KIRA GA 'YAN TIJJANIYYA DASU DAWO SU KAMA AQEEDA INGATACCE(Dr Ibrahim Jalo Jalingo)

·

·

YA KAMATA A SAKE DUBA IRIN
AQIIDUN DA KE CIKIN DARIKUN
SUFAYE
11/4/1434 H 22/2/2013 M
{ﻭﻣﺎ ﺍﺭﻳﺪ ﺍﻥ ﺃﺧﺎﻟﻔﻜﻢ ﺍﻟﻰ ﻣﺎ ﺃﻧﻬﺎﻛﻢ ﻋﻨﻪ ﺍﻥ ﺍﺭﻳﺪ
ﺍﻻ ﺍﻻﺻﻼﺡ ﻣﺎ ﺍﺳﺘﻄﻌﺖ ﻭﻣﺎ ﺗﻮﻓﻴﻘﻲ ﺍﻻ ﺑﺎﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﺗﻮﻛﻠﺖ ﻭﺍﻟﻴﻪ ﺃﻧﻴﺐ.{ ﻫﻮﺩ: ٨٨ .
A kwanakin baya ne muka yi
rubutu a cikin Facebook muna
masu jinjina wa sheik Abduljabbar
a kan matakin da ya dauka na
inkarin munkarin da wasu muridan
Darikar Tijjaniyyah suka bayyana a
fili ta yadda kowa da kowa ma zai
iya fahimtar irin kafircin da yake
cikin abin da suka fada.
To amma a wancan lokacin ni na
ce hakan bai isa ba, saboda ya
kamata a ce shi Sheik Abduljabbar
ya kara matsawa gaba ta yadda
zai dubi dukkan aqiidun da aka
gina Darikun Sufaye baga dayansu
a kansu, sannan ya yi
muqaaranarsu da abin da Shari’ar
Musulunci mai haske ta zo da shi.
Lalle, na fadi hakan ne saboda irin
abin da ni na sani game da
wadannan darikun.
Misali: Dukkan ‘Yan Darikar
Tijjaniyyah sun yadda da cewa
Sheik Ibrahim Khaulaha Shi
Gauthu ne! Abin da kuwa suke nufi
da Gauthu shi ne: Mai yin abin da
yake so cikin duniyan nan, Wanda
kome ke fitowa daga gare shi!!
Yana rubuce cikin littattafansu
magana kamar haka:-
ﻓﺎﻟﻐﻮﺙ ﻫﻮ ﺍﻟﻔﺮﺩ ﺍﻟﻮﺣﻴﺪ ﺍﻟﺬﻱ ﻳﺘﺼﺮﻑ ﻓﻲ ﺍﻟﻌﺎﻟﻢ
ﻓﻼ ﻳﺤﺪﺙ ﻓﻲ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﻜﻮﻥ ﻣﻦ ﺍﻣﺮ ﺍﻻ ﺑﻌﺪ ﺍﺫﻧﻪ .
ﻭﺗﺤﺖ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﻐﻮﺙ ﺑﺪﺭﺟﺔ ﻭﺍﺣﺪﺓ ﺍﻷﻗﻄﺎﺏ ﺍﻻﺭﺑﻌﺔ
ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻳﻤﺴﻜﻮﻥ ﺟﻬﺎﺕ ﺍﻻﺭﺽ ﻭﺗﺤﺘﻬﻢ ﺍﻷﻭﺗﺎﺩ
ﺍﻟﺴﺒﻌﺔ ﻭﻫﻢ ﻳﻤﺴﻜﻮﻥ ﺑﺎﻷﻗﺎﻟﻴﻢ ﺍﻟﺴﺒﻌﺔ ﻭﺗﺤﺘﻬﻢ
ﺍﻷﺑﺪﺍﻝ ﺍﻷﺭﺑﻌﻮﻥ !!
Ma’ana: Gauthu shi ne makadaicin
nan guda daya wanda yake yin
abin da ya ga dama, babu wani
lamari da yake faruwa a cikin
wannan Duniya sai bayan
yardarsa. Sannan a karkashin
Gauthu da daraja guda akwai
Qudubannan guda hudu wadanda
suke rike da bangarorin Duniya.
Sannan su ma a karkashinsu
akwai Autaadannan guda bakwai
wadanda suke rike da
yankunannan guda bakwai na
Duniya. Sannan su ma a
karkashinsu akwai Abdaalannan
guda arba’in!!!
Ke nan daga wannan maganar ce
za mu fahimci cewa lazimin duk
wanda ya yadda da cewa Shehu
Ibrahami Khaulaha Gauthu ne, to
kuwa dole ne ya yadda da cewa
shi Shehu Ibrahim Khaulaha shi ne
mai yin abin da ya ga dama cikin
wannan Duniya tamu, shi ne mai
rayawa, shi ne mai kashewa, shi
ne Mai azurtawa, shi ne mai
tsiyatarwa, shi ne kome, shi ne, shi
ne….
Saboda haka masu wannan waka
ta Ibrahim Khaulaha babu wani
abu sabo da suka fada game da
abin da yake nade cikin aqiidar
Tijjaniyyah, domin da ma wannan
shi ne abin da yake rubuce kuma
shi ne imanin dukkan ‘yan
Tijjaniyyah!!
Muna fata maluman Tijjaniyyah a
duk inda suke za su kara tunani
sosai, sannan su sa tsoron Allah
cikin zuciyarsu, su yi watsi da
wannan aqiidah ta Tijjaniyyah, su
komo su rika yin Musuluncinsu
kamar yadda Annabi mai tsira da
amincin Allah tare da Sahabbansa
suka yi. Allah ya taimake mu.
Ameen.

26 responses to “KIRA GA 'YAN TIJJANIYYA DASU DAWO SU KAMA AQEEDA INGATACCE(Dr Ibrahim Jalo Jalingo)”
 1. ILIYASU IBN ALIYU Avatar
  ILIYASU IBN ALIYU

  Assalamu alaikum warahamatullahi ta,ala wabarkatuhu bayan sallama irin ta addinin musulunci ina makowa fatan alkhairi da farko Malam marubuci ina mai tunasheka
  1.Annabi(S.A.W) yace idan zakai magana to kafadi alkhairi ko kai shiru.
  Domin kuwa bahaushe yace baki shike yanka wuya.
  2.kasani cewa karya haramun ne. sai yasa manyan bayin Allah muminai suke gudun bada wata labarin gudun karsuyi karya Allah yakamasu da laifi aikatata.
  3.katuna Aiki yasha bambam da Aqidah .dakace Yan TIJJANIYA sun yarda shehu ibrahim kaulaha Allah ne Wa’iyazubillah.kaga idan na fahimci maganarka akwai kuskure meyasa Bakace yan INYASSI ba kace Yan TIJJANI? Domin idan ko gaskiya ne da Tijjani za’amaida Allah ba Inyass ba damin shine mai dariqar.
  TOH ABIN TAMBAYA SHIN YAN TIJJANIYAN NAN BASU DAYA DAGA CIKIN WADAN NAN?
  a.sallah
  b.azumi
  c.zakka
  d.hajj
  e.kuma basu yarda da Allah dayane da Annabtar Annabi muhammad??
  4.idan kai makiyi ne ga yan darikun sufaye toh kai hakurima na kabarma zuciyarka Innallaha ma,assabrin domin duk abinda kayi bazai rage darajansu awajan Allah ba kamar yadda Akai ta wulakanta Annabawan Allah ba kuma baisa darajansu ta ragu awajan ubangiba.
  Toh ina baka shawara dakai takan ka domin kaima bawane mai nimar yardan Allah tun baka samu ba harkana waiwayan wadansu ai tsakanin Allah da bawansa kamar mata da mijine ba mai shiga cikinsu.
  Tammat

  1. A s jambil Avatar

   Wannan haka ne kana da gaskiya ilyasu

  2. Musa yalwa Avatar

   Assalamu alaikum,aini inabautama allah ne kumamunyarda da annabcin annabi muhammadu s.a.w kuma muna kwaikwayo da sunnarsace,mubabautawa wanin allah kuma duk wandayahada allah dawanito wannan mushirikine kuma hukumchinshi kisa kowani mawakine,indaiyaceshi musulmine,sabodahaka mubamubautawa shk ahmadu tijjani kuma bamubautawa inyass.

   1. Nibras Avatar

    Masha’Allah.

  3. ALIM Avatar
   ALIM

   Matsala ita ce dukan mabiyan Inyasi yan Tijjaniyya ne, she wandan aka amincewa a cikin Tijjaniyya ake yi wa tarbiyya ya zamo dan fayla.
   Yan Tijjaniyya su suke tallan faylar Inyass. She ya zamanto suka narke cikin yan fayla kuma basu nuna kuskuren yan fayla.

 2. Idris Abubakar Avatar
  Idris Abubakar

  Ka Ga DR. Musulunchi ke nan Allah ya kara mai hazaka,basira da fadin Gaskiya ko mai dacinsa. Amin summa Amin.

 3. YUSUF KURFI Avatar
  YUSUF KURFI

  KARYA KAKE MAKIYI SHEHU! SHEHU BAWA NE DAGA CIKIN BAYIN ALLAH.AMMA KASANI DUK WATA KAWA TA DUNIYA.A ZAMANINSA TA BAYYANA.

 4. Shamsuddeen Ibrahim Abubakar Avatar
  Shamsuddeen Ibrahim Abubakar

  Gaskiya muna bukatan erin wannan safi domin shiga musan darika da kyau

 5. Shamsuddeen Ibrahim Abubakar Avatar
  Shamsuddeen Ibrahim Abubakar

  Gaskiya muna bukatan erin wannan safi

 6. wannan shafi yayi kyu sosai, kuma wannan shafine wanda dukkan mutumin daya shiga zai sami wani ilmi daban akan darika mungode da wannan gudun mawa.

 7. yi hankuri je gida kayi kwana.kai har ka tara ilimin da zaka nuna ma mutane musulunci,yi hakuri je ka nemi ilimi wurin mazauwan shi.

 8. salam .bismillah innallaha ya’amuru bil ad li wal ihsani. da fair kafin muyi nisa su wadannan ma gang da ka kawo munason musan a wane littafi ja gansu?

 9. A s jambil Avatar

  Asslm ina kira ga yan uwa na da bin umurnin allah da ya ce (wa’adi ullaha wa adiur rasula wa ulul amri minkum) anan allah yana mana horo da bin allah da manzon sa da kuma ma’abota ilimi daga cikin mu na kuma tabbata cewa sheikh inyas nadaga ciki.kawai dai wadannan mutane sune wadanda sheikh da fodio ke tsoron kasassabar jahilcin su har yace “na hane ku da daukar litattafan waliyyai,khashifai kuce zaku karanta in ba harkarku bace”A cikin littafin sa mai suna(nasihatu ahluzzaman)ya kuma fadi haka ne saboda tsoron irin wadannan masu karancin ilimi saboda haka ina kira ga yan uwa na yan darikun sufaye su rike shehunan su dakyau kuma su yi imani da abin da suka zo dashi don suna shiryarwne zu ga allah ku rabu da masu shiryarwa zuwa ga naira. su kuma masu irin wadannan maganganu su sani cewa dariku basu taba kirkiran wata karya ga wani sheikhin izala ba. Saboda haka su ji tsoron allah su gaya wa mabiyasu gaskiya,in kuma baza ku iya ba to kubi shawarin shehu dan fodio ku bar shiga litattfan waliyyai don kuwa ba harkar ku ba ce. Ni suna na ahmad salihu jambil da ni dan izala ne har na rike matsayin babban ladanin wani babban masallacin juma’a a bauchi amma daga baya allah yatsamar da ni ta hanyar nuna mun wasu abubuwa wadanda ko jahili yasan wadannan abubuwa haramun ne saboda haka ina kira ga wadanda ke ciki dasu bar ta wadanda suke kyamar ta su kara kymar ta,wadanda suke son shiga kuma su sani cewa ba hanyar allah su nufa ba.ga numbar waya ta domin mai neman jin abubuwan da suka fitar dani daga izala sai ya neme ni, ni kuma in allah ya yarda zan fede masa biri wutsiya,har ma wasu abubuwan da basu shafi wannan ba zan bayyana insha’allhu(08035769485)wassalm

 10. A s jambil Avatar

  Wai me yasa mutane har yanzu basu gama yarda da manzon allah bane har suna iya fitowa suyi inkarin darajar sa

 11. duk wanda yace ‘yan tijjaniya sun riqi shehu ibrahim inyass abin bauta tsinanne ne,kuma maqaryaci ne! Domin duk masallacin da kaje na ‘yan tijjaniyya zakaji idan suna sallah/bauta sunan kiran sunan Allah ba sunan sheik ibrahim inyass ba. Ba sai nayi wani dogo bayani ba,shi kanshi mai wannan magana yasan karya yake,kawai yana isar da sakon gwangilar da yahudawa suka basu ne,do raba kan musulman duniya su kuma su samu damar yakar musulunci kamar abinda ke faruwa yanzu.don haka mu ‘yan dariqu kada mu damu mu dauka wannan jarabawa ce daga Ubangiji,kuma mu yawaita fadin HASBUNALLAHU WANI’IMAL WAKIL.

 12. Yahya umar Avatar
  Yahya umar

  Qaramin sani uqumi

 13. Abba-isa Avatar
  Abba-isa

  Allah da ya ganar daku gaskiya dan shi ka dai za iya fiddaku daga cikin wannan batan @ A S jambil
  mallam Allah ya saka

 14. Usman Isah El-yazkaki Avatar
  Usman Isah El-yazkaki

  Je ku samu irerenku yan bidi’a ku gaya musu wan, mu dai kam ba damu za ayi ba

  1. Lallai A.S JAMBIL, kodashike manyanku ne suke aike ku kushi irin wayannan wurare ku yake musulunci, ku dinga kuna ce wai dama ku izala ne amman sabo da kàzá kun bar izala kun koma dariqa, kai ku cigaba da fadin haka har gobe, mu kam daram muke yakan ku yan bidi’a, dun kuwa ba a bakin ka mun para ji irin wannan ba har da wani bada nomban waya , ire iren ku kun yi yawa da aka aike ku, dun kuwa me zai sa mutum ya bar izala ya koma dariqa? dun saboda yawan tafiya wa’azuzzuka? mutane kuji tsoron Allah madaukaki sarki mana, Allah ne kadai zai mana maganin ire iren wayannan shaidanun, daga karshe ina kiran duk muslman duniya baki daya , mu rabu da ire iren wayannan kalamai mu hada kan mu waje daya mu rugurguzar da bidi’a mu rungume sunnan manzon tsira, MUHAMMAD (s.a.w)…. Allah ka mana rabo da cin jarabawan ka ranan gobe qiyamah

 15. suleiman Avatar

  Allah ya kara ma shehu kusanchi ga annabi muhd(saw). Yan azazilu (izala) Allah ya shirye ku, domin kun san gaskiya.

 16. Sani Ibrahim Avatar
  Sani Ibrahim

  yin magana akan abin da bai shafeka ba wannan munafurci ne

 17. Jalo kayi hattara da rayuwanka. sabo da irin maganganun da kake fada akan manyan mutani. Kaga kafada magana kamarhaka 1. Kace saiyadi Ali( k.l .w) munafikine, don har kace sunan addinin shi ma{taqiyun} 2. Kace saiyadi Abubakar Da Ummar munafikai ne 3.kace yan dariqa sunce ,shiek Ibrahim inyas Allah ne.da saurasu! To haka Allah yace akira mutani izuwa ga Addinin sa? Kokuma son zuciyane. Kaidai JALO KA CHANCHACHI ADDU’A Allah ya laanceka Amin

  1. Daniyala Muhd Bello Avatar
   Daniyala Muhd Bello

   Lallai wannan zancin da jalo yayi bai kyautu dan dariqa yaji komai ba domin mu mabiyane kuma masoyane ga ga wanda girmarsa da rahamar da take tare da shi bai misaltuwa (S.A.W). da S Ali S Abubakar da S Umar da Usman (R.A) kaga Ashe bazamu kufce masaba tunda kowa yasan furucin sa akansu. Mungode wa Allah da ya Shagaltar damu dashi san nan ya shagaltar da wasun mu da mu. Allah ya kara mana kusanci ya kuma kara wa shehu karama.

 18. Ahmad M Tanimu Avatar
  Ahmad M Tanimu

  La,ila ha illallah Muhammadurrasulullah (s.w.a) wannan shine furuci da dan tijjaniya yake yawanyi ako wace rana amma baka duba girman wannan kalma baka yi tunani akan abinda zaka yi postin ba kawai kana neman comment na mutane. ba,abinda xamucemaka tunda ka kafirta mu. kowa yagyara yasani kuma kowa yabata yasani, kaji tsoron ALLAH.

 19. Tahir Mahmood Saleh Avatar
  Tahir Mahmood Saleh

  Mu Allah ne moulan mu amma baTijjane Inyass ne
  sam a addinin musulunci babu wasu khudabau
  wai wani mutum bazai zo ba just kwanan wai ace lallai sai mun bishi sannan inbahakaba addininmu bai cikagaba. Ba Inyass ba , ba kuma Amadu Tijjani ba ko Ibnl Arabi mulhidi dan taada bai isaba

 20. Aminu Abdulaziz Avatar
  Aminu Abdulaziz

  Mtswee JALINGO aje a karo ILIMI

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: