Mas'alolin aure Fitowa ta 20(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Bayani ya gabata akan Sharuddan
daura aure wadanda sun hada da
waliyyi da sadaki, amma mun
amsa tambayoyi biyu dangane da
waliyyi, a yau kuma za mu amsa
tambayoyi biyu akan sadaki.
TAMBAYA:
Shin za a iya daura aure ba tare da
an ambaci sadaki ba?
AMSA:
Na`am! Za a iya daura aure ba tare
da an bayar ko an ambaci sadaki
ba yayin daurin auren, matukar an
yi alkawarin bayarwa a wani lokaci
na gaba. Wannan shi ne auren da
malamai suke kira:
ﻧﻜﺎﺡ ﺍﻟﺘﻔﻮﻳﺾ .
Malamai suna kafa hujja da ayar
da take bayani karara a kan
wannan auren, wurin da Ubangiji
subhanahu wa ta’ala ya fada cewa:
ﻟﺎ ﺟﻨﺎﺡ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﺇﻥ ﻃﻠﻘﺘﻢ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ ﻣﺎ ﻟﻢ ﺗﻤﺴﻮﻫﻦ ﺃﻭ
ﺗﻔﺮﺿﻮﺍ ﻟﻬﻦ ﻓﺮﻳﻀﺔ… ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ236 :
Ma`ana:
Babu laifi a gare ku, idan kuka saki
matan da ba ku sadu da su ba, ko
kuma ba ku yanka musu sadaki
ba…
Abin da za a iya fahimta daga ayar
shi ne, nunin da ta yi cewa an yi
aure har an kai ga saki amma ba
tare da an ambaci sadaki ko an
bayar da shi ba, alhali saki yana
tabbata ne bayan an daura aure.
Sannan kuma sun kafa hujja da
auren Sayyadina Aliyu
radhiyallahu anhu da Nana
Fadima ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ . Domin sai
bayan da aka daura auren
Sayyadina Aliyu radhiyallahu anhu
ya nemi tarewa da ita ne, sai
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya ce da shi:
…« ﺃﻋﻄﻬﺎ ﺷﻴﺌﺎ .« ﻗﺎﻝ ﻣﺎ ﻋﻨﺪﻯ ﺷﻰﺀ. ﻗﺎﻝ »
ﺃﻳﻦ ﺩﺭﻋﻚ ﺍﻟﺤﻄﻤﻴﺔ ».
Ma’ana:
… Ka ba ta wani abu! Sai
Sayyadina Aliyu radhiyallahu anhu
ya ce: Ba ni da wani abu (da zan
ba ta). Sai ya ce masa: Ina
sulkenka Hudamiyya? (Sai
Sayyadina Aliyu radhiyallahu anhu
ya ce: Yana wurina. Sai Manzon
Allah sallallahu alaihi wa sallama
ya ce masa: Ka ba ta shi).
Saboda haka ya halatta a daurawa
mutum aure ya yi alkawarin bayar
da sadaki a wani lokaci sananne,
matukar babu yaudara a ciki. Idan
kuwa matar ta gane cewa mijin
yana so ya ha`ince ta, to, tana da
damar ta ki mika kanta gare shi ko
ta kai shi kara.
A nan muke nasiha ga al`umma,
tunda yanzu al`amarin aure ya
zama mawuyaci saboda wahalar
rayuwa, za a iya daura aure tare
da jinkirta sadaki, amma bisa
amana kuma a gaban shaidu. Idan
mai albashi ne, a jinkirta masa har
sai ya karbi albashinsa. Idan kuwa
manomi ne, sai bayan an yi girbi ya
sayar da amfanin gonarsa.
TAMBAYA:
Shin Shari’a ta kayyade sadaki?
AMSA:
A’a! Shari’a ba ta kayyade yawa ko
karancin sadaki ba. Ya danganta
ne kawai ga mai bayarwa. Mai hali
zai bayar daidai gwargwadon
halinsa, haka kuma marar wadata
ya bayar daidai iyawarsa. An fi so
dai ya zama tsaka-tsaki. Babban
malamin nan Ibnul Kayyim bayan
ya tattara hadisan da suka yi
magana a kan sadaki ya fada
cewa:
Tsawwala sadaki abu ne makaruhi.
Domin Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama ya daurawa wani
sahabi aure bisa sharadin abin da
sahabin ya haddace na Alkur’ani
ya zama sadakin auren. Haka
kuma Ummu Sulaim radhiyallahu
anha ta auri Abu Dalha
radhiyallahu anhu da sharadin zai
shiga musulunci (a matsayin
sadakinta). Kuma Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ya
cewa wani sahabi, ya kawo ko da
zobe ne a matsayin sadakin aure.
Haka kuma hadisi ya tabbata cewa
yayin da aka daura auren Nana
Fadima ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ, Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ya
cewa Sayyadina Aliyu radhiyallahu
anhu:
« ﺃﻋﻄﻬﺎ ﺷﻴﺌﺎ .« ﻗﺎﻝ ﻣﺎ ﻋﻨﺪﻯ ﺷﻰﺀ. ﻗﺎﻝ » ﺃﻳﻦ
ﺩﺭﻋﻚ ﺍﻟﺤﻄﻤﻴﺔ ».
Ma’ana:
Ka ba ta wani abu! Sai Sayyadina
Aliyu radhiyallahu anhu ya ce: Ba
ni da wani abu (wanda zan ba ta).
Sai Manzon Allah sallallahu alaihi
wa sallama ya ce masa: Ina
sulkenka Hudamiyyah? (Sai
Sayyadina Aliyu radhiyallahu anhu
ya ce: Yana wurina. Sai ya ce
masa: Ka ba ta shi).
Kuma wani hadisin ya tabbata
daga Nana A’isha ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ta ce:
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya ce da ni:
ﻣﻦ ﻳﻤﻦ ﺍﻟﻤﺮﺃﺓ ﺗﺴﻬﻴﻞ ﺃﻣﺮﻫﺎ ﻭﻗﻠﺔ ﺻﺪﺍﻗﻬﺎ
Ma’ana:
Yana daga cikin alherin da ake
samu daga mace, dukkan
al’amarinta ya zama mai sauki ne
kuma sadakinta ya zama mai
sauki.
Sai Urwatu Ibn Zubair wanda ya
rawaito hadisin daga Nana Ai’shah
ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ya ce:
ﻭﺃﻧﺎ ﺃﻗﻮﻝ ﻣﻦ ﻋﻨﺪﻱ : ﻣﻦ ﺃﻭﻝ ﺷﺆﻣﻬﺎ ﺃﻥ ﻳﻜﺜﺮ
ﺻﺪﺍﻗﻬﺎ
Ma’ana:
Ni kuma ina fada daga gare ni
cewa: Yana daga shu’umancin
mace;( al’amarinta ya zama
mawuyaci) yayin da aka tsawwala
a sadakinta.
Kuma hadisi ya tabbata daga
UKbatu Ibn Amir radhiyallahu anhu
ya ce: Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama ya ce:
ﺧﻴﺮ ﺍﻟﻨﻜﺎﺡ ﺍﻳﺴﺮﻩ
Ma’ana:
Fiyayyen aure shi ne wanda aka
saukaka wajen yinsa.
A nan muke nasiha ga ‘yan uwa
wadanda suka ba da sadaki
gwargwadon ikon su da su yi
hakuri da abin da amarya za ta zo
da shi. Ko da babu gado da katifa
ko kayan jere. Kuma ya kamata a
fahimci cewa duk hadisan da muka
kawo, babu wurin da Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ya
kallafawa iyaye da su yi abin da ba
za su iya ba. Amma a yanzu sai ka
ga ana yi wa wasu amare gori
yayin da ba su zo da wasu kayan a
zo a gani ba. Wanda hakan, yakan
kai su ga rashin samun nutsuwar
aure da zaman lafiya, wani lokacin
ma har ya kai ga mutuwar auren.
Wannan kuwa kuskure ne, saboda
haka ya kamata a kiyaye.
Allah ya yi mana jagora.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories