Hatsarin Mace Musulma ta rinƙa sanya hotunan ta a Social media

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Allah ya kawo mu wani zamani mai cike da hatsari, wanda ansamu cigaba ta fanni danan daban, daga cikin babban cigaba da aka samu shine fitowar shafin yanar gizo da kuma sauƙin isa zuwa gareshi ga mutane. Wannan yasanya mutane sun ruɗe, sun mance da cewa duk abinda sukeyi komi ƙanƙancinsa Allah zaiyi musu hisabi akai.

Wasu sun ɗauki wannan kafa dama garesu ta yaɗa alheri wa al’umma, Wurin yaɗa ilimi da Al’ummah zata amfana dashi Madalla da wa’innan.

Wasu kuma sun ɗaukeshi a matsayin wata kafa ta yaɗa fasadi aban ƙasa. Kuma babban hatsarin shine duk abinda ka ɗaura a irin wa’innan kafafe ya yaɗu kenan har abada, domin ko ka share shi wani ya riga ya same shi, haka nan shima kuma zai cigaba da yaɗa wa, hakanan abin zaici gaba da tafiya, kuma duk wani sharri da fasadi da ka yaɗa wani ya gani ya yaɗa kana da zunubi akansa, in mutane dubu ne suka yaɗashi toh kaima kana da kwatankwacin zunubansu, haka wannan laifi zaiyi ta binka har zuwa ƙabari har zuwa ranar tashin Al Qiyama, gwargwadon wa’inda suka yaɗa gwargwadon laifinka.

Ashe mutum mai hankali ya dace ya rinƙa taka tsantsan wurin abubuwa da zai rinƙa yaɗa wa a wa’innan Kafafe.

Yana daga cikin abin baƙin ciki da tashin hankali yadda mata Musulmai suka ɗauki wannan kafa ta internet ta zamto musu kafa ce ta yaɗa hotunansu, sai suyi ado, a wasu lokuta ma suyi shiga wacce bata dace ba, su yaɗa ta a irin wa’innan kafafe, mutane miliyoyi su gani. Ba kuma komi yake sanya su yin haka ba sai don neman likes da comments, wanda da yawa masu yi musu comments ɗin ba gaskiya suke faɗi ba kuma suma sun san haka amma duk da haka baisa sun daina ba.

Yake ƴar’uwa kisani wannan yaɗa hotuna taki da kikeyi a kafar internet ba komi yake janyo miki ba sai fushin Allah da kuma zubda mutunci, domin Allah ya haramta wa mace ta nuna adonta ga wani wanda ba maharraminta ba, haka nan kuma sanya hotunanki da kikeyi ko kike tura wa wasu mazaje suna gani suna jin daɗi wannan yana daga cikin zinar ido wanda Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yace

Ido ma yana zina, zinar ido shine kallo

Muslim: 2657

A lokacin da kika sanya wannan hotuna naki wani ya gani yaji daɗi toh yayi zinar ido, yana da zunubi, kuma kema kina dashi.

Shin kinsan mutane nawa hotunanki zasu isa zuwa garesu?

Shin kinsan mutane nawa zasu yaɗa wannan hotunan?

Shin kinsan mutane nawa a dalilin wannan hoto naki zasu aikata abinda bai dace ba?

Kina ga zaki iya ɗaukar duka wannan laifuffukan?

Shin kina da yaƙini ba za’a cigaba da yaɗa wannan hotunan ba har bayan mutuwar ki a cigaba da miki azaba a ƙabari sabida shi?

Ya kamata kiyi karatun ta natsu ya ƴar’uwa. Ba waye wa bace wannan!

Kuma ki sani duk wani mutum mai mutunci bazaiso ya auri mace mai tallata kanta a kafafen sada zumunta ba.

Ki tuba ki koma zuwa ga Allah. Allah mai yawan gafara ne kuma mai jin ƙai. Allah yasa mudace

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories