ba zage zage za’ayi ko tsinewa juna ba. A’a bayani za’ayi kowa ya kawo hujjarsa, wanda yafi karfin hujjah zai zama shine mai gaskiya. Duk wanda kaga ya tsaba wa wannan ka’idar toh ka tabbata ba munini bane shi… Sannan haka ‘yan’uwa in muka dubi rayuwar magabata zamuga cewa cike yake da tsabani tsakaninsu ta fatawa. Amma duk da haka basu rabuwa, suna sallah tare suna mu’amalla tare… Kowa kuma yana tallata tashi fatawar yana karfafata da hujjojinsa, kaga sai abar wa mutane su kuma suyi hukunci… Toh haka wannan ka’idar ya kamata mu dauka, mu sani dolene mu sami tsabani amma hakan ba yana nuna mun rabu kenan ba, muci gaba da kafirta juna, A’a abinda zamuyi shine mubi ka’idar da Allah ya shimfida mana, shine mu maida tsabaninmu zuwa ga Allaah yace manzon Allah yace shi zai samar mana da zaman lafiya…
Sai dai abu mai mahimmanci anan shine akwai tsabani da ake kiranta tsabani ta fikhu. Akwai kuma ta aqeedah. tsabani mai hatsari itace ta aqeedah, ta tauhidi. Da zarar kukayi tsabani a akan aqeeda toh ku tabbata dayanku na kan halaka. Kuma haka inkuka dubi yawancin tsabani da ya auku sakanin sahabbai da tabi’ai da mabi dasu, zaku samu tsabani ce wadda bata shafi aqeedah ba.
Sannan akwai wasu musulmai masu ganin cewa toh ai kowa ya rike tashi fahimta abar bayaani.. Abar yiwa juna raddi Sai suce ai Allah yace ‘LAKUM DINIKUM WA LIYA DEEN’
Toh wannan kuskurene. In akayi haka har a mutu wani bazai fahimci addini ba. Domin ku dubi misali lokacin da bid’oi da Aikin tsabo suka cika kasannan da ace malaman sunnah shiru sukayi basu tashi sunyi da’awah ba shin kuna nufin da muma mun fahimci sunnan? Toh haka abin yake ba shiru za’ayi ba, kowa yayi bayaani ya kafa hujjah da dalilansa sai abar mabiya su kuma suyi hukunci…
Sannan ‘yan’uwa in ana maganar rarrabuwar al’ummah ya dace mu duba shin meye da ya kawo muka rabu? Ba komai bane sai tsaba wa Allah da akayi, aka kauce wa tsarin koyarwar manzon Allah(saw) toh ko in anason hadin kai dole a dawo abi koyarwar manzon Allah. A koma abi tafarkin muminan farko.. Domin Allah yace..
”Duk wanda ya tsabawa manzon Allah(s.a.w) bayan shiriya ta bayyana a gareshi ya kuma bi tafarkin da ba na muminai ba, zamu jibinta masa abinda ya jawo wa kansa, sannan mu shigar dashi jahannama, makoma tayi muni”
Toh kaga anan inkanason tsira sai ka zubar da komai ka dawo kabi tafarkin muminan farko. Wanda basu san darikarka ko wani malaminka, ko shehinka, ko kungiyarka ba.
Kaga a yanzu duk wanda yazo da wata abu wadda bata da asali daga muminan farko ya tabbata kuskure yakeyi… Hadisi ne, ayah ce. Ka tabbata in zaka fassara ta kada taci karo da fassarar da muminan farko sukayi mata….
Sannan wata misali da zan sake bayarwa shine, ku dubi mabiya tafarkin sufanci a Nigeria. Lokacin da da’awar sunnah ta kunno kai a Nigeria wani irin fadane basuyi da ita ba? Kisa, dauri duka, zage zage da cin mutunci babu irin wadda basuyi wa mabiya sunnah ba. Amma da yake lamarin na Allah ne, Allah ya tabbatar da al’amarinsa. Amma ku dubi lokacin da aqeedar shi’ah ta shigo Nigeria. Shin sufaye sun fita sunyi fada da ita? Shi yasa da yawa daga cikin mabiyansu har yanzu sun kasa fahimtar muguwan aqeedar shi’ah. Zaga gansu tare a kullum suna sallah tare suna yin mauludi tare suna yiwa annabi rawa tare. Amma a karshe dan shia’ah ya koma gefe yana zagin sahabbai… Da yawa zaiyi wuya mabiya tafarkin sufanci su fahimci aqeedar shi’ah saboda muguwar aqeedar taqiyyah… Saboda haka nake kira ga mabiya darikar sufaye ku koma cikin littafansu ku karanci aqeedarsu. Mu da kuke ce mana makiya annabi, kuma muna zagin waliyyai shiyasa kuka tsanemu, toh suma ‘yan shi’ar suna zagin waliyyai kuma suna cin mutuncin annabi, inkunce munce iyayen annabi suna wuta duk da baku da hujjah, toh suma sunce iyayen annabi na wuta. Sunce wasu daga cikin matayensa kafirai ne, sannan kuma su waliyyan da suke zagima wanda Allah ya yadda dasu ne, kuma annabi ya shaida, duniya ma suka shaida… Sune sahabban manzon Allah.. Toh dun Allah ‘yan’uwanmu mabiya tafarkin sufanci, da mai zagin sahabbai dame kira ga ayi musu biyayya wanne yafi? Kuyi wa kanku adalci. Shi yasa kwanakin baya nayi rubutu kan ‘ALAKA TSAKANIN SHI’A DA DARIKA’ bude wannan link din don ka karanta.

Alaka Tsakanin Sufanci Da Shi’anci!


Sannan ‘yan’uwa inaso ku fahimta, samun zaman lafiyar mutum shine yabi tafarkin annabi, a aqeedance da ibada. Abi sunnah shine kawai zaman lafiyarmu. Domin wannan ka’idar ta ‘FA’IN TAWALLAU FA’INNAMAHUM FI SHIKAAK’ duk wa’inda suka tsabawa wa annabi zaka ga kansu bazai taba haduwa ba.
Misali dubi sufanci sunanan sun rarrabu kashi kashi har sama da kashi dari uku, dukansu da yau zaka zo kace musu suzo subi waliyyi daya bazasu yarda ba. Kowa da darikarsa kowa da waliyyinsa. Sai dai kawai akwai wasu aqeedoji tasu ta sufaye wadda take hadesu wuri daya kaga kamar kansu daya. Amma sam kansu ba daya bace. Domin zakaji wannan nacewa a ka’ida ta darikarmu babu ziyarar wani waliyyi wanda ba dan darikarmu ba. Da dai sauran ka’idoji tasu wadda bata da tushe… Sannan ku dubi ‘yan shi’ah dukansu suma kansu a rabe. Kowa a shi’ar da tashi hanyar. Sun rabu a wasu aqeeda tasu ta shi’ar…. Toh haka tsarin take kaman yanda yahudu suka kirkiri karya. A matsayin addini suka yita rarrabuwa haka yanzu ma duk wasu musulman da suka riki karya a matsayin addini zaka ga kullum suna rabuwa.. Sannan zakaji basu yawaita bayanin bambancin dake tsakaninsu saboda tsoron kada kiliu taja bau…
Amma dubi wa’inda sukebin sunnah wa’inda ake kiransu da suna sunni, ko ahlussunnah. Ma’ana mabiya sunnan annabi, ko ‘yan salafiyyah, ma’ana masu bin tafarkin salaf. Ko ince muku masu kungiyar jama’atu izalatil bid’ah wa’ikamatussunnah anan Nigeria kaman yadda akafi saninsu… Duka sunansu ne wannan kace musu ‘yan salafiyyah ko ahlussunnah. Inka dubi duniyar sunnah baki daya zaka samu kansu a hade yake, koda sun samu tsabani zaka samu akan mas’ala ce da bata shafi aqeeda ba, sannan koda ta shafi aqeeda zaka samu wasu ‘yan tsiraru ne kawai wanda suke son tsabawa koyarwan magabata…
Ahlussunnah sune ‘hirzul ummah’ kariya wa al’ummar musulmai, domin zaka samesu kullum masu umarni ne da alkhairi da kuma hani da mummunan aiki. Kaga duk mutane da suka zama haka toh hakika sun zama kariya ga al’ummah, domin inda badunsu ba da Allah ya tsine wa al’ummah kaman yadda ya tsine wa banu isra’ila… Allah yace ‘AN TSINE WA WA’INDA SUKA KAFIRCE DAGA CIKIN BANU ISARA’LA. SUN KASANCE BASU HANI DA WANI MUNKARI DA SUKA AIKATA’
Sannan annabin rahama(saw) yace ‘KU DINGA UMARNI DA KYAKKYAWAN AIKI, SANNAN KU DINGHA HANI DA MUMMNUNA KO KUMA ALLAH YA TSINE MUKU KAMAN YADDA YA TSINE WA BANU ISRA’I’ll…….A.K.K(SAW)…
Sannan Allah yace: ‘A SAMU WASU AL’UMMAH DAGA CIKINKU SUNA KIRA ZUWA GA ALKHAIRI KUMA SUNA HANI DA MUMMUNAN AIKI WA’INNAN SUNE MASU RABAUTA’
Da wa’innan ka’idan ne yasa zaka samu ko’ina ahlussunnah suna da kungiya ta da’awa domin dabbaka umarnin Allah da manzonsa….
Tsabanin mabiya wata tafarki wadda ba ta sunnah ba.
‘Yan’uwa kuyi hakuri in na tsawaita, bukata ta shine a fahimta, banyi wannan rubutu don inci mutuncin wani ba. ‘IN URIDU ILLAL ISLAHA MASTADA’ATU’
Allah yasa mugane. Allah ya shiyar damu hanya madaidaiciya…..
Sannan ‘yan’uwa A dage da karatu, sannan a dinga addu’ah…..
Yaa Allah ka nuna mana gaskiya ka bamu daman binta, ka nuna mana karya ka bamu daman kauce mata. Muyita da ikhalas insha’Allahu Allah zai nuna mana gaskiya.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

4 responses to “KUYI RIKO DA AQEEDAR SALAF KU KAUCE WA GURBATATTUN AQEEDU”
 1. Aminullah bangire Avatar

  A kai ga jinin manzon Allah wazaibi wani ga dakir sufaye wanda basuda komai sai son manzon Allah da tsoron Ubangiji (S.W.A) xikin da yiwa annabi salati susuka sa,agaba

 2. Aminullah bangire Avatar

  “A kai ga jinin manzon Allah wazaibi wani ga dakir sufaye wanda basuda komai sai son manzon Allah da tsoron Ubangiji (S.W.A) xikin da yiwa annabi salati susuka sa,agaba”!!!

 3. Garba Abdullahi Avatar
  Garba Abdullahi

  Allah ya saka.

 4. abdul Avatar

  aslm dan ALLAH ka koma makaranta

Leave a Reply

Categories
Latest updates