ALKAKI DA RUWAN ZUMA(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

ALKAKI DA RUWAN ZUMA
Ingantaccen Tarihin Fiyayyen Halitta
Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi
Wasallam
Fitowa Ta 21
Maraya Dan Gatan Ubangiji
Faruwar wannan abin al’ajabi ya sa
Halima ta mayar da yaron zuwa gidan
su saboda firgici da ya kama ta a daidai
lokacin yana da shekaru hudu.
Riwayoyin Ibnu Ishak – sarkin
malaman tarihin ma’aiki – a nan sun
dan yi tufka da warwara. Wai an ce ya
shiga shekara ta uku kenan, kuma an
ce ya kai shekara biyar. Mun rinjayar
da ruwayar ta tsakiya saboda ta fi kusa
da inganci. Amma cewa, ya a sannan
ya fara shiga shekara ta uku.. Ya za ayi
dan shekara biyu da watanni ya je
kiwo?. A samu karin bayani a Ar-
Raheeq Al-Makhtum, shafi na 68 da
Talqih Fuhum Ahl Al-Athar na Ibn Al-
Jauzee, shafi na 7.
Shekara biyu bayan haka, sai Amina ta
dauki yaronta domin ta sadar da
zumuncin sa da danginsa na Madina;
kawunnen mahaifin sa da zuri’ar su.
Bayan da suka kammala wannan
zumuncin ne a kan hanyar su ta
dawowa gida sai Allah ya karbi
baiwarsa a daidai kauyen da ake kira
Abwa’u mai nisan kilomita 180 daga
Madina. A can aka yi jana’izar ta. Ita
kuma Ummu Aimana ta dauko yaron
Sallallahu Alaihi Wasallam ta dawo da
shi Makka. (As-Siratun Nabawiyyah,
na Ibn Hisham (1/68).
Abdulmuttalib ya ji zafin mutuwar
mahaifiyar manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam matuka, kuma ya fito
fili ya bayyana ma sa haka. (Sahihus
Siratin Nabawiyyah, na Ibrahim Al
Ali, shafi na 56.)
Daga nan kuma ya ci gaba da kula da
jikansa har yana fifita shi a kan ‘ya’yan
cikin sa saboda tausayin sa. Shekaru
biyu kacal bayan haka shi ma ajalinsa
ya cim ma sa sai ya ce ga garinku. As-
Sirah An-Nabawiyyah na Ibn Hisham
(1/169).
Haka dai zamu ga manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam ya tashi a
cikin maraici saboda hikimar da
ubangiji gwanin sarki ya tanada ma sa
ta hanyar yin haka. Tarbiyyah da renon
ubangiji sun ishi manzonsa ba sai ya
bukaci wata kulawa daga mahaifa da
kakanni ba. Ashe ba haka annabi
Yusuf Alaihis salam ya tashi da farko a
gaban mahaifinsa ba – annabin Allah
Ya’qub Alaihis salam – a cikin gatanci
da ni’ima da kulawa? To, amma me ya
faru bayan haka? Sai madaukakin sarki
ya raba shi da shi, kaddara ta gargada
shi zuwa inda bai san kowa ba, kuma
ba wanda ya san shi, ya je ya fuskanci
kalubalen rayuwa iri-iri tun daga jefa
shi rijiya, zuwa sayar da shi a kasuwar
bayi, daga nan zuwa fitinar mata da
aukawa gidan kaso, sai kuma babbar
jarabawa ta samun mulki. Kai, a
takaice dai ko da mahaifinsa ya gan shi
– bayan sama da shekaru ashirin – ya ga
annabin Allah. A ina ya samu wannan
baiwa? Kuma wa ya yi tarbiyyar sa a
kan ta? Allah ne da kansa ya jibinci
wannan lamari kuma a kan haka ya
kakkabe hannun kowa daga gare shi.
Babu sauran wani ya yi tunanin cewa,
iyayensa ne suka horar da shi a kan
wannan da’awa da yake yi. Babban
darasin da ke cikin wannan shi ne,
kada mu dauka cewa, yi ma yaro gata
da sagarta shi shi ne abinda zai
daukaka shi ko ya sanya shi a matsayi
mai girma. Babu shakka idan iyaye
suka kula da tarbiyyar dansu, suka
koya ma sa ilimi da imani, sannan suka
hada da rokon Allah to, ana fatar Allah
ya shirya ma su shi.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories