Hukuncin Shayar da dabba giya ko ciyar dashi Najasa da Hukuncin cin naman ta

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Tambaya: Shin ya Halatta a shayar da dabba giya domin hakan na ƙara musu cin abinci da kuma girman jiki?

Amsa: Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.

Allah maɗaukakin sarki ya haramta giya, sannan ya umarci Muminai su nesan ce shi. Shiyasa Maluma sukace baya halatta ayi wani amfani da giya.

Allah maɗaukakin sarki yace:

Yaku wa’inda sukayi Imani, lallai giya, da caca, da gumaka, da kibau na neman nasara Duka ƙazanta ne daga aikin shaiɗan, ku nesance shi ko zaku rabauta.

Suratul Ma’ida: 90

Wannan Ayah tayi umarni ga duk wani mumini da ya nesanci giya, shiyasa da yawan Maluma suka tafi kan haramcin amfani da giya koda kuwa ba sha za’ayi ba.

An rawaito Wani mai yi wa Ibn Umar Hidima ya shayar da Raƙumar sa giya Sai ibn Umar yayi masa Gargaɗi, ya hana shi.

Yazo acikin Almausu’atul Fiqhiyya game da hukuncin amfani da giya suka ce:

Jumhurun Malaman Fiqhu sun tafi kan haramcin amfani da giya domin yin jinya ko wanin sa, Kaman yin amfani da ita wurin yin man shafawa, ko abinci, ko jiƙa laka. Sun kafa Hujja da faɗin Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi “Allah bai sanya Warakar ku cikin abinda Allah ya haramta muku ba”

Almausu’atul Fiqhiyya: 5/25

Tariq bin Suwaid alju’ufi Allah ya ƙara masa yarda ya tambayi Annabi game da yin giya sai Annabi ya Hana shi, ko yaƙi masa yayi. Sai yace ai ina yin ta ne domin yin magani, sai Annabi yace masa. Giya ba magani bace cuta ce

Sahihu Muslim:1984

Saboda Haka baya Halatta mutum yayi amfani da giya wurin shayar da dabbar sa. Domin hakan zai janyo abubuwa kaman haka:

1. Cinikin giya: kuma haramun ne Allah ya tsine wa mai sayan giya, da mai cin kuɗin ta.

2. ɗaukan giya: Shima Haramun ne

3. Yin Giya: Shima haramun ne, domin zai iya yiwuwa shi mai kiwon da kansa zai rinƙa yin giyan, to baya Halatta kamar yadda mukayi bayani a Hadisin da ya wuce.

Amma game da Ciyar da dabba najasa wasu Maluman suna ganin Makruhi ne idan har dabba ce da ake ci, ko ake tatsar nonon ta, Wasu kuma suna ga ya Halatta. Kaman a ciyar da Kifaye jini ko makamancin sa. Sai dai idan Aka ciyar da dabba da najasa to dole sai an tsarƙaƙe shi kafin aci.

Hukuncin sa zai koma Hukuncin “Jallala” kenan a Fiqhun ce.

Jallala: shine dabban da mafi yawancin abinda yake ci najasa ne.

Kafin aci dabba da mafi yawancin abinda yake ci najasa ne sai an bar bashi wannan najasa ɗin na kwanaki kafin a yanka shi, ta yadda za’a rinƙa ciyar dashi da Halal. Har ya tsarƙaƙa. Kafin aci. Amma baya halatta aci shi ba tare da an tsarƙaƙe shi ba.

A Taƙaice: Baya halatta a shayar da dabba giya amma Game da ciyar dashi da wani nau’i na najasa akwai tsaɓani tsaƙanin maluma. Amma idann aka ciyar da dabba da najasa, kuma ya zama mafi yawan abinda yake ci najasa ne to sai an tsarƙaƙe shi kafin aci.

Tsarƙaƙewar kuwa shine: a dakatar da ciyar dashi wannan najasar kafin a yanka shi da kwanaki.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories