Matakan Kariya daga Masu damfara ta Internet

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Wa Barakaatuh.

Kwanakin baya nayi wani rubutu mai taken: Yadda zaka kare asusun ajiyar ka a banki daga ɓarayi wanda na bada wasu shawarwari acikin rubutun ta yadda Mutum zai kare asusun bankin sa daga ƴan damfara.

Wannan rubutun ɗoriya ne akan wannan da ya gabata, da ƙarin wasu shawarwarin, ga wanda bai karanta wannan rubutun da ya gaba ta ba sai ya sake dubawa ga Link ɗin a sama.

Mu sani cewa Shi Addinin Musulunci yazo da kare wasu abubuwa masu mahimmanci guda biyar.

  • Addini
  • Rai
  • Hankali
  • Mutunci
  • Dukiya

duka wa’innan abubuwa guda biyar da na lissafa Musulunci yazo da kare su. Saboda Haka baya halatta ga Musulmi yayi wasa wurin kiyaye su.

Saboda haka Maudu’in mu na yau ya shafi kare dukiya ne.

Kullum ana faɗakarwa amma haryanzu mutane suna faɗawa tarkon wa’innan ƴan damfara ba dare ba rana, shiyasa naga dole in sake yin rubutu kan wannan lamari.

Ga matakan kariyar kamar haka.

Kiyaye Bayanan banki: da farko dai mu sani cewa masu satan kuɗi a banki bazai yiwu su saci kuɗinka ba tare da suna da Bayananka ba, ma’ana yana da kamar wuya su zauna a wani wuri kawai su sace maka kuɗi ba tare da suna da Bayananka na banki da na Sirri ba. Saboda haka dole ka kare bayanan bankinka kada ka baiwa kowa sai wadda ka yarda dashi ɗari bisa ɗari, kama daga BVN naka ko NIN nombanka, hatta account nombanka kada ka yaɗa shi ba tare da wani dalili ba. Haka nan nombobin jikin ATM naka kada ka yadda ka bawa wani, ka kuma ɓoye ATM ɗin yadda babu wani wanda zai samu ikon Saka hannu akai.

Banki ba zasu taɓa kiranka ta waya su tambayeka OTP ko password ko kuma nomban jikin ATM naka ba: Na rubuta wannan a rubutu na da ya gabata amma saboda Mahimmancinsa zan sake kawo shi anan. Mu sani cewa banki bazasu taɓa kiranka su tambayeka wa’innan bayanan ba, Duk wanda kaji ya kiraka yana tambayarka wa’innan bayanan to ka kashe wayarka ka tuntuɓi bankinka, ko ka garzaya zuwa bankin ka sanar dasu halin da ake ciki. Koda ko ranar da ka buɗe account ɗin ne suka kiraka suke Tambayarka suke ce maka zasu kammala cike bayananka, kada ka saurare su.

Ka kare wayarka da Sim naka: Ka sanya tsaro a wayarka mai ƙarfi ta yadda babu wanda zai iya buɗe wa sai wanda ka faɗa masa password ɗin. Hakan na nufin ka guji amfani da password mai sauƙi kamar 12345, ko 00000, ko 11111, ko 11223344 da makamantansu. Domin za’a iya cankar password ɗin. Haka nan Sim naka da kake amfani dashi a banki ka sanya masa pin ka kulle shi, ta yadda koda an saci wayarka bazasu iya buɗe shi ba.

Da zarar wayarka ta ɓace kayi gaggawar sanar da bankin ka domin su kulle account naka: idan aka samu akasi wayar ka ta faɗi to kayi gaggawar sanar da bankin ka halin da ake ciki domin su dakatar da account ɗin. Kowani banki nada irin nashi code da za’ayi amfani dashi wurin dakatar da account yayin ɓatar waya, zaka iya bincika na bankin ka domin shirin ko ta kwana.

Mu guje wa Kwaɗayi: Wataƙila wani yayi mamaki meye ya kawo ƙwaɗayi cikin matakan kariya daga masu damfara ta Internet. Ƙwarai wasu ƙwaɗayinsu take kaisu ta barosu, basu san mutum ba, zai tuntuɓesu yace musu yana da wata harkar kasuwanci da zasu saka 100,000 misali acikin kwana ɗaya ko sati zasu sami ninkin kuɗinsu, ko kuma yace musu sunci wata gasa amma sai sun tura da wani kuɗi kafin a turo musu abinda suka ci alhali su sunsan basu yi wata gasa ba. To irin wa’innan abubuwa da kwaɗayi yakan sa mutane su faɗa tarkon masu damfara ta Internet. Sai su tura musu kuɗi daga baya suzo suna nadama.

Wannan kuskure ne babba. Kada ka yadda ka tura wa wani wanda baka sanshi ba kuɗi don yin kasuwanci ko wani abu. Ka nemi yazo ku haɗu in kaga kana da buƙatar wannan kasuwancin da ya tallata maka. Haka nan in yace kaci wata gasa ce to ka nemi ku haɗu ko ya turo maka kyautar kafin ka tura masa abinda yake nema ka tura, da haka ne zaka kore masu damfara.

Idan kuma aka damfare ka ya zakayi? Allah ya kiyaye idan kuma ka riga ka faɗa tarko yaya zakayi? Akwai hanyoyi da zakabi wurin rage ɓarnar, ko kuma in Allah ya taimaka zaka iya dawowa da kuɗaɗenka.

Idan Zare kuɗin akayi ba kai ka tura ba: kayi gaggawa ka kira bankinka su dakatar da account naka, sannan sai ka garzaya bankin kaje kace kana neman Sashin masu kula da damfara ta bankin, sai ka faɗa musu halin da ake ciki. Bayan sun ɗauki bayanan ka sai ka sake rubuta email ka tura wa cbn ta wannan email ɗin. [email protected]. ka tura musu da duk bayanan da kake dashi. In Allah ya taimaka za’a iya dawo maka da kuɗinka.

Idan kai ka tura kuɗin: Shima zaka je bankin ka nemi sashin masu kula da damfara sai ka faɗa musu halin da ake ciki, sannan sai ka tuntuɓi cbn ta wannan emai ɗin [email protected] ka tura musu receipt na kuɗin da ka tura, sannan da duk wani bayani da zai taimaka, Da nomban mai damfarar da account ɗin da ka tura, shima in kaci sa’a za’a iya dawo maka da kuɗinka.

Wannan sune ɗan ƙarin bayani da zanyi kan rubutun da ya gabata. Allah ya ɗaɗa karemu baki ɗaya.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories