Yadda zaka kare asusun ajiyar ka a banki daga ɓarayi

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Assalamu Alaikum!

Yau zan ɗanyi sharhi ne da kuma bada shawari kan yadda mutum zai kare Bank Account nashi daga masu satan kuɗi.

Da yawa mukan ji labarai na sace sace da akeyi wa mutane daga Bank Account nasu, wanda da yawa akanyi amfani ne da Nombobin jikin ATM card nasu domin sace kuɗin.

Wani lokaci koda mutum ya garzaya zuwa bankinsa bayan an sace masa kuɗi ba dole bane bankin su iya dawo masa da kuɗin. Shiyasa ya dace mu kasance masu lura matuƙa, domin shi addinin Muslunci yazo da kare abubuwa guda uku, daga cikinsu akwai dukiya. Kuma ba’a so musulmi ya zamto kidahumi. Ya kamata ya zamto mai kula da kuma lura da abubuwa dake gudana a gefensa.

duk da cewa tsarin da bankuna suka kawo na OTP ya taƙaita sace sacen matuƙa amma bashi yake nuna andaina baki ɗaya ba.

Shiyasa zan kawo muku wa’innan Hanyoyi da nasihohi da in aka bisu Insha’Allah Allah zai kiyaye.

Nasiha na farko: Kabuɗe Account biyu, Ɗaya na ajiye kuɗi mai yawa. Ɗaya kuma na siyayya online da kuma POS.

Da farko a lokacin da kaje buɗe Account na banki ajikin Form na buɗe account ɗin bankin sukan baka option na ko kanaso ka shiga tsarin sayen kaya online. Toh daga cikin shawari da zan bayar anan shine mutum in yaje buɗe account kada ya zaɓi wannan tsari a ainahin account nashi da zai rinƙa zuba kuɗi masu yawa, abin nufi anan shine mutum ya buɗe account biyu inhar yanaso ya rinƙa siyan abubuwa online. Ko kuma biyan Bills online, Sai ya zamto ainahin account nashi kada ya zaɓi wannan tsari, shi kuma ɗaya account ɗin da zai buɗe domin yin amfani dashi wurin sayayya online sai ya zaɓi wannan tsari akai. Ko kuma mutum zai iya buɗe account a wani banki na daban.

Kada dai ya zamto account ɗin da kake sanya kuɗi aciki da yawa shi zaka rinƙa amfani dashi wurin siyayya online, ko kuma wurin biyan Bills.

Haka nan shi wannan account ɗin da ka buɗe wanda bashi ne main account naka ba ya zamto shi zaka rinƙa amfani dashi wurin POS Transactions. Da siyayya a Shaguna, ko kuma Gidan mai. Haka zaiyi matuƙar taimakawa wurin kareka daga masu sata kuɗi a banki, ta yadda bazaka rinƙa barin kuɗaɗe masu yawa acikin wannan account ɗin ba. Ko kuma ya zamto kada ka saka kuɗi aciki har sai kana da buƙatar amfani dasu, sai kayi transfer daga main account naka zuwa ga shi wannan account ɗin. Toh kaga koda masu satar sun sami bayanan wannan ATM ɗin kuma sun sami nasarar kutse aciki ba zasu sami komai aciki ba, ko kuma abinda zasu samu aciki bashi da yawa.

Nasiha ta biyu:Ka sanya tsaro mai ƙarfi a wayarka.

Abu na biyu shine idan kana amfani da mobile Banking, ko kuma USSD Banking toh ka tabbata ka sanya tsaro a wayarka ta yadda babu wadda zai iya buɗe ta, kada ka faɗa wa wani password naka, sannan kada ka bari notification ya rinka bayyana bayan ka kulle wayarka, domin da haka ne za’a iya samun OTP Daga wayarka ba tare da an buɗe ta ba.

Ka tabbata wurin Sensitive notification yana off.
Zaka iya samun wannan settings ɗin acikin security settings na wayarka.

Nasiha ta uku: Ka saka pin a kan sim card naka.

Bayan ka sanya tsaro a kan wayarka abu na biyu shine sai kuma ka sanya tsaro akan sim naka. Domin da zarar ɓarawo ya sami damar sace sim naka zai iya ya sami otp ko kuma ya iya transferring kuɗi daga account naka in yasan Banking pin naka. Saboda haka yana da matuƙar mahimmanci ka kulle kan sim naka ta yadda koda ɓarawo ya sace babu abinda zai iya yi dashi.

Nasiha ta huɗu: Banki ba zasu taɓa kiranka ta waya su tambayeka OTP ko password ko kuma nomban jikin ATM naka ba.

Yana daga cikin hanyoyi da ɓarayi suke amfani dashi wurin sace kuɗaɗen mutane, sai su kirasu a waya su fara tambayansu bayanai akan account ɗinsu, su nuna musu cewa daga bankin da suke ajiya suke kiransu. Toh in wani ya kiraka yana maka irin wa’innan tambayoyi ka kashe wayarka kuma ka garzaya zuwa bankinka ko kuma ka kirasu domin yi musu bayani.

Nasiha ta biyar: Kada ka saka bayanan katin ATM naka a kowani irin shafi.

Ya kamata mutum ya kula matuƙa wurin saka bayanan katin ATM nasa a online. Kada ya saka wannan bayanai sai a shafi da ya yarda dasu. domin haka zai iya bada dama ɓarayi su saci bayanan katinsa na ATM. Sannan kuma koda shafin da ya yarda dasu ne ya tabbata akwai tsaro a shafin. Za’a iya gane haka idan shafin ya fara da https://.


Wannan sune shawarwari da zan bayar. Amma shawara ta farko tana da mahimmanci sosai, domin naga amfaninta matuƙa domin wani abu da ya faru dani. Kwanakin baya na taɓa yin subscription na wani service online, na biya na shekara ɗaya, ashe a lokacin da nayi wannan subscription na zaɓi a rinƙa sabunta shi ko wani shekara, amma ni ban sani ba. Kuma ni a yanayin tsari na wannan ATM ɗin bana saka kuɗi aciki sai idan zanyi amfani dashi a lokacin. Shekara ta juyo ni har na mance domin na daina amfani da service ɗin, sai sukayi ƙoƙarin sabunta subscription ɗina, sai babu kuɗi a account ɗin, sai suka turomin saƙo ta email cewa Sabunta wannan subscription ɗin yaci tira sabida Rashin kuɗi a cikin katin ATM ɗina. Daga nan ne ma na tuna, sai na shiga nayi cancel ɗin subscription ɗin. To kaga da akwai kuɗi acikin ATM da kawai sai dai naga an turomin saƙo cewa an cire kuɗin.

Allah yasa mudace. Kuma ya daɗa karemu. Ameen.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

3 responses to “Yadda zaka kare asusun ajiyar ka a banki daga ɓarayi”
  1. Ishaq Avatar
    Ishaq

    Masha Allah wannan wayar da kai Abu ne mai muhimmanci, sai Karin shawara akan sanya security wato pin akan simcard bayan na waya domin sau da dama idan suka dauki wayar mutum da zaran sun cire simcard suka sa awani wayar yakan zamo musu sauki wajen shiga account din mutum idan har bai sa pin ba idan kuma da pin to da wahalar gaske ayi mai sata da sim din shi

    1. Nibras Avatar

      Muna godiya da wannan tunanarwa. Insha’Allah zamu saka shi.

  2. […] baya nayi wani rubutu mai taken: Yadda zaka kare asusun ajiyar ka a banki daga ɓarayi wanda na bada wasu shawarwari acikin rubutun ta yadda Mutum zai kare asusun bankin sa daga ƴan […]

Leave a Reply

Latest updates
Categories