Ladduban Shiga Gida(Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

ALLAH (SWT) YACE: “HARAMUN
NE KA SHIGAR WA IYAYEN KA,
KO MUHARRAMANKA BA TARE
DA YI MUSU SALLAMA BA”
HATTA IYALANKA BA ZA KA
SHIGA GARE SU BA SAI DA
SALLAMA.
(Q: NUR 59.)
“Ya ku wadanda sukayi imani!
Wadannan da hannuwanku na
dama suka mallaka da wadanda
basu isa mafarki ba daga cikin ku,
su nemi izini sau uku, daga
gabannin Sallar alfijir, da lokacin
da kuke ajiye tufafin ku, saboda
zafin rana, kuma daga bayan
Sallar Isha’i. Su ne al’aurori uku a
gare ku, babu laifi a kanku kuma
babu a kansu a bayan su. Su masu
kewaya ne a kanku, sashen ku
akan sashe.” (Surutun Nur, aya ta
58)
A takaice ladubban shiga gida
sune, dukkan yaron da ya balaga
dane ko bawa, kada ya shiga gida
ko dakin mahaifin sa ko uban
gidan sa a a bayan sallama, har
sai in an amsa da ya shigo, in ance
ya koma, ya koma. In kuma yana
zaton ko ba’a ji bane, to ya
maimaita sau uku. Neman izini
wajibi ne ga yayanka baligai a
lokutan nan uku, kamar yadda
yazo a aya ta 59, daga gabanin
sallar Alfijir, lokacin tsakar rana,
wato lokacin da ake ajiye tufafi
saboda zafin rana da kuma bayan
sallar isha’i.
Wannan aya ta wajabta mana,
musamman mata da su koyawa
yayansu da kanne ko yan uwa
dake zaune a gida tare da su da
masu aiki, da su dauki tarbiyya irin
wadda Al’qur’ani mai girma yazo
da ita, da kuma sunnar manzon
Allah tsira aminci su tabbata a gare
shi. Halayyar mu ce a yanzu da aje
wa mutum ziyara a ko wane lokaci,
ko kuma a banka kai cikin daki
babu sallama , in ba a amsa ba,
sai mutum ya tafi yana fushi, yana
kunkuni wai anyi masa wulakanci.
Ya ‘yan uwa Musulmi, mu ji tsoron
fushin Ubangiji bana mutum ba,
fushin Mutum ko zagin sa, bazai
cutar da kai da komi ba. Yayin da
ka bi dokar Ubangiji, to zakayi
rayuwar ka cikin kwanciya hankali
babu kunci. Sannan ina Nasiha ga
yan uwa maza da su daina zuwa
gidajen abokai a lokutan Da Allah
ya hana.
“Babu laifi a gare ku da kuci
abincin juna, ko ‘dai ‘dai, ko a
kwano daya, a gidajen kawunan
ku, ‘yan uwanku har da abokan ku,
amma in anci a tashi, kada a tsaya
hira, kuma kada aje kafin lokacin
da aka gayyace ka, ka zauna har
sai an gama abincin, wannan baya
halatta, yayin da muka bi dokar
Allah, to baza mu sami kuntata a
kanmu ba, insha Allah. Yana daga
dabi’un mu a yanzu a ki watsewa
bayan gayyata, ko bayan aboki
yaci abinci, sai ya tsaya hira, har
masu gida su kosa.
Bahaushe yace, wai bayan ci zama
tsegumi, tafiya rashin kunya, to
umurnin Allah zaka bi ko son rai?
Shima bahaushen ai cewa yayi
zama tsegumi, wanda yake
haramun ne, cewa kuma tafiya
rashin kunya, shima kuskure ne,
domin yaci karo da umurnin Allah.
Allah ya samu a bisa hanya
madaidaiciya, ya nuna mana
gaskiya gaskiya ce ya bamu ikon
binta, ya nuna mana karya karya
ce ya bamu ikon guje mata.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

4 responses to “Ladduban Shiga Gida(Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe)”
  1. Haruna Idris Sufyan Avatar
    Haruna Idris Sufyan

    ameen thumma ameen

  2. ALLAH YA SAKA DA ALHAIRI

  3. umar Abdurrahhman Avatar

    yes

  4. Umar Avatar

    Allah saka

Leave a Reply

Latest updates
Categories