Hukuncin cin danyen nama

Tambaya: Shin ya halatta aci ɗanyen nama?

Amsa: Wasu daga cikin Maluma suna ga Makruhi ne cinsa, amma magana mafi inganci Halal ne, sabida babu wani dalili da ya hana cin ɗanyen nama, kuma kamar yadda aka sani asali acikin Abinci da abin sha shine halacci har sai an samu dalili da ya haramta ko kuma Ya zamto abin yana cutar wa. Domin Allah ya turo Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ne ya Halatta mana abu wanda yake Tsarƙaƙa ya kuma Haramta mana duk wani abu mai cutar wa. Kamar yadda yayi bayani acikin Suratul Araf ayah ta 157. Allah yasa mudace.

Click Here to Support our work

Leave a Reply

%d bloggers like this: