ALHAJRUL-ASWAD(Mal.Aminu Ibrahim Daurawa)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Hadisi ya tabbata cewa wannan
dutse daga cikin Aljannah yake,
kuma lokacin da aka saukar dashi
fari ne, kal, yawan sabon mutane
yasa ya zama, baki, wannan dutse,
yasha gwagwarmaya iri-iri, a
tsawon tarihi, lokacin da
kuraishawa zasu sabinta ginin
kaabah, lokacin Manzon Allah saw,
yana da shekara talatin da bakwai,
sunyi sabani, gamai da wanda zai
dora wannan dutse. karshe, suka
amince sa cewa, duk wanda ya
fara shigowa, shine zaiyi hukunci,
kuma zasu yarda da hukuncinsa,
sai Manzon Allah saw ya fara
shigowa, kuma dukkansu, sukayi
farin ciki, da zuwansa, saboda sun
sanshi, da gaskiya, da Amana, da
Adalci, sai ya nemi, su nada
wakilai daga ko wacce kabila, ya
shinfida, mayafinsa, ya dora
dutsan akai, yace ko wane wakili
ya kama gefe, daya, su daga tare,
sukai wajan, shi kuma ya daidaita
shi, ,
Manzon Allah saw yace, wannan
dutsan zaizo ranar a
kiyama da ido da harshe zaiyi
sheda ga duk ya sunbace shi,
wannan dutse yana da sunnoni
guda biyar :
1- Ashafe shi da hannu, ya
sunbace shi, yayi kabbara
2-Idan ba hali sai ya tabashi, ya
sunbaci hannunsa
3- Idan ba hali, sai ya tabashi da
sandarsa sai ya sunbaci inda ya taba
da sandar.
4- Idan haka bata samu ba, sai ya
nuna shi da hannu, yayi kabbara,
ba tare da ya saunbaci hannunba.
5- Idan babu cunkoso, yana iya yin
sujjada akansa.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories