Corona virus da komawa zuwa ga Allah

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Bayan ɓullar wannan cuta mai kisa wacce aka mata laƙabi da Corona Virus da yawa daga cikin mutane sun ruɗe, wasu suna ta yaɗa labaran ƙarya kan wannan cuta. Wasu sun kiɗime har sun mance da Allah.

To haƙiƙa duk wani Musulmi ya sani cewa irin wannan jarabawar zata zo cikin ko wani lokaci, Allah kan iya jarrabar bayinsa ko dun laifin da sukayi masa domin su dawo su gyara, ko kuma dai don wata hikima tashi.

A irin wannan lokaci da aka samu irin wannan jarabawa abinda ya dace Musulmi yayi shine: ya amshi wannan jarabawa da hanu biyu, ya kuma duba ayyukansa, ya kuma yi ƙoƙarinsa wurin komawa zuwa ga Allah da neman kariya.

Allah maɗaukakin sarki yace cikin surat Aal emran aya ta 42-43:

ولقد أرسلنا إلى أمم من قبلك فأخذناهم بالبأساء والضراء لعلهم يتضرعون

فلولا إذ جاءهم بأسنا تضرعوا ولكن قست قلوبهم وزين لهم الشيطان ما كانوا يعملون

Haƙiƙa mun aika annabawanmu zuwa ga Al’ummomi kafin zuwan ka Ya Muhammad, sai suka kafirce mana, sai muka kama su da talauci, da cututtuka domin ko zasuyi ƙanƙan da kai su dawo zuwa ga Allah.

Da ace lokacin da azaba ta tazo musu sunyi ƙanƙan da kai sun koma zuwa ga Allah da yafi musu, amma sai zuƙatansu suka ƙeƙashe, shaidan ya zayyana musu abubuwan da suke aikata wa, suna ganinsa da kyau.

wannan yake nuna abinda ya dace Musulmi suyi a irin wannan hali na jarabawa shine:

  • Su amshi wannan jarabawar
  • Su koma zuwa ga Allah su nemi agajinsa, kada su dogara da ƙarfinsu kaɗai.
  • Su cigaba da ƙoƙarin amfani da hanyoyin kariya daga wannan cuta.
  • Sannan su cigaba da neman hanyoyin magance shi.
  • Su guji yaɗa labaran ƙarya

Allah yasa mudace, Allah kuma ya kare mu baki ɗaya.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories