Hukuncin ɗaura Aure a Masallaci

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Tambaya: menene Hukuncin ɗaura aure a Masallaci?

Amsa: Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.

Wasu daga cikin Maluma sun sanya ɗaura aure a Masallaci a Matsayin Mustahabbi(Abin so). Sun kafa Hujja da cewa Hakan akwai Albarka aciki, sannan sun kafa Hujja da wani hadisi da aka rawaito daga Aisha Allah ya ƙara mata yarda sai dai hadisin Mai rauni ne.

Hadisin Tirmidhi ya rawaito shi a Hadisi: 1089

Sai dai cewa da sukayi akwai albarka acikin ɗaura aure a Masallaci, idan da Haka ne da Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya kwaɗaitar da yin hakan, haka nan da ya umarci Sahabbansa da ɗaura aure a Masallaci. Sai dai ba’a rawaito hakan ba.

A zamanin Annabi ba’a san taron ɗaurin aure irin wanda akeyi a zamanin mu yanzu ba. Wani Sahabin ma ya kanyi aure sai daga Baya Annabi ya sani.

An Tambayi Maluman Lajnatud-da’ima game da Hukuncin ɗaura aure a Masallaci idan har za’a kiyaye dokokin shari’ar Musulunci a wurin ɗaura auren ta yadda baza’a samu cuɗanya tsaƙanin maza da mata ba. Sai suka ce:

Idan har lamarin haka yake kamar yadda aka ambata babu laifi a ƙulla aure a masallaci

Fatawa Lajnatud-da’ima: 18/110

Sannan an tambaye su shin sanya ɗaura aure kodayaushe a masallaci Sunnah ne ko bid’ah. Sai suka ce:

Lamarin ɗaurin aure a masallaci na da faɗi a Shari’a. Amma bamu samu wani dalili da yake nuna cewa a maida ɗaurin aure acikin Masallaci kawai, sunnah ne, saboda haka a maida ɗaurin aure kodayaushe ya zama acikin Masallaci Bid’ah ne.

Fatawa Lajnatud-da’ima: 18/ 110-111

Sannan suka ƙara da cewa:

ɗaura aure acikin Masallaci bashi daga cikin Sunnah, sannan lazimtar ɗaura aure acikin masallaci da ƙudurce cewa sunnah ne: Bid’ah ne yin hakan.

Idan kuma ana samun mata wa’inda suke fita ba tare da suturce dukkan jikin su ba, ko yara ƙananu da zasu zo su cutar da mutane a Masallacin to baya Halatta a kai ɗaurin aure Masallaci.

Fatawa Lajnatud-da’ima: 18/111-112

Sheikh Muhammad Bin Salih Aluthaymeen yace:

Ban san asalin Mustahabbancin ɗaurin Aure a Masallaci ba, sannan bansan wani dalili daga Manzon Allah da yake nuna hakan ba, amma idan aka dace da waliyyin matan, da mai karɓan auren suna nan a Masallacin aka ɗaura to babu laifi.

Idan aka ɗaura auren a masallaci babu laifi yin hakan, amma idan mukace hakan Mustahabbi ne, muce wa mutane su rinƙa fita suna zuwa masallaci domin ɗaura aure, ko a rinƙa ce wa mutane duk aure da za’a ɗaura a rinƙa zuwa Masallaci ana ɗaura shi to wannan yana buƙatar dalili, nikuma bansan wani dalili kan haka ba.

Liƙa’ul Babil Maftuh: 167 Tambaya ta: 12

A taƙaice: babu laifi a ɗaura aure a masallaci. Amma maida ɗaurin aure ya zama dole sai a Masallaci wannan bashi da asali a addini, an ɗaura aure a zamanin Annabi, amma ba’a rawaito Annabi yayi umarni a rinƙa kai ɗaurin aure masallaci ba. Bal wasu Sahabban ma suna yin aure Annabi bai ma sani ba sai daga baya.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates