JIFAN SHEDAN DA TARIHINSA(Mal.Aminu Ibrahim Daurawa)

Danna nan domin shiga karatu Online

1- Ya tabbata a tarihi wanda ya
fara jifan shedan shine, Annabi
Ibrahim saw, lokacin da Allah taala,
ya umarceshi,a mafarki, ya yanka
dansa, sunzo bayan gari, a mina
shine shedan, ya biyoshi, yana
gaya masa cewa wannan mafarki
ba gaskiya bane, shine Annabi
Ibrahim as, ya jefeshi, da duwatsu
bakwai, har sai da kafafunsa suka
nutse a kasa, ya kara biyoshi, ya
kara jifansa da duwatsu bakwai
har sai da kafafunsa suka kafe a
cikin kasa, ya kara biyoshi, Annabi
Ibrahim ya kara jifansa, da
duwatsu bakwai har sai da ya kafe
a cikin kasa, Sai Abdullah Dan
Abbas yace: Shedan kuke jifa,
Kuma addinin Babanku kuke bi.
( Sahuhut-targib wat-tarhib)
2- Jifan shedan wajibi ne daga
cikin wajibobin hajji,
3- Kwanakin jifa hudu ne, Ranar
goma ga wata, a jefi babbar Jamra
kawai da duwatsu bakwai,
4- ranar sha daya, da sha biyu, ,da
sha uku, zaa jefi Jamra uku, Babba
data tsakiya da karama, kowacce
duwatsu bakwai- bakwai, ga
wanda ya cika kwanakin jifa, zai
jefa tsakuwa sabain (70)
5- ko wadanne Alhazai miliyon
daya zasu jefa miliyan sabain, idan
Alhazai sun kai miliyon uku, zaa
jefi shedan da tsakuwa miliyon dari
biyu da goma, kuma kowacce sai
anyi kabbara.
6- Jifa koyine da Annanbi Ibrahim
as
7- Jifa Tabbatar da ambaton Allah
ne, saboda kabbara da akeyi ga ko
wanne dutse
8-Jifa koyawa mutane biyyaya ne,
akan wani adadi.
9- Jifa bin umarnin ne,
10- Jifa Koyawamusulmi tsari ne,
11- Jifa Bayyarnar da gaba ne da
shedan
12- Jifa dole ya zama da dutse
kuma karami kamar girman gujjiya
13- Jifa Dole ayi kabbara ga ko
wanne dutse
14- Jifa dole ya fada cikin wannan
ramin idan ana kwakwanto sai a
sake.
15- Jifa dole ayi daya bayan daya
baa jefawa duka a lokaci daya .
16- Jifa dele ya zama a fara a jere,
daga karama zuwa ta tsakiya zuwa
babba, tsakanin ta daya data biyu
a tsaya ayi addu’a ta karshe a
wuce babu tsayawa.
17- Lokacin jifan shedan yana
farawa ranar farko daga rabin dare
zuwa washe garin ranr goma ga
wata zuwa, har zuwa dare na
wannan rana.
18- Ragowar kwana uku na jifa ko
wanne yana farawa daga Zawali
Wato lokacin azahar zuwa faduwar
rana har zuwa dare ga wanda ya
makara.
19- Wanda bazai iya jifa ba
saboda tsufa ko yarinta ko rashin
lafiya , yasa wani yayi masa babu
laifi.
20- Ba gaskiya bane masu cewa
idan ka jefi shedan zai rama, ko
abin da yayi kama da haka, Allah
yasa hajjin mu karbabbiya ce,
Allah ya samu cikin ceton Annabi
saw ya shayar damu ruwan
kausara, yasa mu cika da imani
Amin.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates